*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~*DEDICATED TO*~
_My Amritie Nafisat Mrs Bukar_
_Kiji daɗinki Allah ya ƙara danƙon ƙauna keda Bukar🥰__*Ku Taɓa Ku Lashe Ne Fa🤣🤣🤣*_
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 19*
Ruwaida mayan fararan idanunta ta warosu waje duka, tana kallon yanda Rahma take wani rawar jiki akan yayan nata, harda gudu. Haka kawai taji ranta ya ɓaci, amman da ta tuna ɗazu da rana dan ta ƙele Rahmar ya mareta, sai kawai ta kauda kanta ɗaga kallon Rahma ɗin, ta basar. Waigowa tayi ɓangaran Acp, taga hankalinsa Akan Rahma yana watsa mata lafiyayyan murmushi, mai sanyaya zuciyar masoyi, yana ƙoƙarin miƙewa zaune.
Ruwaida hauahin hakan yasa ta miƙe da sauri, ganin abinda yake ma Rahmar, taji haushi sosai, kamar an jefota gaban Safuwan, sai gata atsaye gabansa, tayi saurin zama bakin gadon ƙwalla ta tarun mata, acikin idanunta, tana kallonsa ta sanya lallausan hannayenta duka biyu, saman kafaɗarshi, tana ƙoƙarin tashinsa. Kallonta yayi cikin zazzaƙar muryashi me ɗauke da amon daɗi, can ƙasa yanda ba wanda zaiji ya furta “Sakeni bana so, tin ɗazu nake miki mgn kika shareni.....yaja dogon numfashi sakammakon jin da yayi mgnr ta masa mugun tsayi bazai iya ƙarasata ba, kai tsaye. Ruwaida ta zumburo baki gaba ta ɗaga ƙafada alamar bazata sakeshi ba, har ta fara shasheƙar kuka, ta kama Acp tsaf ta zaunar dashi, ta kifa kanta gefen kafaɗarsa tana shasheƙar, kuka, tana jin yanda bugun zuciyarshi yake fat-fat, da karfi. Rahma wace tinda taga Ruwaida ta miƙe ta zauna bakin gadon ta kama Acp, jikinta yayi sanyi, wani matsanaicin kishi ya rufeta, amman ta dake, ta ƙaraso bakin gadon ta matso da kujera da Ruwaida ta tashi ta zauna, tana kallon sarautar Allah wajan Ruwaida, tinda taga Abbaye ya tamƙe fuska tam, yana mata mgn kuma tabbas tasan cemata yake karta taɓashi, duba da yanda bayan ta tashesa ta kifa kanta gefen kafaɗar tashi, tana shasheƙar kuka bai tanka taba saima idanunsa da ya runtse.
Asma'u da Zainab, suka ƙaraso suna murmushi dan su abin dariya ya basu, ganin ita Ruwaida sam bata san ɗan uwan nata yana neman temako ba, saida suka shigo ta waiga taga yana ƙoƙarin tashi, gefe ɗaya kuma sun tausaya mata, saboda kurmancinta. Rahma ta kama hannun Acp cikin tanƙwasa harshe tace. “My Acp! Sannu ya jikin? Allah ya ƙara maka lfy, wlh da farƙo nazata mugun harbi aka maka, sai yanzu hankalina ya ɗan kwanta....pls kayi hakuri ka rarrashi ƙwanwarmu, Ruwaida kiyi haƙuri, yayan ki baya fushi dake.” Rahma ta faɗa cikin jarumta, tana riƙe da hannun Acp. Abbaye ya buɗe fitinannun idanunsa, ya sauke su kan Rahma ya sakar mata tsadaddan murmushi, ahankali ya furta,“My dear ki barta ta raina ni ne...” ya faɗin haka ya ɗora hannunsa tsakiyar bayan Ruwaida ya ɗan bugi bayan nata kaɗan ya mintsineta yace“Oya ɗagani, ke ko kunyar matata bakya ji?” Ruwaida najin haka tayi saurin ɗago da kanta, ta kalleshi hawaye ya wanke mata fuska, ta haɗe hannunta alamar yayi haƙuri bazata sake ba.
Ta juyo tama Rahma kamar yanda ta masa ta miƙe tana goge hawayen fuskarta ta koma saman kujera ta zauna. Acp ya girgiza kansa. Rahma tace“Ƙanwata dan yayanki na miki wasa kikayi fushi ko?”Ruwaida ta saki murmushi tama Rahma nuni da hannunta“A'a ba fushi tayi ba.
Asma'u da Zainab da suke gefe zaune suka ce“Abbaye ina yini sannu ya ƙarfin jiki? Allah ya kiyaye gaba. Acp ya amsa da“Amin anty! Zainab ya karatu?” Zainab tace“Ya Acp muna taɓawa. Rahma tayi murmushi tana kallon Acp tace“zakaci wani abu na zuba maka?” Safuwan ya girgiza kansa yace. “ Ba yanzu ba. Ya faɗa yana kallon gefen da Ruwaida take zaune, bata ko kallon su, kanta aƙasa. Idanunsa ya lumshe ya fesar da zazzafar iskar bakinsa waje.
Rahma tace miƙe dam ta nufi ƙofar idanunta kan Ruwaida, ta ɗauke kanta tana tafiya, Ruwaida ta ɗago jin takun tafiya. Ido suka haɗa Rahma ta sakar mata murmushi. Ruwaida ta mayar mata, tana tambayarta da hannu ina zata? Rahma ta nuna mata ƙiran Dr zata. Ruwaida ta miƙe ta iso gaban Rahma ta kama hannunta, Rahma tanajin haushin Ruwaida amman ganin Ruwaidar ta sauƙo yasa ta basar ta damƙe hannunta ta buɗe ƙofar suka fita. Acp idanunsa a lumshe jin ƙaran buɗe ƙofar yasa ya buɗe idanunsa yaga Rahma da Ruwaida sun fita Rahma tana riƙe da hannun Ruwaida. Kai Acp ya girgiza ya sake lumshe idanunsa. Tinda suka fita Ruwaida kebin ko ina da kallo, sosai asibinti ta mata kyau, kallon ƴan sadar da suka baza aaibitin take, tamkar wani gwamna ne aka harbe, Ruwaida kallon wanda suke dafifin zuwa kallon Acp take, amman police ɗin nan sun hanasu sai ta window suke leƙensa.
Rahma wata nurse ta tambaya, ta nuna masu office ɗin Dr. Suna zuwa office ɗin Dr Rahma tayi knocking ɗin ƙofar. 2 minutes Dr ya buɗe masu ƙofar,
Rahma ta gaishesa tace“Daman Acp Safuwan ne ya farka. Dr yace“Ok gani nan zuwa.” ya faɗa yana kallon Ruwaida yace“Ruwaida ƙanwar Acp. Ruwaida bata kalleshi ba, ta kalli Rahma tana ɗan turo baki gaba, kasancewar shagwaɓa ta zauna ajikinta. Rahma batayi mgn ba, ta kama hannunta suka bar wajan. Dr murmushi yay yace“Yarinyar nan na sigani wlh.” ya faɗa yna komawa office. Suna komawa room ɗin da Acp yake Ruwaida ta zauna saman kujera da ta tashi, ta sadda kanta. Rahma zauna kusan Acp can ƙasa² tace “My nawan Inasu Mummy da Abbah, su Widaad islam Aneesa?” Acp ya buɗe idanunsa ya ɗan jingina da pillow bai dai yi mgn dan baima san duk sun zo ba, kai ya girgiza mata, alamar bai saniba. Rahma tace“Pls Nawan kaci wani abu, ya kake jin jikin naka?” Abbaye ya ware mata manyan fitinannun idanunsa, ya ɗan yamutsa fuska, yace“My dear ko sallah ban ba fa.” daga nan yaja bakinsa ya kulle, ya kalli ɓangaran Ruwaida yaga kanta sadde ƙasa tana wasa da,zara-zaran yatsun hannunta, idanunsa ya lumshe yana ɗan feso da iskar bakinsa waje.
Asma'u tace“Acp zamu koma Allah ya ƙara lafiya.” Acp ya buɗe idanunsa ya amsa“Amin Ngd anty, Zainab zaku wuce?” Dr Junaid ne ya buɗe ƙofar ya shigo, da sallama Dsp da Nadeer suna biye da Dr, wanda Dcp suna shigowa Nadeer na fitowa daga masallacin hospital ɗin, suka gaisa suka shigo tare. Rahma ta miƙe tace“Allah ƙarama lfy pls kaci abinda na kawoma zaka ji daɗi kaji nawan.” Abbaye ya ɗaga mata alamar “To” murmushi tayi nan suka gaisa da Nadeer ta masu sallama suka tafi, bayan tama Ruwaida sallama. Dr ya duba Acp yace“Acp yana da kyau kaci wani abun sai kasha magani.”Abbaye yace“Ok inaso nayi sallah.”Dr ya temaka masa ya sauko, Nadeer na riƙe da hannunsa suka nufi toilet. Ruwaida ta bisu da kallo tana matsar ƙwallar tausayin Acp.
Dsp yace“Ƙanwar Acp se ke ɗaya? Ta so mana zo kusan yayan naki.”Ruwaida ta sadda kanta taƙi ko kallonsu, miskilancin ya motsa mata.
Bayan Abbaye yayi fitsari yayi alwalla Nadeer ya kamashi suka fito, ya shimfiɗa masa darduma ya tsadaddan agogon hannunsa da Nadeer ya ɗaura masa, tin bayan da ya gama alwalla ya kalla yaga ƙarfe 8 saura minti 9. Idanu ya waro yana faɗin “Ya Salam haka na jima, banyi ko la'asar ba fa...” ya ƙarasa mgnr yana tayar da kabbara sallar isha. Dr Junaid yace“Acp kayi sallar a zaune bazaka iya ba fa a tsaye, harbi a ƙafaɗa ramuwar salla uku fa zakayi.... Abbaye dai sallar ya tayar, haka cikin dauriya da jarumta da nuna shiɗin namijine. Haka yayi sallar amman ya taɓa yaji, sbd yaji muguwar wahala, kafin yake gamata, amman haka kaf saida sallaci sallolin da suka fice shi, yayi isha ya rama magarib ya rama la'asar, har wata zufa yake ta azaba. Nadeer da Dsp da Dr ba ƙaramin mugun ganin ƙoƙarinsa suka yi ba. Bayan ya gama yayi Addu'a ya miƙe Dr ya kama hannunsa suka nufi saman gadon. Ruwaida da idanun take binsa, wani irin taisayin sa take ji, sai matsar ƙwalla take. Jama'a kuwa ƴan dubiya Caaaaaa suna waje, ba'a barsu suka shigo ba, waau.sai ta window suke leƙensa suna masa Addu'a. Bayan Acp ya zauna Dr ya kalli Ruwaida yace“Ƙanwar Acp zo ki zuba masa abunci mana.” Ruwaida ta ɗago ta kalli Dr ta mayar da kanta ƙasa. Nadeer yay dariya yace“Bari muga me uwar gidan naka ta kawo maka waccaan ƙanwar taka sarauta take ji bta niyar ciyar dakai...”Ya faɗa yana sunkuyawa ya ɗauko kular da Rahma ta kawo. Dr murmushi yayi ya ɗauko ledar magamin zai gwadama Abbaye. Nadeer ya buɗe kular dambun kifin da ƙwai, ƙamshi ya baibaye wajan, Dr yace“Yauwa bashi yaci, sai yasha maganin bari na nuna maka yanda zai sha.” Safuwan Miƙewa yay ya nufi wajan Ruwaida, Dr da Nadeer suka bishi da kallo. Cikin jarumta yake takawa tamkar ba mai jinya ba. Ruwaida jin takun mitum yasa ta ɗago dakanta da sauri, idanunsu ya shige cikin na juna, haka atare suka ji wani abu ƙamar mashi ya suke su a ƙahon zuciya, haka zalika wani irin abu Ruwaida ta fara ji marar musaltuwa.
Da sauri ta kauda kanta tana cin maganai. Acp lips ɗinsa na ƙasa ya ciza yana kallonta har ya iso dab da ita, ɗan ranƙwafowa yay dab da ita, har suna jin ɗumin hucin junansu. Bai mata magana ba ya sanya tattausan hannunsa ya kama lallausan hannunta, ta zabura ta ɗago da kanta, wani mugun kallo ya watsa mata, wanda saida ƴan hanjin cikinta suka juya, kanta ta sadda ƙasa tana runtse lumsassun manyan idanunta haɗi da turo ƙananun laɓɓanta gaba, tana son ƙwace hannunta. Baki ya ɗalle mata da ƴar yatsarsa, can ƙasan maƙoshi cikin tattausan murya yace“Ban son raini fushin me kike dani...?” ya faɗa yana murza mata laɓɓanta. Ruwaida taji zafi amman ta basar dashi taki ko motsi bare ta nuna masa taji zafin, idanunta alumshe ƙamshin turaren jikinsa ya addabeta, tamkar yanzu ne ya fesa turaren ajikinsa....
Nadeer da Dr baki suka iriƙe suna kallon ikon Allah! Acp Miƙar da ita tsaye yay, Yana riƙe da hannunta, ƙin buɗe idanunta tayi, Abbaye yace“Buɗe idanunki muje ki ban abinci.” banza ta masa taƙi buɗe idanun nata. Janyota yayi idanun nata arufe ya nufo kan gadon tana tirjewa..!! '''(💃🏻Yasin inada wasu Aƙasa😂 idan naga ruwan comments zaku jini Akoda yaushe, idan banganiba kunwa kanku Dan Ba Ruwana Yasin🙄🙄🙄)'''
_*Real L Rahma Momy'n Fareesatu ce💋*_
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.