Chapter 33

413 13 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''





*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 33*

“Abbana bari naje na kwanta.” ya faɗa yana rungume Abbah, yana basa kiss a kumatu.    Mummy tace“Allah ya maka albarka Abbanmu...” Abbah ya amsa da “Ameen” yana buga bayan Acp.  Musaddiq yace“Allah bata lfy.” Acp ya janye jikinsa yana faɗin“Ameen my bro.
                 Parlour'n suka fito Safwan ya nufi ɓangaransa, zuciyarsa fes yake jinta.  Abbah da Mummy da Musaddiq suka bisa da kallo.  Abbah yace“Bara na leƙo su Bappa...”  Fu'ad yace“Abbah zanje.”Abbah yace“Kai sarkin yawo ko? Oya muje.” cikin murna Fu'ad ya  kama hannun mahaifinsa suka fice.
                       Musaddiq ɓangaransa ya nufa. Mummy tace“islam! Widad  Oya kuji wajan Ruwaida, saura kuyi ta surutu ku tasheta, ko baku gama ɗaukan karatun ba?” islam tace“Mummy bara muje can zamu gama, sai muyi alwala muyi sallar  nafila muyi mata Addu'a.”    Mummy tace“Yauwa Allah ya maku albarka.” suka amsa da “Ameen.” suka miƙe suka nufi bedroom ɗinsu. Mummy bedroom ɗin Abbah ta nufa tai masa gyaran kaya.
                  Bappa suna zaune cikin parlo, shida ummani, sai Buhari ƙanansu Aneesa yana kallon Tv.  Abbah ya shigo da sallama yana riƙe da hannun Fu'ad. Amsawa sukayi cikin sakin fuska, Bappa na tambayarsa“Ya jikin na Ruwaida?”  Abbah ya zauna kusan Bappa.  Fu'ad ya isa wajan Buhari ya zauna yana cewa“Anan zaka kwana?” Buhari yace“A'a dady idan ya shigo zan tafi hira na kawo masu.”
                            Abbah yace“Yauwa yaron kirki sannu, Bappa me jiki tayi sauƙi sosai, na rasa wasu irin mutane ne marasa imani suka mata haka? Sun cutar da yarinyar sosai, ko da rashin mgn suka barta ya isheta ba sai sun haɗata da jinnu ba... Kai Allah shi kyauta...” Ummani tace“Muci gaba da Addu'a ishaq insha Allahu kaidinsu zai koma masu, bi'izinillah...Yarinyar tana bani tausayi, ciwonta na son kulawa sosai.” Abbah yace“Eh hakane ummah insha Allahu zata samu fiye da yanda zamu kula islam da Widad.” Bappa yace“Ishaq Allah ya maku albarka.” Abbah ya amsa da “Ameen” sukaci gaba da hirasu.
                          Acp yana zuwa ɓangaransa ya sake shirin bacci cikin wasu haɗaɗɗun kayan bacci, sai baza ƙamshi yake, kwanciya yayi sbd agajiye yake, bakinsa ɗauke da Addu'a, ya kunna karatu wayar kusansa, bayan ya gama Addu'ar ya rinƙabin karatun har bacci ɓarawo yayi gaba dashi, asuba ta gari.

**************     *******   **************
*Bayan kwana 5*
Alhamdulillah jikin Ruwaida na ƙara samun sauƙi, akullun sai an kaitai gidan malam ɗan asabe ya mata ruƙiyya, tasha ruwan Addu'a wanda yake mata da ruwan zamzam dasu garin habbatulsauda, da garin zaitun.  Matsalar har yanzu cikin na nan haka zatana abu irin na masu laulayi, amman hakan bai damusu sbd malam yace ba abinda zai faru insha Allah zasu barta.  Hakan yasa  suka dage ta kowane ɓangare wajan Addu'a da karatun Qura'an. 
                        Ɓangaran shirin biki ma ba abinda ya canza gidansu Acp ƴan matan sai shagalinsu suke, wanda har Ruwaida aciki, amman Mummy ta hana amata kitso da ƙunshi, sbd ƴan iskan aljannunta, itako ta dage sai an mata, har kuka take.  Haka gida ya fara ciki da baƙi ƴan mali wanda ayau ne ƴan niger zasu iso.   Acp su uku suke shirye-shiryansu, shi da Musaddiq da babban abokinsa Nadeer tare suke komai na biki hatta wajan da zasuyi dinner an kama A haɗaɗɗiyar hotel kuma tsadaddiya. ( *Star xclusive suites hotel*) Nan suka kama wajan dinner.
                         Aneesa  tasha gyaran amare abin ba'a cewa kome sosai mom ɗinta ta tsumata tasha kitso da ƙunshi masu ɗaukar hankali, tayi kyau har ta gaji.
                  Ɓangaran  gidansu Rahma Masha Allah idan kaga Rahma sai ka kuma kallonta, tayi kyau har ta gaji, abin ba'a cewa kome, gashi ta tsumu.  Inna tana iya ƙoƙarinta wajan gyara ɗiyarta.
                        Zaune Rahma take tayi wani irin kyau saidai ta rame ta ƙara haske fayau.  Murmushi tayi ta ƙara manna wayar akunnenta tace“A'a my Qalbi yanzu dai zanyi breakfast kafin me kitso da me ƙunshin su iso.” ta faɗa ƙasa².   Acp yana fesa turare yace“Ok my dear ayi min me kyau.” yana faɗin haka yaja bakinsa yay shiru yana ajiye turaren.  Rahma tace“pls kaje kayi kaima breakfast pls.” ɗan guntin smile yay yace“Ok amarsu bye zan ƙiraki.” yana faɗin haka ya yanke ƙiran.
               Rahma tayi ƴar dariya tayi fari da ido, ta cilla wayar kan katifar ta miƙe ta fito tsakar gida.   Inna na shan shayi malam gefe, shima karin yake, Zainab ta tafi school sai  baƙin da sukayi su uku Hindatu ƙanwar malam da ƴarta Sabira sai ƙanwar inna Sa'adatu.  Rahma ta iso kusan inna ta zauna tana faɗin “Su goggo Hindatu ana ta fama da ruwan zafi ko?” ta faɗa tana dariya.  Inna ta taɓe baki tace“Ai dole tinda an shigo birni ko...” Rahma ta katseta tana faɗin “inna bari nayi na karya me kitso na hanya.” goggo Hindatu tace“Wannan yarinya ba kunya Rahma har son kitson barin gida ake....?” inna tace“Eh ai ba rashin kunya bace...” malam yace“Zinaru kimin shiru ina ruwanki da hirasu?” Sa'adatu tace“Yaya malam kayi haƙuri su aunty Zinaru sai addu'a.  Inna tace“Ikon Allah to Allah baku hƙr malam baka gane bane ai dai kasan bazan faɗa da baƙina ba, baƙonka Annabinka.” Rahma ta haɗa shayinta tana sha suna hirasu dasu goggo Hindatu.  Ko gamawa basuyi ba me kitso da ƙunshi suka iso, daman yaya da ƙanwane.  Tana gamawa  suka fara mata,se ga Samira da Fadila se ga mmn Sabrina, suka haɗe anata hira mai kitso nayi me ƙunshi nayi.
                              Haɗaɗɗan falon nasu ya shigo cikin takunsa na isassan namiji, sai baza ƙamshi yake, uniform ɗin ta kamashi sosai yayi wani irin kyau, kai kana kallonsa kasan angone, ƙamshinsa ya gama karɗe falon.   Mummy zaune ita da ummuh ya hango su, ya iso yana faɗin“Good morning my Mummy.” ya faɗa yana zama, ya kwanto jikinta.  Mummy ta shafa kansa tana murmushi tace“Morning son, yauwa gwara da ka fito, ai nazata ka fice tin sassafe kaga, ƴar gidanka ni nayi Musaddiq yayi, tazo tayi breakfast taƙi sai kuka take, Abbanku yace mu barta aka kunna mata karatu, tana ɗakinsu, je kaji meke damunta, wlh bana son naga tana kuka...” Abbaye  yace“Oh my god! To Mummy meyasa ba'a tadoni ba?” ya faɗa yana sakin mahaifiyar tasa, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsu Ruwaida, ya manta ko ummuh bai gausheta ba.
                 Zaune take kan gadon nasu ta haɗa kai da guiwa tana sharɓar kuka, harda majina ta barbaje dogon gashin kanta, ya rufe mata fuska. Wayarta gefe karatun Qura'an na tashi. Ƙofar ya murɗa ahankali ya shigo, bakinsa ɗauke da sallama.  Halin da ya hangota yasa yay saurin nufar bakin gadon.
                  Ruwaida tanajin jin muryasa amman taƙi ɗagowa ta ƙara sautin kunka nata.  Safwan ya zauna bakin gadon, ba tare da yayi mgn ba, ya sanya hannunsa duka biyu ya ɗago da kanta, ya fara tattare mata gashin da ya rufe mata fuska.
                 Ganin yanda fuskarta ta ɓaci da hawaye, yace“Subahanallahi Ruwaida! Meya samiki ƙanwata?” ya tambayeta yana ɗaure mata gashin nata baya, ya ɗauki hijbin da yaga ajiye kusanta, ya shiga goge mata fuskarta, tana shasheƙar kuka.  Fitinannun idanunsa masu mutiƙar haske, da jan hankalin duk wata ƴa mace, ya ƙura mata su, yana goge mata hawayen, haɗi da majinar.
         Shanyayyun  idanunta ta runtse, tana ƙoƙarin kauda kanta. Tallafo fuskarta yay cikin kwantar da murya yace“My happiness! Meye kike famar kuka, haka? Yi shiru faɗamin me kikeso, zan miki bana son kukanki.” ya ƙarasa mgnr yana share mata hawaye da yake gangarowa saman kyakyawar fuskarta, yana hura mata iskar bakinsa. Jikinsa ta faɗa ta tura kanta cikin ƙirjinsa, tana sauke ajiyar zuciya.
                       Hannunsa ɗaya ya ɗora saman gadon bayanta, yana bugawa ahankali, ɗayan yana shafa lallausan gashin kanta. Ya ɗan duƙo kaɗan dab da kunnata, can ƙasan maƙoshi yace“Kin sami nutsuwa yanzu?” Baki ta zumɓuro gaba, tana ƙara shigewa jikinsa tayi luf tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, tana shaƙar ni'imataccan ƙamshinsa, mai sakawa taji nutsuwa.. Sai kuma tai saurin zabura ta janye jikinta, tuna hakan sam bai dace ba, duk da ta sami nutsuwa, amma haramci take aikatawa, rungumrsa da take, tinda ba muharaminta bane.  Baya ta matsa can ƙarshen gadon, ta sadda kanta, tana sauke numfashi, tana wasa da yatsutsin hannunta.
                Abbaye ya zaro wayarsa ya matso ya kamo lallausan hannunta, ya saka mata wayar cikin tafin hannun nata, yace“Oya faɗamin me kikeso?” Ruwaida cikin zaƙuwa ta fara rubuta masa _“Yayana me kirki inaso nima ayimin kitso da ƙunshi irin nasu islam da Widaad pls kaji,😥 ka roƙi Mummy'nmu ta yarda, amini._ Haka ta rubuta masa ta bashi wayar.
              Yana dubawa ya watsa mata harara cikin tsawa yace“Oh kina nufin sbd an hanaki ne kike kuka kika ƙi cin kome? Sbd kin raina Mummy da Abbah? Baki son lfyrki? Kinfi son sheɗanun wannan suna bibbiyar rayuwarki?” ya tambayeta cikin tsawa, wacce ta firgita Ruwaida, ta gigice ta fashe da kuka tana girgiza masa kai da ɗaga hannunta, ta yin ƙuro ta iso gareshi zata faɗa jikinsa ya daka mata tsawa“Karki taɓani maza sauka kije kici abinci.. Kuma wlh ki haɗiye kukanki ko na karya miki wuya yanzu...Baza'ayi miki kitso da ƙunshinba, kuma babu inda zaki fita ran aure, kina gida.. Miƙe maza ki fice kici abinci, idan na fita aƙirana ace kina kuka, kiga yanda zanyi katantanwa dake...”
                  Ya ƙarashe mgnr yana jan dogon numfashi sbd yanda yay mgn me tsayi, ya haɗa da zabga mata harara.  Ruwaida ta ɗauke kanta daga kallonsa, jikinta ya fara ɓari ganin yanda yay mata, tsoransa ya shigeta sosai, ƙam ta ƙame waje ɗaya, tana ƙokarin haɗiye kukanta, ta fara ƙoƙarin sauka daga saman gadon, tana dab da saukowa kanta ya fara juyawa, ta tafi luuuuu zata faɗo ƙasa ya tarota, jikinsa ya ɗauketa caɗak, yana jijjigata.
                              Idanunta ta buɗe ta shafi gefen fuskarsa tayi murmushi hawaye ya wanke mata fuska, sai kuma yaga idanun sun lumshe numfashinta na sama da ƙasa, saitin zuciyarta yana wani irin mahaukacin bugo.
                    Jijjigata ya fara yana ƙiran sunanta, amma ina... Parlour ya nufo, sukayi karo da Mummy a ƙofar ɗakin. Wacce tsawar da tajini yasa suka nufo ɗakin da gudu ita da ummuh baƙuwar da sukazo daga mali.    Mummy tace “Abbanmu! Lfy? Tsawar me naji kana mata? Me kuma ya sameta? Acp ya nufi saman kujera da Ruwaida, yana faɗin “Mummy bani ruwa me sanyi.” Mummy fridge ɗin ta nufa da sauri.  Kwantar da ita yayi saman kujera lokacin ta sanƙame kamar gawa, bata motsi, Acp yace“Ya Rabbi!! Oh wai meke faruwane haka? Haba abun yayi yawa fa.” Mummy ta iso tana buɗe murfin robar ruwan ta bashi ya amsa ya shiga zuba mata, amman bata farka ba.
                        Mummy tace“Me ka mata wai?”Acp yace“Me kuwa zan mata? Muje hospital mu gani a bata temakon gaggawa.” ya faɗa yana cicciɓarta yay waje.  Mummy daman tana sanye da hijab tace da ummuh su tafi, sukabi bayansa, tana ƙiran Abbah A waya sbd sun fita shi da Musaddiq.
                                Suna zuwa hospital ɗin aka amsheta, aka fara bata temakon gaggawa.  Acp da Mummy hankalinsu duk atashe. Haka su Abbah suka iskosu, har lkcn likitan bai fito ba daga ɗakin da aka shigar da Ruwaida.    Abbah ya dafa Acp yace“Abbanmu jeka wajan aikin kaga sai ƙiranka ake, zamu kula da ita...”Acp ya lumshe fitinannun idanunsa, ya shafi sumar kansa, ya riƙe hannun mahaifinsa yace“Abbah ko naje banida nutsuwa, nafi son ta farfaɗo ɗin sai na fice...”Abbah yace“No kaje ɗin da zaran ta farka zan ƙiraka, pls yaron kirki.” gunti smile ya saki yace“Ok Abbana! My Mummy! My  bro Ummuh bye.”  Ya faɗa yana tafiya.  Ya manna waya akunnensa, bugu ɗaya aka ɗaga, cike da bada uwarni yace“ ina _*Danny's wellness clinic*_ kuzo ku ɗaukeni.” yana faɗin haka ya tsinke ƙiran, ya fito farfajiyar asibitin wacce take ɗauke da shuke² iri² sai ɗaga masa hannun jama'a suke, ganin Acp guda na yawonsa shi ɗaya, ga yanda uniform ɗin ta zauna masa ajikinsa.  Nazifa dake ƙoƙarin shiga parking spece ta hango Acp, jinta tayi kamar a aljanna, jikinta har rawa yake, tai parking ta fito, ko motar bata rufe ba, ta nufi wajansa.
           Yana ta shawaginsa kamar daga sama, yaga Nazifa a gabansa fuskarta cike da murmushi tace“Amincin Allah ya tabbata agareka, ya kai ma'abucin kyau da cikar zati, good morning haƙiƙa ni ɗin me sa'ace daga zuwa dubiyar mamar ƙawata na haɗu da farin cikina haske mai haskaka duniya hasken da baya dusashewa...” Wani  banzan kallo watsa mata wanda yasa saura mgnrta ta maƙale a harshenta.  Da hannun ya mata nuni ta matsa ya fice.  Ba musu ta matsa, cike da danasani, ga kunyar mutanan da suke kallonsu.
                         Wata arniyar motace me numfashi ta faka agaban Acp. Gaishesa sukayi cikin girmamawa haɗi da sara masa, ya shiga baya ya kame, motar har tabar wajan Nazifa na tsaye kamar gumki tana zubar da hawaye'n baƙin ciki dizgatan da Safwan yayi.   Kasa shiga ciki tayi ta shiga motarta tafi.
                Musaddiq yace“Abbah me zai hana ayi wani abu akan wannan lamarin, ciwon yarinyar nan maganinsa na wajan Safwan dan Allah a ɗaura masu aure, domin yaji daɗin bata kulawa...”Abbah ya katseshi ta hanyar cewa“sam hakan ba meyuwa bane.. Sbd yarinyar ta faɗa auranta ƴan kwanaki ta fito, to idan fa an ɗaura ya kake ga abin zai kasance? Idan ta dawo haiyacinta tace batason Abbanmu fa? Idan iyayanta suka nuna bamu masu adalci ba fa? Agsky ina tsoron abubuwa dayawa, da yake faruwa ta wannan hanyar, sanna ya zan kalli idon malam Ɗahiru mutum me mutunci da nagarta nace masa zan kuma ɗaurawa yarona aure? Kai mubar wannan abun, yarinyar nan lamarinta akwai firgitarwa fa.”  Mummy tace“Abbansu amman hakan zaifi, idan ta dawo haiyacinta  in bata sonsa sai ya saketa, ai ba dole, sannan babu ma fa tabbacin gaskiya an ɗaura mata wani aure...”Abbah ya ɗaga mata hannun  yace“Bazaku ganeba mubar mgnr don Allah, Musaddiq ƙira mana malam ahaɗa da ruƙiyya kaga yau daman ba'a mata ba, idan anci sa'a sai ta farfaɗo.” Mummy taja bakinta tayi gum, haushin ma Abban ta fara ji, sam bata son ɗanta na yawan rungumar Ruwaida tinda ba muharamarsa bace, gashi ciwon dole sai yana taɓata, ita bataga illar auran ba, ita Rahma ba'a aure zai aureta? Kuma ai larurace ba tabbacin warkewarta kusa haka za'a zuba ido ƴar mutane ta lalace bayan sunada kusan rabin maganinta atare dasu...Idan ta warke tace bata sonsa ba sai ya saketa ba...Wajan ta bari taje can nesa dasu ta zauna.  Ummuh ta biyota.  Abbah ya gane Mummy sarai fushine tayi, ya basar da ita  shi dai bazai haɗa abinda zai zo ya damesu ba.   Musaddiq shima tafiya yayi ya shaidama malam matsalar da ake ciki.
                  *Niger*
Masarauta me adalci, ko ina ka waiga bayine maza da mata sanye da uniform ɗinsu kamar kullun suna kai komo kowa na aikin da ya saba, masu tsaron ƙofofi nayi.  Wata jigegiyar mota fara ƙal, me numfashi, sai walƙiya sai wasu guda biyu baƙaƙe, wanɗa suke bayan farar dogarai na tsaitsaye kusansu,kana kallon motocin kasan fita za'ayi dasu.  
                            Tsaye yake tsakiyar matan nasa, da yaransa yana masu bankwana, cikin shigarsa ta alfarma, yake akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da kwarjini, sosai shigar tasa tai masa mugun kyau. Hannun Safna ya saki ya shafi kan Ashiru cikin izzarsa yake faɗin“Insha Allah kwana 3 kawai zamuyi ku kula da kanku Ashiru ka maida hankali wajan karatunka, beby bye.” yana faɗin haka yasa kai cikin izzarsa yake takawa yana riƙe da wannan sandar girman wadda ta zame masa ado sai sheƙi take ta zallar zinare da azurfa.  Bayansa suke take masa cikin sanyin jiki suke bin bayansa har ƙofar ta ƙarshe.  Sarauniya ta danna wani ɗan madanni, sai ga wata ƙofa mai adon zaiba, mai masifar kyau ta buɗe.  Tsaitsaye suke bakin ƙofar sun kame, jin ƙaran buɗe ƙofar suka zube ƙasa suna masa ƙirarani, duk da akwai  iyakar da ba'a ganinsu, sai motsinsu.   Jakar Sarauniya ta ƙira wata ƙuyangarta ta zube ƙasa ta bata ta kai asa amota.  Sallama sukayi ya isa ƙofar. Ƙirarani dogaransa suka fara masa sun tattaresa da rigunansu sun karesa, ahaka ya fitowa.  Takunsa yake cikin nuna izzarsa, sai ƙirari suke zuba masa. Kai tsaye wajan motar suka nufa, sbd jirgin ƙarfe shaɗaya zai tashi.  Wajan shiga motar ma, ƙaryaka kaga shigarsa motar, sun kareshi, sai ƙirari suke masa, haka ya kame a bayan motar, motoci ukku ne suka bar gidan domin zuwa airport. 
                      *Nigeria*
Acp tinda yaje wajan aiki bayada wata nutsu, ahaka dai yae gabatar da kome.  Ruwaida kuwa likitocin basu samu ta farfaɗoba sai malam ɗan asabe yazo ya haɗa da karatun   ga ruwan zamzam me ɗauke da Addu'a yana yayyafa mata su sunayi kusan awa biyu kafin numfashinta ya dawo, jikinta sai wata irin kyarrrma yake, tana fizge fizge haka yaci gaba ɗa Addu'ar har rawar jikin ta tsagaita, aka saka mata drip. Sai lokacin hankali Abbah da Mummy ya kwanta, malam ya ƙara masu bayanin wlh duk sharrin jinnu ne, insha Allah sai sunga bayansu, tunda sun riƙe Allah.
          Tafe suke suna hira wasa da dariya, hankalinsu yayi nisa sun raja'a sosai, da mgnr da suke har basu san sunzo tsakiyar titi ba, aƙoƙarinta na tayi baya, kamar yanda sukayi sam ta gigice sai tayi gaba sbd  uban horn ɗin da direban   ke mata, ga burkin yaƙi riƙuwa, kawai sai ji kake ya bugeta da ƙarfi ta bugi motar ta faɗi wanwar ƙasa, ba alamun numfashi ajikinta, jini na bulbulowa daga hancinta!!

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now