Chapter 5

388 21 0
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 5*

Kwana da yini tayi a cikin ɗakin bata buɗe ba, babu irin lallashin da Giɗaɗo bai mata ba, amman Ruwaida taƙi, ga yunwa da take ƙwanƙwalarta, se ruwa kawai take sha.
                Giɗaɗo ganin abin yayi yawa yasa ya ƙira mai gyaran kofa aka ɓanɓare kofar, ta bashi  tausayi sosai, ya shiga lallashinta.       Ruwaida ganin ba sarki se Allah yasa ta barma Allah kome ta saki ranta kamar gaske, amman koda wasa bata tsawa kusansa, nesa da nesa duk da baya ko kama hannunta, ya mata lallashin duniya ta faɗi garinsu ya maidata taki, ƙarshe ma kuka zata saka masa, sau biyu tana gwada guduwa daga gidan bata sami hanya ba.
                              Kayan dawa kala² ya siyo mata.       
                          Safuwan tinda aka bashi case ɗin Alhaji sule yake binkice sosai ya ɗana masa tarko waje dayawa, gwsmma kuwa numbersa aka bata so biyu ya batar da kamanin yana zuwa unguwar, sbd jama'a an sansa gidan Tv dole sai yayi taka tsantsan, yanxu ta waya yake ƙiranta, kan ya ganta yana so, zubinta ya mata, itako sakara ta hau ta zauna, tace yaxu yace shi baya gari zai sami dama yazo.....to ta haka yake mata wayo, yanajin cikinta, duk baya son mgn amman dole yake cijewa ta fannin aikinsa, yanzu lokaci yake jira na kama sale da temakon gwamma, cikin siyasa ba tare da tagane kome ba zai cafkesu.
                    Zaune yake cikin haɗadɗan office ɗinsa, yana juyi saman haɗadɗiyar kujerasa,   a nutse yake ba sigarin wuta, yana famar feso haƙi ta baki ta hanci.   Yana sanye uniform ɗinsu, wace tayi masa masifar kyau cikar zatinsa ta fito sosai.
                          Wayarsa ce ts ɗauki ringing, fitinannun kyawawan idanunsa da suke a lumshe ya buɗe, ya kalli haɗaɗiyar wayar dake ajiye a saman babban table ɗin gabansa, ganin sunan dake yawo ne saman screen ɗin wayar,  yasa ya beƙa kyakyawan farin hannunsa mai cike da yalwar gashi, ya ɗauki wayar.
                             Picking ɗin call ɗin yay ya manna wayar a kunnensa, cike da izza ya amsa sallamar, daga ji bayanin me mahimmanci ne sbd yanda ya bada hankalinsa baki ɗaya, yana sauraransa.     1 minute yay kafin yay mgn cikin daddɗar mursa yace.
                    "Ok DOC tnx so much, Dsp Samir ya ɗauki kamar mutum uku su bishi Abujar duk inda zai shiga ya kasan ce tare dashi." yana gama faɗin haka ya tsinke ƙiran ya ajiye wayar.   Wani ƙiran ne ya shigo wayar tasa, tsaki yaja yana kallon wayar, ganin Rahma ce yasa ya ɗauka ya amsa ƙiran ya kara wayar a kunnensa.   Daga can Rahma tace"My Acp nawan barka da yamma, nayi missing ɗinka sosai, ina ƙishirwar ganinka, sosai fa."Ta faɗi a sakalce.   Abbaye ya lumshe idanunsa yana juyi saman kujera, ya tura hannunsa cikin yalwatacciyar sumar kansa, a hankali ya furta.
                           "My dear ykk?"Rahma ta saka masa kukan shagwaɓa, yanaji tana bubbuga ƙafafunta, tace" My Acp ni banida lfy yo baicin jiya da yau baka zoba, se waya shima jifa²." Safuwan ya ɗan ja gashin kansa a hankali yace.
                  "Ok dear shiru zanzo." ya faɗi yana tsotsar lips ɗinsa na ƙasa.  Rahma tayi murmushi tace"Nawan kana nufin aiki yay maka yawa shiyasa baka zoba yanzu nayi shiru zaka biyu komy Acp?" Abbaye ya jinjina kai kamar tana kallonsa."koda taji shiru tasan amsar kai ya bata, tai murmushi tace.
                               "Ok Nawan se kazo Allah ya dafa maka cikin lamuranka abokin rayuwata."sosai yaji daɗin Addu'ar tata, yace.   "Ameen daer muahhhhhh." ya tsinke
ƙiran.   Yana ajiye wayar, ya kunna sigarinsa ya bata wuta, wata number ta ƙirasa ya ɗayan wayar ba suna ganin hakan yasa yaƙi ɗagawa, se da aka ƙira sau biyar ya ɗaga, ya manna wayar kunnensa baiyi mgn ba.   Nazifa daga can tace"Amincin Allah ya tabbata a gareka ya ma'abucin kyau da nagarta, ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwarka."Abbaye cikin izzar sa yace"Wacece?" Nazifa ta fara masa kauɗi, kitt ya tsinke ƙiran.   Ta sake ƙira yaƙi ɗagawa.        Nazifa ta jifar da wayar, ta ɗiro daga saman gadon tana kuka, ta nufi parlo.       Giɗaɗo yana zaune yana zuba uwar ƙarya akan yayi tafiya ne kwana biyu, yasha wuya a Nasarawa.....kukan Nazifa ne ya katse masa hirasa.  Ya zafga mata harara yace.
                               "Wlh idan baki  kama kanki ba zan sauya maki kamanni."  jikin Ummi faɗo tana haɗiye kukanta.  Mimi tayi dariya, tace"Yaya Jamil kasan me takewa kukan nan?" Giɗaɗo ya miƙe cike da ladabi yace"Ummi zan fita zuwa amsar wasu kuɗaɗena, se na dawo, amman dan Allah ariƙa sakama Nazifa idanu wlh idan ba hkaba zan karta." Ummi tace" Ikon Allah Giɗaɗo me ta maka ne?" baiyi magana ya fice.   Nazifa tace"Mugu kawai, keko Mimi wlh zan kirta maki rashin mutumci, ummi kawo kunnenki kiji wai harni za'ana wulaƙantawa."Ta faɗi tana kama kunnen uwar tai mata raɗa.
       Ummi tace" Ai dole ki ya wulaƙantaki kin zubar da kimarki ta ɗiya mace da Allah ya baki, wlh kar na sake jini."Nazifa ta saki ummi ta miƙe  ta shiga ciki.   Tana zuwa ta fara shirin tafiya gidansu Rahma, taci mutuncinta.
              Gwamma na tsakiyar karuwan gidanta, mai gurmi na nayi ganga na tashi, tana kunna sigari tana juyi gaban makaɗi sai iya shege ake da iface² maza da mata,  tayi ɗaurin ture kaga tsiya, tana taunar chingum. 
        Ƴar liba ce ta fito cikin shigar kamala kamar gaske, sai ƙirari sauran karuwan suke mata, da tambayar ta tubane...? Tana hura hanci ta rungume  gwamma suna rawa ana masu ɓarin nera.  Sun jima kafin ta janye, gwamma gefe, tace"Aunty zanje Abuja gobe zan dawo."Gwamma tace"Sai kin  dawo, nima nayi kimeme fa acan, wai da sale zaku ko sabon ɗaukane?''Ƴar liba tace"Yes shine wani taro suke na gaggawa kuma zai kwana shine ya gaiyaceni."Gwamma tace"A kwayo mana kayan arziki dai."Ƴar liba ta miƙe ta rataya jakarta tana dariya tace"Angama uwar ɗakina." ta faɗi tana tafiya.  A kofar gate sukayi karo da Giɗaɗo zai shigo.   Damƙe wuyan rigarta yay yace"Muje ki kashemin ƙishirwata, yarinyace kallonta nayi sai shaawa ta motsamin." Ƴar liba tace"Yasin bazan jiraba, ina sauri tab yaushe rabon da kace zaka kusanceni to bazanyi ba..."ɗauketa yay da mari ya damƙi wuyan rigarta yace.
                             "Kutumar ubanki karuwa maras amana, kin shirya zaki wajan wani, to sai na kashe ƙishirwata."ya faɗi ba kunya ɗauketa tana kuka, ya nufi ɗakinta.
    Magajiya tana kallonsu, ko ajikinta, saboda irin maƙuddan kuɗaɗan da Gifaɗo ke bata, tasan sale bazai bata ba.
Yana zuwa kofar ɗakin  ya iske a rufe, jakarta ya ciro a kafaɗarta ya duba key ɗin ya buɗe ɗakin tana kuka yay ciki da ita.   Tin tana noƙewa har ya samu kanta ta sakar masa jiki ya bugata sosai harda sambatu take.
        Bayan sun nutsu ya shiga yay wanka ya watsa mata uban damin kuɗi yay gaba, itako tana murna ta sake wanka da shiri bata bi ko ta kan gwamma ba ta tafi, saboda ƙiran da Sale yake mata....Giɗaɗo dake zaune a parlon gwamma yace"Please ki faɗamin ina ne garinsu kurmar nan, idan kuɗin ne bai miki ba na ƙara miki, wlh inason auranta, Wlh hkr na ya ƙare akan Baby ina sonta, ina son kusantarta bana son zina da ita."
                       Magajiya tace"Wlh yanda ka ganta haka na ganta, bansa ina ta fito ba, yo yaushe ka barta ta kwana wajena bare nasan daga inda tazo, wai kana nufin yau tsawon kwana uku, bakayi kome da itaba? To tana ina ne yanzu? Amman  ɗan gambo yace daga kano sukazo tare."Giɗaɗo yace"Ok ina ɗan gambo yake wlh zan basa ko nawa ne...?" Gwamma tace.
                         Ka ƙirasa kaji mana wai ina yarinyar take? muje mana na tambayar maka ita ." Giɗaɗo yay dialing ɗin number ɗan gambo, bugu ɗaya ya ɗaga.  Giɗaɗo yace"Don Allah idan kasan garinsu yarinysr nan kurma ka faɗamin." daga can ɗan gambo yace.
                   "Wlh a kano na ganta cikin bus ne muka haɗu bansa garinsu ba, gani ma a kano."Guɗaɗo yace"Ok nagode." ya faɗi yana tsinke ƙiran.
               Miƙewa yay yace"Zanje na lallaɓata zuwa dare ko zata faɗamin idan taki kuwa zan nemi iyayan haya a ɗaura mana aure amman yau sai nayi romance ɗinta, ko zan rage ciwon da yake damuna a zuciyata." ya faɗi yana ficewa.   Magajiya tace"Ɗan bariki kenan, shege uban ƴan iska, ka hanani neman kuɗi da Babyn nan, Allah yasa ta gudu..."

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now