Chapter 32

389 17 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

_*NA*_

_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_

*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

https://www.wattpad.com/story/256436795


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 32*

Glass ɗin motar ta ƙwanƙwas tana faɗin. "Samira bye zanji da ogana." ta faɗi tana yanke ƙiran. Acp ya buɗe mata motar ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Amsawa yayi yana ɗauke kansa daga gefenta.
Cike da kissa tayi ƙasa da murya tana faɗin"My Qalbi ina yini." Acp ba tare da ya waigo ba, cikin izzarsa yace" sbd me ina ƙiranki kika ƙi ɗauka? Kinsan babu abinda na tsana irin ƙin ɗaukan ƙira!! Ki kiyaye." Rahma ta ƙura masa ido cike da jin haushin tambayar da yay mata, da nuna fushinsa, yana nufi har ya manta me yay mata? Yaƙice takaicinta tayi, cikin kwantar da murya tace"kayi hƙr nawan ina toilet wayar na cikin ɗaki, lkcn da zan mayar maka da ƙiran lkcn kazo fa." Ta faɗa A shagwaɓe.
"Ok"
Yace ya ɗan kalleta ya kuma cewa"Hope dai kinji sauƙi?" itama tana kallonsa tace"Eh naji Qalbina." ƴar hararata yay yace"To zan isa gida na huta, tin safe rabona da gida..." ya faɗa cikin jan numfashi sosai. Rahma tace"Sannu my Acp nah, kaje ka hutu toh." hancinta ya ɗan ja da ƙarfi ya ɗaga mata kai alamar "Ok" Rahma ta buɗe motar ta zuro ƙafafunta waje, ta waigo tace"Seda safe Allah ya huta gajiya nawan." ta faɗa tana jan ɗan guntin gemunsa, ta fice ta rufo motar tana dariya. Acp murmushi ya ɗan saki, yabita da ido, yana ma motar key yabar layin nasu.
Rahma da sallama ta shigo gidan. Zainab da Babansu suna hira yace" Har ya tafi ko? Masha Allah." Rahma tace"Eh Baba. Ɗaki ta nufa inna nata linke kayanta, wanda ta firfito dasu ɗazu ta zaɓi na tarbar baƙi. Rahma ta amsa tana faɗin"Bari na linke miki innata..." inna tace"Ya naga hannunki baƙiƙirin ba wani haske? Halan bai baki kome ba? Ko ɗan madaran ruwan nan me kumfa².."?
Rahma ta rufe mata baki tana faɗin"please innata! Ki daina hakan babu kyau, wlh banajin daɗi ai lafiyata yazo dubawa ba wai wani abu zai kawomin ba." inna ta ƙwace bakinta tace"Ke kika sani." ta fice tabar ɗakin. Rahma ta shiga linke kayan tana mayar dasu ma'ajiyarsu.
Zaune suke acikin falo anata hira gwanin sha'awa. Ruwaida na kusan Mummy, idan anyi abin dariya murmushi take, sai ta tafa hannunta, tayi tsaf abinta tana sanye da ɗan ƙaramin hijab ne, milk colour ya fito da kyan fuskarta sosai. Widaad tace"Abbanmu! Gsky anko kala ukun nan da aka mana tayi kaɗan, a ƙaro mana biyu na musamman, zamu samu ɗinki wajan Nasiru tinda yauma saura sati..."islam tayi caraf tace"Yauwa ƙanwata gaskiya aƙaro mana lace da shadda, ko Ruwaida?" ta tambaya tana kallon Ruwaida.
Ruwaida Mummy ta kalla tana murmushi. Mummy ta rungumeta tace"Basu amsa mana dota." Musaddiq yace"Mummy ai kinsan bata cikin haukansu ba." Fu'ad ne zaiyi mgn sukaji sallamar Acp. Tsuru² sukayi da idanu suka haɗiye mgnrsu. Sallamar suka amsa masa. Ruwaida ta ɗago da kanta, cikin farin ciki ta kallesa tana murmushi.
Shima murmushin ya mayar mata. Abbah yace"Sannu Abbanmu ya gajiya?" Acp ya iso ya zauna kusan Abbah ya zauna yace"Abbana gajiya yunwa bacci." ya faɗa yana yamutsa fuska. Mummy tace"Sannu namijin duniya tashi maza kayi wanka ka cika cikin ka." ba musu Abbaye ya miƙe yana kallon Mummy yace"Mummy ya jikin kanwata?" Mummy ta shafa bayan Ruwaida tace"Alhmdllh taji sauƙi sosai taci abinci." kai ya jinjina yana kallon Ruwaida wacce ta sadda kanta, tana wasa da siririn yatsotsin hannunta. Kallonsu islam yay yace"Akoda yaushe ina son ya kasance wayarku na ɗauke da karatun Qura'an sannan ku kasance masu yawan karatanta fiye da baya, saɓanin hakan na kama yarinya na sauraran kiɗa agidan nan wlh kashinta ya bushe." ya faɗa yana zabga masu harara, yasa kai ya fice yana faɗin"My bro ango ya gida?" ya faɗa yana tafiya.
Dariya Mummy da Abbah da Musaddiq sukayi, atare suke faɗin"Kai ɗin fa?" Ruwaida ta saci kallon Acp yanda uniform ɗin ta kamasa, yana wani takunsa me tsayawa arai... Sosai yayi mata kyau.. Shanyayyun idanunta ta lumshe tanajin kamar taje ta bisa tai ta kallonsa. Widad tace"Toh Abbah tinda dodo ya tafi, yane zancan ƙarin ɗinkin namu?" Mummy tace"Bazamu ƙaraba, duk irin kayan da kukeda sabbi wasu baku taɓa sawaba, kaya kala uku ya isheku mana." islam tace"Mummy munji abar maganar." Ruwaida murmushi tayi tana buɗe idanunta. Ta miƙe tsaye ta nufi bedroom ɗinsu. Tana zuwa alwala tayi ta zauna saman darduma, ta ɗauki Qura'an me girma tana karatu. Acp yana zuwa ya cire uniform ya shiga bathroom shower ya sakarwa kansa. Yajima kafin ya fito ya murje jikinsa da daddaɗan lotion me ƙamshi, da kuma taushi ya shirya cikin ƙannaun kaya ya feshe jikinsa da daddaɗan turaruka ya fice. Kan dining ya nufa, Mummy najin motsinsa taje ta zuba masa lafiyayyan girki mai daɗi, suna hira sama² akan abinda ya shafi Ruwaida nan take faɗa masa tana ɗaki tana karatu. Dan tana tashi Mummy tabi bayanta, ganin abunda take yasa tace dasu islam karsu shiga su barta tayi karatunta anutse.
Haka suka kasance da mahaifiyarsa, har ya gama cin abincin, suka dawo falon.
Mummy tasa aka haɗo masa coffee me daɗi. Yana gama shan coffee ɗin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsu Ruwaida yaga halin da take ciki. Zaune take saman darduma ta rungume Qura'an tana gyangyaɗi.
Ƙofar ya murɗa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Tozali yayi da ita tana gyangyaɗi. Acp ya iso dab da ita ya rankwafo ya sanya tattausan hannunsa ya janye Qura'an ɗin da ta rungume a hankali ya fara zarewa har ya zare luuuuu tayi zata kai ƙasa ya sanya hannunsa ta kifa kanta ahannunta, bacci sosai Ruwaida take. Safwan idanunsa ya tsura mata yanada yaƙinin sheɗanunan ne suka sakata bacci tabbas yasan Ruwaida na neman temakon gaggawa cikin rayuwarta. Ba tare da tunanin kome ba ya cicciɓeta sama ya nufi saman gadon da ita. Idanunta ta buɗe cike da firgici. Ido suka haɗa. Yace"Oya bacci." idanunta ta ƙura masa, sai kuma ta lumshesu, ta maida kanta saman ƙirjinsa ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya, ta zagaye hannunta bayansa take taji wata irin nutsuwa, ga wani irin daddaɗan ƙamshinsa da ya bata wata irin nutsuwa, kamar walƙiya baccin ya kuma ɗauketa.
Bakin gadon ya isa ya kwantar da ita tare da bismillah, ya rankwafo yana tofeta da Addu'a ta riƙe hannunsa gam haka take baccin. Aƙalla yakai 30 minutes yana tofeta da Addu'a, ya shafe mata fuskarta ya ɗauki wayarta ya kunna mata suratul baqarah, ya ajiye mata kusan kanta, ya zare hannunsa cikin nata, ya lulluɓeta da lallausan bargo, ya miƙe ya ɗauke Qura'an ɗin ya linke dardumar ya ajiyeta A muhalinta. Juyowar da zaiyi ya nufo ƙofar fita suka haɗa idanu da Mummy da Abbah da Musaddiq suna tsaye suna kallonsa. Lallausan murmushi ya sakar masu, yana shafa lallausar sumar kansaya iso wajansu Abbah yana faɗin"Abbanah!!! *Kuyi manage ina busy ne.😻*

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now