Chapter 2

641 21 11
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''

*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*~Wai Wai Wai Kai.....Wallahi Kowa ya rasa masoyi yayi kuka, Naso lissafo ku masu manya² comments dan kusan ina tare daku, amman kashhhhh......wlh kuna da yawa, ba zanso nasa wasu nabar wasuba, tinda sai nabi ɗaya bayan ɗaya, amman kusani ni kam banida bakin maku godiya, masoyan wannan littafi na Ruwaidah, Se dai nace Allah ya saka maku da Alkhairi, agaskiya ban taɓa zaton labrin nan zai karɓu hakaba, har ga Allah ba yanzu nayi niyar cigaba ba, amman tsautsayin da ya saka na ɗora number na......cewar naji yanda ya karbu, Yasin kuwa jiya da shekaran jiya naga ruwan ƙauna, wlh naji matuƙar daɗi ba kadan ba. Dan haka banida abinda zance Da masoyan Ruwaidah sai Allah ya ƙara ƙauna, Wlh naga ruwan comments ɗin jama'a bila'adadin, Naji daɗi sosai wlh.😘 Nagode kuci gaba da haka niko zanci gaba da faranta maku cikin wannan tafiya mai cike da abubuwa daban daban, wlh jin daɗin comments ɗinku ne yasa kuka jini nan kusa da masu bina pc roƙon nayi masu cigaba, to gahinan🤣 na sambaɗo maku, Asha karatu lafiya, son so Domin Allah.😍~*


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 2*

"Wai gaskiyane Angel ɗina tin safe ba agantaba duk girman gidanan? TO garin yaya yarinyar da ba fita take ba sai makaranta ko da dalili, ina kuyangunta? Ina sarkin kofa? Ina duk wasu bayi masu kula da shige da ficen gidan ne...? Duk Suna ina hakan ta faru? Wlh Nan da 1 hour idan ban samo Angel ba, zan saka ama kowa azaba mafi muni tare da horo mai tsananin gaske...."
ya faɗi cikin ɗaga murya jikinsa yana wani irin tsuma, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur. Hajiya kilishi Ce tayi saurin share hawayen fuskarta, ta riƙe yarima, ta kamashi ta zaunar dashi saman wani ƙaton tuntu mai masifar kyau, da laushin gaske.
Ta fara bubbuga bayansa cike da jimami haɗi da tattaro jarumta ta fara mgn acikin tashin hankali, da ta kasa ɓoyewa tace.
"Yazeed ka nutsu ka kwantar da hankalinka, Ruwaida bazata ɓata ba, baka fini ƙaunarta ba, bakasan halin da nake ciki ba. "Wai wane mai ƙaiƙayin bakin ne ya ƙiraka a cikin masarautarnan har ya faɗama, ka biyo dare ka taho? Inaji ajikina batayi nisa ba.....Kasanta da tsokana, ka tuna Angel ɗinka akwai tsokana, zasu iya haɗa baki da Mabaruka, dan sam ban yarda cewar bata san inda take ba, ba tasan mai martaba sunyi tafiya ba, saboda naga tanama Mabaruka ɗin kwatancan irin dai zatayi tsokana, amman ina tambayar Mabaruka tace dani wai hira irin kitson da za'a matane..... Da ƙunshin aurenku, wlh nafika shiga tashin hankali aure kwana 5 yay saura ace Angel ta ɓata, wlh akwai wata ƙasa, sanin kankane, Mai martaba zanfi kowa shiga bala'i a wajansa, ba kamar sarauniyarsa ba, duk da naga hankalinta a tashe, gashi Nanah bata nan bare ace da ko da saninta, tinda bata ƙawaye sai su biyu, kaf faɗin masarautarnan kai dama wajanta, amman ita na ƙira Mabaruka ɗin nayi mata binciken duniya tana kuka tace rabonta da Angel tin jiya dai da dare bayan ta gama tsefe mata kai, ta tafi..." Ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke tace.
" So Bayan ta tafi na niɗa sarauniya, muka saka aka taramana duka wasu baya ga jakadiya zaune babu irin tsoron da ba'a basu ba, cikin su babu wanda bai mana ratsuwa da azabar Allah ta tabbata gareshi ba basu ga fitar Angel ba, wannan masifa dame tayi kama, na saka an duba duk girman gidanan lungu da sako, babu ita..... Sarauniya ma ta ɓangaranta tayi duk wani bincike, har wazirin na saka aka ƙira cewar yaba Mabaruka tsoro idan Ruwaida tana nan Gidansa ta faɗi idan taki zan saka akamota akaita ɗakin horo, amman iya gaskiyar kenan a yau bata ganta ba, kamar yanda babu wanda ya ganta ayau a gidanan..... Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un!! Allahumma arjirni fi masibatin wa'akilli khairan,minha......" ta faɗi tana zama dabas tace"Inaso Yarima kayi duk abinda ya dace kafin Mai martaba yake isowa." Jakadiya kuwa wacce ta dasƙare waje ɗaya ta ƙam saboda sosai taji tsoron! Yazeed sabida saninsa mutum ne mai sauƙin kai, amman sanin ƙaunar dake tsaninsa da Ruwaida ba ta wasa bace tasan zai iya sawa ayima jama'ar gidana azaba launi² zai iya yin abinda ba'ayi tunani ba, itama duk inda take hankalinta na gareshi........ Satar kallonsa tayi tai saurin kauda kai, shida mahaifiyarsa kallo ɗaya zaka masu kasan suna cikin musifa, duba da yanda hawaye suke sauka kan fuskarsa, ga wani irin mazari da jikinsa yake a zaune, sbd jin bayanin Hajiya kilishin..... Baki Jakadiya ta kuma buɗe tace.
"Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, takawarka lafiya ɗan sarkin sarakuna mai adalci, a temaka aji abinda ya kawoni wajanku sakone daga sarkin fada...."Yarima ya kuma cewa"Jakadiya baki bani amsar tambayata ba..... Me kuke tunanin zai faru idan mai martaba ya sami labari, sanin kankune masarautar nan babu zama lafiya, ko sarauniya bazata taɓa gane kansa ba, ciwonsa zai iya tashi, bayan haka ni ina kuke son na saka rayuwata? Yanzu ta ina zamu nemanta...? Ina zan fara neman Angel? Sanin kankune bazan iya cikakkiyar rayuwaba ba tare da itaba, suwaye? suwayene.....? Ina Angel ta shiga."
Yarima Yazeed ya faɗi yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa. Hajiya Kilishi ta dafa kafaɗarsa tana bashi baki. Jakadiya ta ƙara rusunawa tace"Allah ya huci zuciyar Magajin gobe Mai martaba baida labari amman ni shawarata Ada wada sarkin faɗa ya bayar, me zai hana a saka duk wasu kuyangunta ɗakin horo tare da Mabaruka a basu azaba da horo mai tsanani ko za'a dace, ni kam munyi iya bincike babu gimbiya Ruwaida a gidan... Sannan antabbatar, Nanah bata wani lbr akan Ruwaida? " Hajiya kilishi tace"Ok tashi na sallameki turomin kuyanguna dukansu." Jakadiya ta miƙe cikin girmamawa tayi godiya ta fita. Yazeed ya miƙe yace"Allah yaja da ran kwananki ya mahaifiyata, banason ki dakatar dani akan duk abinda kikaga nayi, mutiƙar ba Angel ɗina ta fito ba." yana faɗin haka ya fice daga falon, yana gama hanya. Kai tsaye sashen sarauniya, ya nufa, dan sunan da suke faɗa mata kenan a gidan duba da tsantsar ƙaunarta da martaba yake, hakan bai taɓa damun hajiya kilishi ba, sanin darajarta daban take a wajansa kuma taga ai ba aibu, dan anƙirata sarauniya tinda matar sarki ce.
Yana shigowa ya isko Mabaruka na kirtar kuka duƙe gaban saraunuya, Ashiru yana mata tambayoyi Ƙunyangun na zagaye da sarauniya suna ma fifita wacce take kuka wiwi tana cewa.
"Sanin kankune gobe idan mai bartaba ya dawo nice zan kwana ciki kuma kunsan ba ɓangarena take ba tana ɓangaran Kilishi ne to ya zanyi, taya za'ace aure saura kwana 5 Angel ta gudu ina xata bayan tana son Yazeed fiye da ranta..." Yazeed ya iso yace"Haba ranki shidaɗe kiyi haƙuri, duk zasu ɗanɗani kuɗarsu, inma wani abun ake shiryawa, to zai baiyyana da izinin Allah, aurena da Angel ba fashi, da izinin Allah ke! Mabaruka kin tabbatar babu hannunki a fitar Angel?" cikin kuka tace"Narantse da wanda raina yake hannunsa, bansa Ruwaida bata gidaba, sbd a yau banzo ba, kuma bata min text ba, tinda watarana muna kwana biyu bamu haɗu ba..." hannu ya ɗaga mata. Jakadiyace ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Ya kalli jakadiya cikin izza yace"Jeki atara duk wasu bayi da suke gidanan baki ɗaya, maza da mata Allah yaja da kwananki inaso ki ƙira Nanah kome take ta iso zuwa gobe gidanan, Ke ko Mabaruka bazaki koma gudanku sai mun gama bincike, ko nace sai kunci azaba wlh bazan ragama kowa ba..... Waziri ma yasan hakan, hukunci babu kan wanda baya hawa koda nine......Ashiru maza muje duk wani gidan Tv da redio dake cikin garinan da police station." yana gama faɗin haka ya sa kai ya fice, Ashiru na biye dashi. Jakadiya ta miƙe cikin rawar jiki ta fice. Mabaruka kuka take wiwi, Sarauniya ta goge hawayen fuskarta hankalinta a tashe ta beƙama wata kuyangarta hannu, naga ta rusuna har ƙasa ta bata waya, wata number ta laluɓo tai dialing ɗin number, bugu ɗaya aka ɗaga. Cikin tashin hankali tace"Nanah kome kike ki baro ki nemi ticket ɗin jirgi a yau cikin daran nan kizo Damagaram na faɗa maki Ruwaida ta ɓata, kowa zarginsa ake please ki taho duk da bakya gari hakan ta faru..." bata jira cewar Nanah ba ta tsinke ƙiran. Ta zauna dabas, kallo ɗaya ta masu kowa ya kama gabansa, cike da fargabar me zai faru gobe Mabaruka ta miƙe ta fice, tana sharɓar majina, ta nufi ɓangaran hajiya kilishi.
Tare da fadawa suka fita, duk wata kafa ta sadarwa gidan Tv redio babu inda basu jeba, suka bada sanarwa, saboda sanin dole mai martaba zai samu labari. Daga can suka nufi police station, harda pic ɗinta suka bayar, a lkcn aka bazama nemanta, haka suma duk wata kafar sada labarai ta yanar gizo sun sanar sun ɗora pic ɗinta tare da sanarwar bata mgn kurmace, amman tanaji, tinda daga baya ciwon ya sameta.

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now