*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~*Sadaukarwar page gareki👉🏻Hajiyar Tanimu Saratu mai ɗan ƙulli*~'''😆😝 yau pagen nakine kyauta.👌🏻 Wollah kiyi yanda kikaso dashi😻'''
*🤣Kwarankwatsi dubu yauma pagen ba yawa, ku taɓa ku lashe ne...😋😜🤪*
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 11*
Sheme take babu wani alamun motsin rai a jikinta, sai na'urorin da aka saka mata, ko ina a jikinta.
Abbaye ya ƙarasa da saurinsa ya raɓa ya zauna a bakin gadon, ya ƙura mata fitinannun idanunsa, wanda sauka canza launi, lallausan hannunta ya kamo ya damƙe cikin nashi yana murzawa ya rumtse idanunsa, zuciyarsa na masa wani irin zafi. Da hanzari ya buɗe idanunsa, ya rankwafawa ya ɗora kansa saman kanta, yana damƙe da hannunta yana murzawa da sauri², ciki mugun tausayinta, ya kai bakinsa saitin kunnenta ya janye dogon gashinta da ya rufe mata fuska, sabida Dr ya cire mata hijabi akan aikinsa. A hankali ya fara mgn.
Ruwaida! Meke faruwa dakene?? Cikin ƙanƙanin lokaci kika koma bakida banbanci da mataciyya." ya ƙarashe mgnr yana jan dogon numfashi, yana shafa kanta, yay bismillah ya fara karanto mata surah Yasin a cikin kunneta.
Dr ya fice ya rufo masu ƙofar. Safuwan cikin daddaɗar muryashi yake mata karanto mata suratul yasin ɗin cikin kunnenta yanayi yana ɗagowa yana tofa mata ajikinta, zuwa kanta yana shafa mata, har yakai ƙarshen surar ya dago yana kallonta, idanunsa yay arba da wani irin baƙin hayaƙi abun babu kyan gani, na fita daga bakinta zuwa hancinta. Tabbas idan bakada dakekiyar zuciya, a wannan lokacin idan ka kalli Ruwaida sai kaji mugun tsoro ka fita da gudu. Abbaye cikin dakiya hannunsa ya ɗora wajan bugun zuciyarta, zuciyar bata bugawa, bata motsi. Idanu ya zaro ya sake damƙe hannunta cikin nashi, ya tallafe fuskarta da hannunsa ɗayan, a hankali ya furta.
" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ruwaida! Meye wai ke faruwa dake!? Tabbas wannan lamari Allah zamu faɗama." Ya ƙarashe mgnr yana kai bakinsa dab da kunneta, yay bismillah ya sake fara karanta mata surar yasin ɗin, yana yi yana tofa mata a jikinta yana shafa mata ajikinta da kanta da fuskarta, sosai ya haye gadon ya shiga jikinta yana mata karatun tin ƙarfinsa bilhakki da gaskiya.
yana dab da ƙarshen surah yaji hannunta ya motsa wanda yake damƙe da nashi. Kallonta yayi yaga bugon zuciyarta na harbawa da sauri², cikin murna ya katse karatun ba tare da ya ƙarshan surar ba.......kashhh Abbaye!.😔 Ya kwanto jikinta ya ɗago kanta ya haɗe face ɗinsu yana jijjigata yace"Ruwaida! Tashi." zuciyarta kawai take bugawa da ƙarfi, bayan shi bata motsi.
Jikinsa ya janye ya miƙe ya sauko daga saman gadon ya fice ƙiran doctor. Yana buɗe kofa Mummy da Abbah suka nufishi. "Abbaye ya Ruwaida ɗin take?" Abbaye ya iso ya kama hannun iyayen nasa yana fesar da zazzafar
iskar bakinsa waje, ya ƙura masu fitinannun idanunsa yace."Mummy! Abbah!"
Ya ƙarashe ƙuransu yana jan dogon numfashi. Mummy ta jijjiga hannun nasa tace.
"Acp Abbay! Meke faruwa ne...?"
Dakyat yace."Wallahi aljanu ne Ruwaida gareta, bari na ƙira doctor ya dubata numfashinta na ƙoƙarin dawowa." ya faɗin haka ya saki iyayan nasa ya fara tafiya kai tsaye office ɗin doctor ɗin ya nufa saboda shike kula duk family ɗinsu. Mummy ta kalli Abbah tace"Kanaji Abban Taslim aljannu ne da ita to ya ya gane?" Abbah yace"To Bahijjah ina zan sani, ko Addu'a ya mata suka motsa ko, ya Allah ka shigo cikin wannan lamari Allah ka dubu wannan baiwa taka, ya Allah kasa ta tashi da bakinta, ka bata ikon faɗin inda iyayanta suke." Mummy tace"Ameen ya Allah."
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.