*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~*Sadaukarwa gareku Ƴaƴana abin alfaharina, Shureim and Fareesatu Rabbi ya raya mana ku cikin tafarkin addinin musulumci*~
'''Alqura'an Yau bana cewa page yayi kaɗan haka ma zan maidohi Hudu²😸😸😸'''
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 12*
Parking space ya shigar da motar yay parking, kyakyawar fuskar nan tashi, babu walwala ko ƙaɗan, sigari ya kunna ya busa ya fesar da hayaƙin baki da hanci, ya lumshe fitinannun idanunsa masu kyawun gaske, sai yamutsa fuska yake yana ba sigari wuta. A haka ya shanye karan sigarin guda ya buɗe fitinannun idanunsa yana wani warosu waje, buɗe motar yay ya zuro da kyawawan fararen ƙafafunsa waje yana sanye da takalmin zalar fata mai kyan gaske, phone ɗinsa ya ɗauka ya shiga ma'adanar numbres ya lalubi number doctor Khalifa yay dialing, bugo biyu ya ɗaga. Acp yace"Dr nazo ina son ganin ƙanwata ne." kodaga jin mgnrsa ba wasa. Dr Khalifa daga can yace"Ok Acp yanzu bana asibitin bari na fadama Dr Junaidu." Abbaye ya jinjina kai yace"Ok Thanks." ya tsinke ƙiran. ƙarasa fitowa yay ya danna remot ya rufe motar ya zura hannayensa cikin aljihunsa, ya nufi cikin hosfital ɗin yana takunsa irin na ƙasaitattun maza masu ji da kansu, tafiyar Abbaye kadai abin sha'awace. Yana shiga kai tsaye ya nufi room ɗin da Ruwaida take. A kofar room ɗin ya isko Dr Junaidu, hannu Abbaye ya bashi sukayi musabaha, ya masa jagora har cikin ɗakin da take ɗin.
Dr Junaidu ne ya waro idanunsa cike da tsantsar mamaki ganin Ruwaida ta cire na'urorin jikinta tana fatali da kome na ɗakin tana wani irin gurnani dogon gashin kanta ya sauka har gadon bayanta ya hargitse. Da gudu Dr Junaid yay kanta. Ai kuwa itama kansa tayo gadan² tana wani irin gurnani. Kamantan da yake ta damƙi wuyan Dr da hannunta ɗaya ta ɗagashi sama. Acp ya waro idanunsa a guje ya nufosu yana faɗin" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!
"Ruwaida! Me ya sameki haka?" kafin yake isa ta buga Dr da ƙasa, ta haye samansa. Acp Ayatul kursiyu ya fara karantawa ya kamota da ƙarfi, ta fizgota ta rarumeshi iya ƙarfinta, ya goce mata bata taɓashi ba karatu yake iya ƙarfinsa yake ɗaga murya suna zagaya cikin ɗakin, Dr Junaid ya miƙe ya fita a guje ɗauko allurai, Ruwaida ta bishi, Acp ya saka iya ƙarfinsa ya damkota ya rufo ƙofar, kokowa suke ba dawasaba, ya samu ya kaita ƙasa yabita ya danne iya ƙarfinsa ya banƙare mata hannayenta ta baya ya matse ya kai bakinsa cikin kunneta ya dage iya yanda zai iya ɗaga murya yake karantu suratul baqarah yake karantawa tana wani irin ihuuuu. Wani irin baƙin hayaƙi ya fara tashi a cikin ɗakin, kafin me ɗakin baya ganuwa ɓaƙiƙirin ya tirniƙe da duhu, cikin hayaƙin nan mgn ta fara fita babu daɗin ji "Haƙiƙa idan Judaaaaaa taji ciwo rayuwarku na haɗari zamu dawo yanzu mun gudu, sai mun saceta kasa ido ka gani." aka ƙarasa mgnr ana kecewa da wata irin dariya. Acp ko ajikinsa kartunsa yake kawai babu ƙakƙautawa. jikin Ruwaida ya ɗauki wani irin kyarrrrrma, wani irin ihuuuu ta saki mai tsananin ƙarfi. Tare da atishawa jikinta ya saki lakwas. Hayaƙin nan ɓat ya ɓace babu kuma alamar ƙaurin hayaƙi ko wani abu.Safuwan wata uwar zufa ce ta keto masa, sbd tsananin mamakin wannan lamari, amman sam bai daina kartunba dan yayi niyya ko zaikai asuba a haka sai ya karancema Ruwaida Baqarah baki ɗayanta, Jin yanda Ruwaida take sauke numfashi tana mutsu² da hannunta alamar tanajin zafin banƙara da yay mata, yasa ya saki hannun ya ɗan mirginata gefe, rabin jikinta manne da jikinsa, still bakinsa cikin kunneta, ya dage yana mata karatu. Dr Junaid ya shigo ɗauke da alluran, kallonsu yay yace"Acp da amata alluran zai fi ko?" Abbaye baiyi magana ba, karatunsa yake Dr gefe ya koma ya zauna saman gadan. Bayan 1 hour, Ruwaida ta buɗe manyan kyawawan fararan idanunta tar, cike da mamaki ta waigo jin murya yayanta a kunnenta, tana shirin kallon Acp ya juyar da kanta ya sake maida bakinsa saman kunneta yana mata karatun, idanunta ta lumshe tanajin daɗin karatun sosai, tana mmakin to me ya kawosu hospital yake mata karatu? Hannunsa ɗaya ta kamo ta damƙe cikin nata gam, tana wasa da zoɓen hannunsa ta ƙara shigewa jikinsa, yatsarta wacce ta saba tsotsa ta saka a baki tana tsotsa, a haka har barawo bacci ya ɗauketa, tana fitar da numfashi cikin nutsuwa.
Sai ƙarfe biyun dare cif Safuwan ya gama karancema Ruwaida suratul baqara cikin kunneta, tana manne jikinsa tana baccinta cike da nutsuwa.
Bakinsa ya janye daga cikin kunneta, ya zame hannunsa da yake damƙe a cikin nata, ya janye jikinsa daga nata ya miƙe tsaye, kansa da bakinsa na masa azabar ciwo, tinda uwarsa ta haifesa bai taɓa rabin kwatankwacin ihun da yayi yauba, baima taɓa sanya ran akwai abinda zai saka yayi mgnr 30 second ba, ba tare da yaja burki ba. Kansa ya ɗan dafe ya saki ya sunkuya ya cicciɓeta sama, ya kalli Dr da yake bacci saman gadon da aka kwantar da Ruwaida, ƙiransa. "Dr! Dr!" Junaid ya buɗe idanunsa ya miƙe yace"Sannu Acp kwantar da ita na mata alluran na haɗasu." Abbaye ya kalleshi ya yamutsa fuska, dakyat yace"No baxa asake mata alluran kome ba, ni na wuce gobe zanga Dr Khalifa." yana faɗin haka ya nufi kofa yana rungume da Ruwaida tana baccinta cikin nutsuwa. Dr Junaid ya iso ya buɗe masa kofa yace"Ok Acp Allah ya ƙara bata lfy se da safe, nima naji jiki har allura nama kaina sbd nasan kadin nan sai ya taɓamin lafiyar jikina." Abbaye baiyi mgn ba kai jinjina ya fice.
Yana zuwa parking space ya zaro remot ɗin daga aljihunsa ya danna motar ta buɗe seat ɗin baya ya kwantar da ita ya rufe kofar ya zagaya ya shiga ya shiga mazaunin direba yaja motar yana zuba horn, megadi cikin bacci yaji horn ya fito a sukwane ya buɗe masa gate ɗin ya fice a guje.
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.