*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 9*
Safuwan ya waro fitinannun manyan idanunsa waje, yana kallonta cike da mamaki, sake damƙe hannunta sosai yay a cikin nasa, yana murzawa a hankali ya ƙira sunanta cikin daddaɗar amon muryasa yace.
*"Ruwaida!"* wani irin yamma zirrrr taji, a dukan ilahirin jikinta, saboda daɗin yanda ya ƙira sunanta. Rage shasheƙar kukan tayi, ta kifa kanta saman hannunsa wanda ya damke hannunta, tana kukan a hankali.
Abbaye lips ɗinsa na ƙasa ya ciza ya lumshe fitinannun idanunsa, ya ɗora ɗayan hanunsa saman kanta yana shafawa, a hankali haɗi da ɗan buga bayanta.
Shiru tayi tana maida numfashi ta sake tura kanta cikin damtsan hannunsa, tana shaƙar daddaɗan ƙamshinsa mai rikita mata lissafi.
Abbaye ya buɗe idanunsa ya kalleta ganin ta lafe a rabin jikinsa sai sauke ajiyar zuciya take, kanta ya ɗago yana kallonta, itama kallonsa tayi, cikin wani irin baƙon yanayi suke kallon junansu. Da sauri ta sadda kanta ƙasa jikinta yayi wani irin sanyi tamkar an zare mata laka, har wani ɗan sanyi takeji ya fara ratsa sassan jikinta, saboda wasu irin kibiyoyi dake fitowa daga cikin idanun Abbaye suna harbin idanunta, bayan hakan ƙwayar idanun Acp Allah ya masu wata irin baiwa yanada wuya ka iya haɗa idanu dashi kai tsaye ba tare da kaji wani abu ba. Fuskarta ya tallafe a cikin wani irin cool voice yace.
Zaki bini na tafi dake ko?" Cikin zumuɗi ta ɗaga kanta hawaye na fita daga fuskarta, tana murmushin jin daɗi, dan tasan tunda ya tambaya to zai tafi da ita ne. Kai ya girgiza yana kallon gefen kyakyawar fuskarta yace "Ok naji shiru." ya faɗi yana kama fuskarta ya goge mata hawayen da hannunsa ya jinginata kafaɗarsa yana buga bayanta. A cikin muryasa mai fitar da amon daɗi yace"Ba zan maidoki ba...." ya faɗi yana tsayar da mgnr yaja dogon numfashi, ya ɗago da fuskarta yaci gaba da cewa"Sai na gama uzurina zamu dawo zuwa dare..." ya faɗi yana jan gashin girar idanunta mai tsayi.
Cikin murna ta kalleshi tana dariyar murna ta jinjina kanta, ta shafi sajan fuskarsa ta kama dohon hancinsa taja, tare da gemunsa tana murmushi, gira ya ɗaga mata ba tarw da ya wani saki fuska ba. Baki ta ɗan zumburo gaba, ta matsa ta gyara zamanta ta rufo kofar motar. Acp bai sake mgn ba, yama motar key ya nufi gate, yana zuba horn, dan megadi ya gaji har ya sake rufe ƙofar. Wangame masa ƙaton gate ɗin yay Acp ya solala hancin motar waje aguje.
Saman titi ya hau yana sharara gudu, cikin ƙwarewarsa yake murza stirring motar, Ruwaida sai kallon titi take ranta fari tas, kai tsaye police station ɗinsu ya nufa.*Niger*
Cikin ƙurgumin dajin nan bakaji kome, sai wasu irin kuka marasa daɗi cike da abin tsoro.
Zaune take gaban bokanya Sinaye, ta gurfane tana famar wasu irin sambatu. Sinaye kuwa yau halittar tata ta canza, idanunta sun zazzago sosai faracan hannunta da ƙafarta kuwa abin babu kyan gani, zaune take saman jan ƙyalle ƙatonɓkaho tsakiya kanta, ƙaton ƙoƙo a gabanta ta ware gunduma-guduman hannunta, sama, tana wasu irin sambatu da ƙarfi, dajin ko ina amsawa yake, haka kukan da yake tashi adajin dole yaba mutum tsoro, gamanyan duwatsun nan masu zame ƙaton gumaka suna wani irin motsawa, haka bishiyar tsamiyar nan sai wani irin ƙaran abu mara daɗi kakeji. Da ƙarfi sinaye tace.
"Kama bakinki haka, ya isa nagama ganin kome, ga shugaba na isowa." Cikin ɗaga murya tace"A taimaka ya mai girama Sinaye kome ya kusa caɓewa gaskiya na neman fara baiyana a kashesu kawai bana son jin kunyar duniya..." Sinaye ta bushe da wata irin dariya, saida dajin ya amsa, tace"Ƙundariii! Ƙundaaaa!! Ta faɗi tana saka hannunta cikin wannan ƙaton ƙoƙan wanda yakai biyun na ranar se dai wannan rabinsa jini rabinda wani abune wanda sam ilimina ba zaikai wajan ba. Wata irin iska ce ta tashi ta karɗe baki ɗayan dajin sai ga wata irin guguwa nan baƙi ƙirin ta taso ta rufe ɗakin tsafin baki ɗaya, baka ganin kome, sai wasu irin surutai ke tashi da dariya, murya abin tsoro, duhun ya fara yayewa sai wani baƙin hayaƙi ya fara baibaye ƙaton ƙoƙon nan, take wata ƙatuwar hallita babba da ƙarama suka baiyyana, masu manyan ƙaho a tsakiyar kai, idanunsu jajur kamar garwashin wuta, ƙwala ƙwala kamar zasu faɗo waje, harshensa najan ƙasa. Sinaye ta zube gabansu. Tace"Mai girma Ƙundariii! Ƙundaaa! Da Judaaaaaa Barka da zuwa." Wani irin ihu ya saki yana dariya cikin wata irin muraya wacce idan kanada tsoro ya isa ka suma yace"Babu damuwa aci gaba da abinda ake na gayamaku sai kome ya faru, amman zamu iya hana kome da ƙarfin tsafi ni ina tare da duk wanda ya bijirewa mahaliccinsa, dan haka basu isaba sai munga bayansu . Ya ƙarasa maganar da ƙarfi ɗakin saida ya jijjiga, ko ina na dajin se da ya amsa. Wannan ɗan ƙaramin da suke tare dashi mai manyan haƙora zaƙal² Mai suna Judaaa ya beƙa dogon hannunsa wanda bashida iyakar tsayi sai ga wani ƙaton ɗauri ya janyo ya zura zabgegen harshensa ya janyo sinaye ya naɗeta saida ta saki ƙara ya damƙa mata ɗaurin a hannunta ya saketa. Wata irin guguwa ta tashi ɗakin yay baƙiƙirin, 1 minute haske ya baiyana. Babusu sun tafi, Sinaye ta kakaɓe da dariya tana zaro idanu, tace"Karkiyi fatan mutuwarsu a yanzu saboda daidai take da taki mutuwar, domin abinda Ƙundariii Ƙundaaa da Judaaah suka faɗamin a yanzu idan kinji zaki saki zawo, bazan iya faɗa miki ba, amman zamuyi nasara ba kisa idan dai ba mun sake babban tsafi akan kisanba, sunada ƙarfin Addu'a idna muka matsa mune zamu lalace, shiyasa nake cewa abi kome a sannu." ɗaurin nan ta saka cikin ƙoƙon da Ƙundariii da Judaaaah suka gama shanye abinda ke ciki tana sakawa ta kifa hannunta a ciki ta juya har sau uku, ta ɗago ta kalli matar wacce kana kallon idanunta babu tsoro sabida rashin imani, tace"Matso ki ɗauki ƙullin nan ayi ƙoƙarin duk wani halitta dake cikin gidan yaci shi tabbas shima madafarmu ne kome zai ƙara shafewa, wannan baba tsohon aikinsa Ƙudarii ƙundaaa yake, dan shine ranar da ya fito akwai babbban tashin hankali sai ya tone sirrin ɓoye haramtacciyar alaƙar da mukeson haɗawa saboda biyan buƙatarmu bazai samuba, saboda ƙarfin rabon dake tsakaninsu." ta faɗi da ƙarfin gaske tana zazzago idanunta tace"Tashi maza inada babban aiki sai naga shugaban Matsafan duniya." Jikinta na kyarrrama ta saka ɗaurin cikin rigarta ta fara jan ginɗi kamar yanda ta shigo, tana faɗin "Ya Shugaba Ƙundariii Ƙundaaa ya ƙara maki ƙarfin tsafi na barki lafiya mune da nasara, baba tsoho yayi kaɗan ya hanani cikon burina." a haka ta fice. Sinaye ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, ta miƙe tsaye tana wasu irin sambatu sai hayaƙi ya turnuƙe ɗakin ta ɓace ɓatt...
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.