*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
https://t.me/joinchat/SZsoOxZNu0jO--Ly4vuMlg
~*DEDICATED TO*~
_Mah Sweety Ummah Hajiya Chalawa, kiji daɗinki💞💞💞_*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 20*
Tirjewa Ruwaida take tacika ta batse, ahaka suka isa wajan gadon tana tirjewa, Acp ya zaunar da ita, ya zauna dab da ita, yana riƙe da hannunta tana kiciniyar ƙwacewa, tayi kicin_kicin da fuska. Abbaye ya kalli Nadeer wanda suka tsare su da idanu suna kallon wata irin sahihiyar ɓoyayyar soyayya. Acp ganin irin kallan da suke masu, yasa ya tamke fuskarsa ya koma Acp Safuwan ɗinsa sak, yace "My friend bani kular nan." ya faɗa yana ɗauke kansa daga kallon su ya maida kan Ruwaida, wace ta cika tayi fam. Dr yace"Wai ni kam naga jinya ana, mara lfy shike lallaɓa me lfy, wannan ƙanwa tamu akwai sarauta, to Ruwaida adai yi haƙuri aba yaya abunci, yasha magani, Nadeer ka nuna masa na tafi." Dr ya faɗa yana tafiya.
Nadeer ya ɗauko kular dambun kifi da ƙwan da Rahma ta kawo, ya buɗe nan take ƙamshi ya gauraye ɗakin, ya beƙama Acp ya ɗora saman cinyar Ruwaida, ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago haɓarta, ya ƙura mata fitunannun lafiyayyun idanunsa, ya ɗan duƙo da kansa yay dab da fuskarta, har suna jin hucin junansu, ahankali ya ƙirata"Ƙanwata! Bani naci." ya faɗa yana sakin haɓarta. Ruwaida duk da tana halin ɓacin rai seda gashin jikinta ya ya miƙe yammm, amman ta basar dashi ta ɗauke kular ta ajiye inda ta tashi, zata toilet, riƙe hannunta Abbaye yayi baiyi mgn ba, ta kalleshi, fuskarsa ya tamke ya tambayeta da ido ina zata? Baki ta zumburo gaba, ta masa nuni wanke hannu zata.
Mayar da ita yay ta zauna ya ɗora mata kular ya kama hannunta ya sanya ciki ya tsakuro da hannunta ya kai hannunta bakinsa, tare da bismillah. Idanu ta ƙura masa fuskarta a haɗe, jin yadda ya sanya hannunta cikin bakisa, kai ta ɗauke tana turo ɗan ƙaramin jajayen laɓɓanta gaba.
Idanun ya lumshe sbd daɗi ya zare hannunta a bakinsa yana taunawa, yace" Oya bani ko na haɗaki da Mummy da Abbah." ya faɗa yana ɗauke kansa kamar ba shi ya mata mgn ba. Kallonsa tayi taga baya ko kallonta, jin yace zai haɗata dasu Mummy yasa ahankali ta saka hannunta cikin kular ta tsakuro dambun ta sanya hannunta ɗayan ta juyo da fuskarshi, tana tutturo baki takai masa dambun bakinsa, ya amsa yana ɗaga mata gira. Ruwaida dai bashi take yana ci kamar wani yaro, sosai yake jin daɗin dambun, saida yaji cikinsa ya ɗan cika na ƙarshe da ta ɗauko zata bashi ya riƙe hannunta ya juya yakai bakinta, ta kauda kanta, alamar bataci.
Safuwan yace"Baki isa ba wlh se kinci." yana faɗin haka yaja bakinsa yay gum, ya tallafe kanta yana bata, dole Ruwaida ta amsa tanaci sbd ya mata daɗi sosai. Yanda yake bata abaki da hannunta, yana mata hira gira da ta idanu, yasa taji haushinsa acikin kaso ɗari tamanin sun tafi, har ta manta fushin da take dashi ta saki jikinta tanaci. Hannunta ta jimƙe, ta riƙe hannusa tana jujjuya masa idanuwa alamar ta ƙoshi. Acp wani lafiyayyan murmushi ya watsa mata, wanda ya fito da zallar kyawunsa, dimples ɗinsa suka loɓa. Ruwaida bata san lkcn da ta sanya yatsarta ramin wajsn ba tana jujjuya yatsarta, tana murmushi, ta shagala da wasa da ramin dimples ɗinsa, hakan yasa sanya yatsunta abakinsa ya ciji yatsarta, ba shiri ta ɗago tana turo baki haɗi da gunguninta"Uhmm-uhmmm." ta miƙe ta nufi toilet tana gyatsa alamar ta ƙoshi tana yarfa hannunta.
Nadeer ya miƙe tsaye yana dariya yace"Tabdijam Amman na tausayama Rahma Ruwaida na shirin yin wuff da mijinta."Ya faɗa yana ɓaɓɓalo magugunan ya buɗe robar ruwa maras sanyi ya iso wajan Acp yana beƙa masa. Acp kuwa fuska yay ya haɗe gira sama da ta ƙasa Yace"Me ya kawo mgnr so...? Sanin kanka Rahma nake so, wannan baso atsaninmu, amanata ce, tanada nata mijin." ya faɗa yana kicin-kicin da fuska. Nadeer ya bashi magani yasha baice ƙala ba sai murmushi da yake, sbd yasan so baya ɓuya, dole sai sun fallasa sirrin zuciyarsu. Ruwaida lkcn da ta fito Safuwan ya kwanta, idanunsa lumshe, Nadeer na masa hira uhmmm ko ɗaga kai shi kawai yake baya mgn.
Ruwaida ta zauna bakin gadon, Acp ya buɗe idanunsa ya sauke su kanta, can ƙasan maƙoshi yace"Kina jin bacci?" Kai ta ɗaga, idanunsa ya lumshe yace"Ok kwanta gefena kafin su Mummy su iso." Kanta ta kwantar gefen matashinsa, ta saka yatsarta abaki tana tsotsa. Nadeer yace"Uhmmmm Allah bar ƙauna.... Knocking ɗin ƙofar akayi tare da buɗe ƙofar aka shigo tare da sallama. Hakan yasa Ruwaida ta ɗago kanta, ganin su Mummy ne ta miƙe cikin murna ta nufi wajansu. Acp ya buɗe fitunannin kyawawan idanunsa yabi Ruwaida da kallo ya lumshe idanunsa yana jin mugu-mugun tausayinta ya cika masa zuciya.
Ruwaida tana isa wajansu Mummy ta rungume Mummy cikin murna. Mummy ta ɗan buga bayanta tace"Ruwaida ashe yayan naki ya farka?" Abbah yay murmushi yace"Ruwaida! Mummy kadai kika gani ko?" Ruwaida ta saki Mummy ta iso gaban Abbah tana murmushi ta kama hannusa tana masa kwatance Acp yaji sauƙi. Taslim tayi murmushi tace"Ruwaida shagwaɓaɓɓiyar su Abbah." ta faɗa tana nufar wajan Safuwan. Islam tace"Ruwaida ya me jikin?" ta faɗa tana bin bayan Taslim. Ruwaida ta riƙo hannun islam tana mata nuni da yaji sauƙi, islam ta janye hannunta tana famar nishi dan kwandon kayan abincin ya mata nauyi, tabi bayan Taslim. Ruwaida ta waiga ɓangaran Acp. Idanunsu ya sarke waje ɗaya, gira ya ɗaga mata yana janye idanunsa anata, ya lumshe fitinannun kyawawan manyan idanunsa. Ruwaida wani zirrrr yarrr taji ajikinta, yanda ya lumshe mata idanun, basarwa tayi ta waigo tana murmushi. Abbah yana riƙe da hannunta suka nufi wajan Acp ɗin.
Taslim ta zauna bakin gadon suna gaisawa da Nadeer, tace" Nadeer sannu fa ya me jiki? Abbaye buɗe idanunka, naga fa yanxu ka gama kallon Ruwaida..." Nadeer yay dariya ya nufi wajansu Abbah ya taresu yana gashesu Abbah ya kama hannunsa da ɗayan hannun yace"Nadeer sannu ya jikin Acp ɗin?" Nadeer yace"Da sauƙi Abbah." ya faɗa suna isowa wajansu Abbaye'n. Abbaye ya buɗe tsumammun idanun nasa ya saukesu kan Taslim yana yamutsa fuska yace" Anty ykk?" Taslim tace"Allah ya ƙara tsare mana kai." Islam tace "Amin Ya Abbaye ya ƙarfin jikin?" Acp ya harareta yana taɓe baki. Mummy ta ƙaraso ta zauna tana faɗin"Kana halin jinyar ma? Sannu Allah ƙara tsare mana kai." ta faɗa tana kama hannunsa. Abbaye ya shagwaɓe fuska yace"My Mummy kamani to na zauna." Su Abbah suka iso Abbah ya saki hannun Ruwaida ya kamashi yana faɗin. "Alhmdllh Abbana sannu." Ya ƙarashe mgnr yana zaunar da Abbayen wanda ya wani langwaɓe jikin Abbah ɗin.
Ruwaida murmushi take ganin yanda Abbayen yake zuba shagwaɓa, iyayan nashi suna nan nan dashi. Taslim tace"Wannan kular daga ina?" Nadeer yace"Rahma ta kawo basu jima ba dai suka koma."Mummy tace"Allah sarki yarinyar kirki ta haɗu da iyayan kirki, ango da ciwo, to yanzu ya za'ayi ɗaga bikin za'ayi ko ƙaƙa ne...?"Abbaye ya lumshe idanunsa can ƙasan maƙoshi yace"Aa kar a A ɗaga."daga haka bai sake mgn ba. Abbah yace"Bappa da ummani na gaisheka ni na hana su dawo, islam zuba masa abinci yaci."Abbaye yace"No na ƙoshi." Mummy ta buɗe kular dasu Rahma suka kawo taga dambun kifi da kwai ne ssura ma kaɗan.... Sosai ta yaba masu, Ruwaida ta zauna bakin gadon dab da Acp ɗin, aɓoye ya kama hannunta ya damƙe anashi. Ta langwaɓar da kanta tana satar kallonsa ta milleshi a tafin hannunsa, yaji sarai ya basar, ya ɗago kansa suka haɗa ido ta shagwaɓe tana ƙif-ƙif da ido. Sam ba wanda hankalinsa ya kawo kansu.
islam ta zuba mata daddaɗan girkin da suka kawo taƙi ci ta nuna ta ƙoshi. Acp ya harareta ya mata nuni taci ta maƙale kafaɗa, tana zumburo baki tayi narai-narai da ido. Su Abbah dariya suke masu, Taslim tace"Ruwaida kizo mu koma gidana pls kinga Abbansu ihsan baya zama..."Ruwaida ta kalli Mummy da Acp wanda ya harareta, murmushi tayi iya fatar bakinta. Nadeer yace"Abbah bari naje gida nazo."Su Abbah sukayi ta saka masa albarka yama Ruwaida sallama da Acp ya tafi ya dawo. Hira suke cikin nishaɗi, jama'a sai shigowa suke ganin Acp, da dai ɗaya ake barinsu shigowa, abin tamakar fa gwamna sbd sosai aka zuba jami'an tsaro, Abbayen kansa yayi mamakin haka yake da jama'a.
Hamza shida Aneesa suka sake dawowa Ruwaida kuwa afakaice take zubama Acp shagwaɓa, sai ta koma ta noƙe. Ƙarfe 10 cif Abbah yace"Maza ku tashi direba yazo yana jiranku."Hamza yace"Aneesa kice ma mamarki gobe ta dafo mana farfesun kan ragon ta biyo dashi da safe." Aneesa tace"Ni gidan Anty zani tinda Ya Abbaye ya hana Ruwaida zuwa." Taslim tace"Yauwa ƴar gari muje to..."Abbah yace"Aa Taslim karki jamin ɗiya jeki abinki, Bahijjah ki saka yaranki gaba, Ruwaida ko zaki gidan Taslim ɗin?" Ruwaida ta kalli Abbaye taga idanunsa a lumshe amman fuskarshi a haɗe, sai jikinta yayi sanyi batace kome ba.... Abbah yace"Ya hana ko?? Dariya Taslim tayi tace"Bari zan rama."Mummy ta shafi kan Acp tace"Allah ya ƙara tsaremin kai sai gobe idan mun dawo." ta faɗa tana masa kiss agoshi. Abbaye ya buɗe idanunsa yana shagwaɓe fuska yace"I love u Mummy."Mummy tace"Me too." ta haɗa kan iyallanta suka fice. Taslim na tsokanar Acp bai ce mata ƙalaba, suka tafi. Shiko Abbaye gani yake idan yabar Ruwaida tabi Taslim kamar aljanun zasu iya saceta ne acan shiyasa ya hana. Idanunsa ya ƙara runtse sbd yana jin zafin wajan harbi, take ya shiga mamakin yanda ma akayi Alhj Sale ya zambace shi har ya harbeshi akafaɗa. Abbah ya fito da wayoyin Abbaye ya ajiye masa kusan matashi yace"My Abba a kunna wayoyin naka ne...?"Har zaice A'a ya tuna yana so ya ƙira islam ta bashi Ruwaida ya mata mgn akan tayi Addu'a idan zata kwanta sannan ya saka taje part ɗinsa ta ɗauko wayarta, ta kunna Baqarah, . Kai ya ɗaga yace"Abbah a kunna matsagaiciyar, ka akunna babbar, Abbah inason coffee." ya faɗa asangarce daga nan yaja bakinsa yayi shiru, ya lumshe idanunsa.
Su Mummy suna fitowa compound ɗin asibitin, bayan sunyi sallama da Taslim ta shiga motarta, Sani driver ya ɗaukesu suka tafi.
Ruwaida na jikin Mummy islam na gaba Aneesa na gefen Mummy sai hira suke, Ruwaida banda fuskar Abbaye bata ganin kome lokacin da yake bata abinci abakinta, yana watsa mata wani sihirtaccan kallo, ji tayi wani irin sanyi ya fara ratsa mata jiki, ta muskuta ta sake laɓewa jikin Mummy tana murmushi, kome ta tuna sai ta haɗe face, take ƙwalla ta ciko mata a idanu, ta sake shigewa jikin Mummy ta fara sauke tagwayen ajiyar zuciya... '''Kuci gaba da Ruwan Comments🤣'''
_*Rahma Oummu Fareesatu ce💋*_
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.