Chapter 17

526 26 15
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''

*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

'''GODIYA DA FATAN ALLHAIRI A GAREKI, MY TAKWARATA HAJIYA RAHAMA BABIRU TUKUR ƳAR MUTAM NASARAWA STATE, WALLAHI BAKINA YAYI KAƊAN DA GODIYA GAREKI SAIDAI NACE ALLAH YA ALBARKACI ZURI'RKI YA JIƘAN MAHAIFA, HAƘIƘA WANNAN ALHERI NAKI GARENI BAZAN MANTABA, ALLAH YA BANI IKON FARANTA MIKI AMEEN🤝🏻😍.'''

~*🤣🤣🤣Masoyan Ruwaidah Bazance Daku Kome Ba Yasin Kawai Na Gode Maku🙄🙄🙄*~

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 17*

Abbah suna isa asibitin hankalinsa a tashe ya shiga ciki, ko wajan Abbaye bai bari an kaishi, ba ya saka Dr Junaid ya ɗebi jininsa, ya gwada aka saka ma Abbaye, wanda yake baccin alluran da yasha sam baisan wanda yake kansa ba, Hamza na zaune a gafesa saman kujera riƙe da hannunsa wanda akai masa ƙarin jini. Can ko ɓangaran Abbah.
Ana sakama Abbaye jinin Abbah ya ya miƙe zaune, Dalhatu ya riƙeshi yace.
"Haba ishaq ka kwanta ka huta kaɗan, yaromu na tare da kawunsa, har a jima." Abbah yace" A'a babu wata damuwa muje na ganshi." dole Dr Junaid ya kaisu wajan Abbaye'e ɗin. Kwance yake kyakyawar fuskarshi babu abinda ta canza sai ma wani irin kyau da ya ƙara. Abbah ya zauna dab da Abbaye ya riƙe hannunsa yace"Sannu namijin duniya Allah ya ƙara kiyayemin kai, ya tsare gaba ya baka lafiya tare da sauran bayin Allah..." Hamza da Dalhatu suka amsa da" Ameen" Dr yace"karku masa yawan surutu yana buƙatar hutu sosai..." Wayar Junaid ta ɗauki ringing yana dubawa, yaga Mummy ce, ya ɗaga cikin girmamawa tare da sallama.
Mummy tace"Dr gamu munzo bamu san inda kuke ba, wani ɓangare kuke?" Dr yace"Hajiya gani nan fitowa." ya faɗi yana ficewa daga ɗakin. Rahma na kusa da Mummy sai raraba idanu take, zuciyarta na baugawa haka kawai ta rasa nutsuwarta. Dr yana hangosu Mummy ya isa wajansu bakinsa ɗauke da sallama. Mummy tace"Dr wani hali ake ciki muje a gwada jini na sai asaka masa, ina Abban nasu...?" Dr yace"An saka masa na Abbansa ai bismillah muje." ya faɗi yana gaba suna binsa. Islam har haɗa hanya take dan ba ƙaramin so takema yayanta ba duk da yana gana mata azaba. Suna shiga room, suaka hango Abbaye'n a cikin wannan halin.
Rahma jikinta rawa ya ɗauka hankalinta a tashe amman ganin Abbah wajan dole tayi kawaici hawaye ya gama wanke mata fuska ta raɓa kusan gadon ta zauna ƙasa dirshin tana kuka a hankali, ta ƙura masa idanu.
Aneesa Widaad islam Fu'ad Taslim Mummy, aguje suka ƙarasa wajan Acp ganin halin da yake. Mummy ta zauna gefe kusan Abbah ta kama hannunsa tana fitar da hawaye. Abbah yace"Haba me kuke haka ne pls ku barshi yana buƙatar hutu ke kina kuka yaranki fa sbd da Allah sai na hanasu suyi, kalli surukarki kin karyar mata da zuciya itama kuka take kalli ƴaƴanki, haba Taslim keda zaki lallashi ƙanninki kece kuma kike kukan kalli ihsan ma kukan suke meye haka ɗin....? "yafa ji sauƙi an saka masa jinin, dan Allah kuyi shiru." ya faɗi yana riƙe hannun islam yana lallashinsu. Mummy ta miƙe ta kama Rahma ta miƙar da ita tsaye tace"Kiyi haƙuri zai warke da yarda Allah kinji ɗiyata." Rahma ta jinjina kai Allah ya gani kawaici take. Taslim ta kama hannunsa tana masa Addu'a tace"Allah ya ƙara kiyayemin ɗan uwana ya rabaka da sharrin masu sharri." Hamza yace"Ameen Taslim insha Allah wannan ne na ƙarshe, Aneesa wai bazakiyi shirun ba?" jikin babanta ta faɗa tana kuka tace"Dady Ya Abbaye ya bani tausayi." Dr Junaid yace"Masha Allah sai dai ku fita daga waje haniyar tayi yawa fa."Mummy bata musaba bayan sun masa Addu'a suka fito Mummy na riƙe da hannun Raham.
Zaune sukayi saman kujerun da aka tanada domin zama. Taslim tace"Mummy ya kamata Rahma taje gida kar ai mata faɗa ta jima, in yaso idan ta shaidama iyayan nata sai ta dawo zuwa yamma liƙis ko dare lokacin ya farka, nima zance na dawo." Mummy tace"Eh hakan yayi Ruwaida ma ita ɗaya a gida islam ya kamata kuje sai direba ya kawoku har ita ɗin." Islam tace"Mummy sai anjima ni sai naga Ya Abbaye ya farka." Taslim ta miƙe tace"Ok ke Rahma tashi muje na ajiyeki gida." Rahma cike da biyayya ta miƙe duk da ba haka taso ba. Taslim tace"Mummy sai mun dawo idan na gama abinda zanyi zan biya na ɗauko Ruwaida sai muzo." Nan sukayi sallama ta kama hannun yaranta suka nufi mota har Rahma. Yaran suna seat ɗin baya Rahma na kusanta zaune haka suka bar hospital ɗin.
Rahma kamar butum butumi ta zama sam batajin daɗin duniyar duk taga ba wai ya jimu sosai bane. Suna zauwa ƙofar gidansu, Rahma Taslim ta ƙara mata nasiyya ta mata sallama ta nufi cikin gidan nasu jikinta sanyi ƙarai. Taslim ta ɗauki hanyar gidanta. Inna Talatu tana cikin rumfar ƙofar ɗakinsu a zaune tana masifa, malam na gefe zaune fitowarsa kenan daga sallar la'asar, Zainab na kusansa. "Wallahi naga shegen da zai sake barin Raham fita, ba dai ta maidamu iyayan banza ba, ai malam duk laifinka ne da nayi mgn kace banida tunani, wlh baza a ɗaukomin mgn dangin ka su zageni iheeee." ta faɗi tana hura buɗadd'an hancinta. Malam Ɗahiru yace"Talatu wai me zai sameki ni kam banga abinda yaron nan ya tsare miki, tinda dai da na hanashi ya maki alheri kawai sai kikamai dashi ɗan iska."Zainab ta bushe da dariya tana toshe bakinta. Ai kuwa inna talatu ta warci tayani tsugunni, zata buga mata ya matsa ta ɓoye jikin Babanta.
Raham ce ta shigo da sallama jikinta sanyi ƙarai. Zainab ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Auntyna." ta rungumeta.
Malam yace"Sannu Rahamar Allah amman kin jima sosai lfy dai ko?"Rahma ta saki Zainab ta zauna kusan mahaifinta tana matsar ƙwalla. Inna talatu tace. "Ikon Allah yanzu sbd Allah Rahma yau kika fita daga gidanan, amman shine zaki shigo da salon munafurci ki naɗe tarbarmar kunya da kukan munafurci." Rahma tace.
"Aa innata ba haka bane wlh tsautsayi ne ya faɗa kan Acp..." Nan ta basu labarin kome. Malam yace "Subahanallahi ai banga ta zama ba bari naje na duboshi ko hirace naji anayi a shagon bahari?"Rahma ta jinjina kai duk da bata tabbacin hakan. Inna talatu tace"Allah ya sawwaƙa malam sai a ɗaura girki a tafi dashi ko?"Ɗahiru ya miƙe yace"Wane girki kuma? Haba idan kina zuwa tashi kawai muje." inna ta miƙe ta shiga ɗaki ta shirya shima ya shiga ɗakinsa. Rahma tace"Zainab mu bari idan sun dawo sai mu koma." ta faɗi tana buɗe jakarta ta zaro dubu ɗaya daman dubu biyo ne kawai gareta, tace" Zee amshi sayo kwai guda goma da abinda babu tinda akwai kifin gwangwani sai na masa dambun kifi da kwai mu tafi dashi kiyi sauri Zainab." zee ta amsa tace"Tom antyna" ta faɗi tana shiga cikin ɗaki ta saka hijabi. Raham tayi dialing ɗin number Asma'u ta miƙe ta shiga ɗakin, lkcn ta ɗauka, ta zauna gefen katifarta tace"Aunty idan kinada dama anjima kixo muje hospital Acp ya sami tsautsayi an harbeshi." Kome tace mata tace"Eh gasu zasu tafi.......Ok se kinzo bye"tace tana kallon innata tana shiryawa. Talatu tace"Matar police aromin dubu biyu zan siya masa lemo a hanya ni wlh banida ko sisi yau, gyaran da nake maki ya tatikeni." Rahma tana tsoron tace batada sai dubu ɗayan da zasuyi kuɗin napep azageta ba yanda zatayi, ta zaro dubun ta bata tace"Inna gata daman biyu ce naba Zainab ta siyo mana kwai na masa dambun kwai da kifi."Inna ta amshe dubun tace"Ngd haka ma kya ƙira ƴan gidansu su kaiku..." Ƙiranta Malam yayi yana faɗi"Zan tafiyata fa." hanci ta hura tace"Muje ai na kimtsa. Ta juyo tace"Sauran idan kinyi dambun ki ƙi ajiye mana saura ki sauye masu duka, uwar neman suna. Ta faɗi tana fita.
Rahma ta girgiza kai tace" Innata kenan abinda dai kun dawone zamu tafi, zanjira kizo ki ɗebi wanda zai maki." ta faɗi tana miƙewa ta cire kayan jikinta ta ɗaura zani ta saka hijabi, ta fito ta ɗauki bokiti ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki tayi wanka ko taji daɗin jikinta.

RUWAIDAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora