*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~*Fatan Alkhairi Ga Masoyen Ruwaida, Wallahi inajin Daɗin Yanda kuke Zuba Ruwan Comments, Da Sharhi, Kusani hakan yake Ƙaramin Ƙwarin Guiwa Nagode Masoyen Ruwaidah Rabbi Yabar Ƙauna🤝🏻😻*~
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 13*
A hankali ta isa bakin bed ɗin rabin jikinsa luluɓe da blanket, naɗe hannayenta tayi a ƙirjinta, tayi tsaye tana kallon kyakyawar fuskarshi, mai ɗauke da kyakyawan saja haɗi ƴar ƙasumba, ga ɗan gemun nan nashi mai kyau, da ya ƙara ƙawata farar fuskarshi, faffaɗan ƙirjinshi ta kalla wanda ke cike da yalwar gashi baƙiƙirin, kyakywan nipples ɗinsa a waje, kasancewar rigar bata maraba da singlet, yanayin girman take kallo masha Allah, gabanta taji ya faɗi.
Bacci yake sosai cike da nutsuwa yana fitar da numfashi sannu a hankula.
Kanta ta ɗauke daga kallonsa, ta kai kallonta geben ɗayan wayarsa, wacce take manne a chaji, murmushi tayi ta buɗe Passward ɗin wayar hannunta, ta shiga gun message ta rubuta masa.
*("Good morning yayana mai kirki, nazo na ƙare maka kallo kana bacci,😜 kuma anata ƙiranka a waya, ni bazan tasheka ba. Ya Abbaye Ngd da temakonka a gareni Allah ya tsaremin yayana ya kareka da dukanin sharrin abin ƙi, Allah ya barku da antyna, ya kuma kaimu ranar biki musha shagali na koma gidan yayana na zauna, Ya Abbaye please idan ka tashi ka fitomin da wayana, nayi missing ɗinta, kaji yaya Abbaye😥.)*
Haka ta rubuta masa bata fita ba daga gun message ɗin, ta ƙaraso dab dashi, ta ajiye masa wayar kan drower ɗin gadon, wani ƙiran ya shigo, ta taɓe ƙaramin ɓakinta, ta rankwafo dab da fuskarshi, ta beƙa hannunta zata shafa sajan fuskarshi, se tayi saurin janye hannunta tana murmushi ta ɗago da kanta ta juya sadab²ta. fice ta rufo masa ƙofar.
Tana fitowa ta isko Larai na jera kayan breakfast, akan dining Ta sallah na mopping ɗin parlo.
Tsaye tayi tana kallon Lairai, Larai tace"Ina kwana Ruwaida ya ƙarfin jikin ki?" murmushi tayi tana kallon Larai ta jinjina kanta, ta shiga haɗama kanta tea mai kauri, ta zuba sinasir da miyar ganye, taji naman rago, ko takan soyayen dankali bata bi ba.
Kujera taja ta zauna tayi bismillah ta fara shan tea ɗin da zafinsa, tana lumshe shanyayyun idanunta saboda yanda, takejin daɗin gumin da yake ratsa cikinta da ƴaƴan hanjinta. Saida tasha kamar rabi ta ajiye taci sinasir ɗin, shima taci sosai kafin take haƙura sbd bata fiye cin abunci ɗayawa ba.
Tana idarwa ta miƙe ta tattare kayan da ta ɓata ta nufi kitchen. Ta sallah tace.
"Masha Ruwaida! Allah ya ƙara lfy." Ruwaida tayi murmushi wushiryata ta baiyyana, ta jinjina kai, ta fice daga kitchen ɗin. Bedroom ɗinsu ta koma taga har yanzu bacci suke, juyawa tayi ta komo parlo ta kunna Tv, tashar sunnah Tv tana kallon wa'azi.*Niger*
Sinaye ce tsaye cikin wani ƙasurgumin jeji, tsakiyar wasu manyan duwatsu guda uku, wanda akai masu zanen Ƙudariiii ƙundaaaa na shan jini babu kyan gani, babu abinda zai baka tsoro irin manya² kahon da bakinsa da idanuwa da haƙoransa.
Wannan duwatsu, sune a tsakiyar wajan sun zagaye jejin, gurin bashida kyawun gani dole duk mai imani idan ya tsinci kansa anan yaji tsoro, ya nemi Allah ya kuɓutar dashi. Haka Sinaye take tsaye, tsirara haihuwar uwarta, gaban wannan manyan duwatsu babu kyan gani.
Jikinta ko ina tsuma yake tana faɗin. "Ya shugaba ina ƙara tuba agareka, wannan laifi ba nawa bane, Judaaaaaah tayi garaje nace mubi kome a sannu yaron nada haɗari, tace bai kaitaba, gashi har ta sami rauni, amman dole zasuci ubansu, dole nasan Ƙudariiii ƙundaaaaa, zai bamu sa'a mu aiwatar da aikinmu, sannu sannu bata hana zuwa, ayanzu dole zamu saurara mata kaɗan saboda gudun halaka sai sun sakankance, mu koma gareta, ina ƙara tuba kaina bisa wuyana." ta faɗi tana zubewa ƙasa kwanciyar rubda ciki ta beƙa hannunta suka miƙe ta haɗasu waje ɗaya tana wasu irin sambatu. Wata irin dariya akayi babu daɗin ji wacce ta karɗe duka jejin, cikin wata irin magana wacce masu karatu idan kukaji sai kunyi fitsari,😸ga maganar tana maimaici kamar mutum 10 ne suke yinta Nan take yake faɗin. "Duuuuduuuuuduuuu! ƙaaaaaaaa!! KO ina na jejin ya karɗe, yana faɗar " Zamu rama zamu samu nasara amma sai kinba uwar zumuɗi haƙuri yaron bazamu masa garajeba, zamu ɗaukota, nan kusa, amman Judaaaaaa! Tayi kuskure itama waye yace ta tono wannan kwalbar taje da ita badan nayi saurin janyotaba na maidata da bakinta ya buɗe kenan, ta tuna sunan kowa nata da mahaifarta, ta tuna alƙarta da kowa, itace zata tone mana shegen tsohon wannan mai son haɗa auren da Uwar gijiyarmu zaiyi sanaɗin barinta duniya. ni nasan badai biladama ba ya toneta, dan haka ki tashi ɓacemin da gani ɗago kanki kalli sharan hagum ɗinki kiyi kallo." yana gama faɗin haka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Sinaye ta waiga gefen da yace, idanu ta waro ta bushe da dariya, ta mike tace"Nasara tamuce na barka lfy ya shugaba." ta faɗi tana wasu irin surutai sai gata ta ɓace ɓat. Wajan tsafinta taima dirar mikiya, wasu irin halittune guda uku masu manyan idanu da dogon kai harshe waje ƙafafunsu na kofatone, idanunsu ƙwala² tamkar kare haka suke zazzaɗo harshe waje. Sinaye wani irin ihuuuuu! Tayi tana jijjiga, ta ƙira wata number, bugo ɗaya aka ɗaga tace"Mune da nasara, amman ku kama kanku zamu saurara masu zuwa ƴan kwanaki har ranar nasara na gani." kitt ta katse ƙiran. Tace da wannan halittun " Karku taɓata labari kawai zaku rinƙa kawomin haka Ƙundariiii ƙundaaaaa! Ya bada umarni, kuma nima ina ganin iya abinda ilimina yake nunamin ." ta faɗi cikin ƙaraji. Wannan halittun kai suka jinjina suna faɗin "An gamaaaaaa!" Ɓat suka ɓace. Sinaye ta bushe da dariya nan tayi wani sihirinta sai gata cikin shiga ta alfarma ta mutane sak ta sake ɓacewa.
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.