Chapter 31

444 21 7
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

'''🕌Juma'at Mubarak🕌'''

_*ASTAGFIRULLAH WA'ATUBU ILAIHI.  YA ALLAH KA YAFE MANA ZUNUBAN MU DAN HASKEN ANNABI DA ALQURA'ANI DA KUMA WANNAN RANA TA JUMA'AH MAI ALBARKA.🤲🏻🤲🏻🤲🏻*_

_Kyautar Page gareki Tare Da Jinji  Da Nuna_ _Godiyarmu *👉🏼Miss Flowar💐*_
_Haƙiƙa Munji Daɗin Yabinmu Gareki_ _Ni Babu Abinda zance miki_ Saidai Na Biki Da Addu'a Allah Ya Kareki _Da_ _Kariyasa Ya Ya Rabaki Da sharrin_ _Masheranta, Allah Ya Rabaki Da Mugunji Mugun Gani, Kwanciyar Hankali Nasara Sa'a Ɗaukaka Arziki Me Anfani lfy Duk Su Kasance Atare Dake, Zanyi Ta Binki Da Kyautar_ _Zafafan flowers.🌷🌷🌷_

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 31*

Dr ya girgiza kansa yace“Tabbas na yarda da aljannu na iya yin kome, amman abin akwai ban mamaki da rikitarwa, ɗazu cikin ya nuna min sati 5 yanzu ya nuna min sati 7,
cikinta keda shi fa...” Safwan ya katseshi“ Dr karka damu insha Allahu da ƙarfin Addu'a sai sun barta, ba ciki bane.” ya faɗa yana sanya hannunsa ya kamo hannun Ruwaida ya miƙar da ita tsaye.  Manyan fararan idanunta ta ƙura masa, alamar tambaya. Yace“Karki fa damu ƙanwata.” yana faɗin hakan yaja hannunta suka iso wajansu Abbah.  Musaddiq yace“Ya Allah ka tarwatsa wannan shaiɗanun...”Hamza yace“Ameen insha Allah bazasu kai lbr ba, wato sun mata ajiya sun gudu ko?  Malam ya miƙe tsaya yana faɗin“Dr gwajin farko sati 5 yanzu kuma sati bakwai?” Dr yace“Eh malam.
                                   Acp yace“Malam gata kaji sun ƙara mata kwanakin cikin sun gudu...”Ruwaida ta fizge hannunta ta ɗora akai tana zaro idanu ta rushe da kuka.  Abbaye ya riƙota yana faɗin“Yi hƙr bari kuka, bakida kome fa to meye na kukan yi shiru, insha Allah kome zaiyi daidai.” ya faɗa yana  rungumeta.  Shasheƙar kuka
take sosai bata daina ba, tayi lamo aƙirjinsa, yana bubbuga bayanta, yace“Ya isa mana yi shiru kinji ƙanwata.” kai ta ɗaga masa alamar
                      “Toh”   jin tayi shirun tana maida numfashi, ganin tayi shiru yasa Acp ya janyeta daga jikinsa yana goge mata hawayen fuskarta da tafin hannunsa. Wani irin daddaɗan ƙamshine Ruwaida take shaƙa, daga hannun Acp, wanda ya narkar mata da zuciya taji bata buƙatar kome kamar tajita jikin Acp tana shaƙar ni'imataccan ƙamshinsa.  Ido ya kashe mata ganin tana kallonsa tana murmushi hawayen na kwaranyo mata kan fuskarta.  Musaddiq tausayi suka bashi su duka, sai yake ganin kamar suna ma son junansu suke.
Kallonsu kawai su Abbah suke, har lkcn da ya goge mata hawayen yaja dogon hancinta ya ɗalle mata jajayen laɓɓanta, ta ɗanyi murmushi ta sadda kanta.
                    Malam yace“Ina zuwa Tasi'u mu fara  Addu'a.” Tasi'u ya miƙe suka fara zagaya ɗakin, kowace kusurwar bango saida suka tofama addu'a, har ƙasan gado saida Tasi'u ya shiga.
                       Qura'an mai girma malam ya buɗe, yana zaune Ruwaida na gabansa a zaune, Acp na gefenta.  Yace“babu alamunsu A hospital ɗinan sun gudu, amman zamu haɗe insha Allah.. Ɗiyata ke ƴar inace? Sannan can da farko kina mgn?” Ruwaida ta yarfa hannunta alamar bata saniba.
                Abbaye ya ciro wayarsa ya rubuta mata tambayar da malam yay mata ya ɗora da cewa _“Please my ƙanwata ki ɗan faɗi wani abun wanda kike riƙe dashi, kinji._ Ya bata wayar ta amsa ta duba ta rubuta _“Yayana me kirki wlh ni na manta na taɓa mgn ko ban taɓa ba, ni yanxu bansan ƴar inace ba, uncle kawai na riƙe akaina, yana sona sosai, amman inaji ajikina zan tuna kome nan kusa, kaji yayana ina so muna hira baki da baki dakai.😿_
                             Yana dubawa ya ƙura mata ido tausayinta yakeji fiyeda kome a duniya, gira ya ɗaga mata, ya kashe mata ido.  Bayanin abinda ta rubuta yama malam.  Malam yace “Karku ƙosa ko kuyi gaggawa insha Allah sannu a hankali kome zaiyi daidai.. Bani ruwa a ɗan cup.” Kafin Acp ya miƙe Musaddiq har ya isa wajan fridge ɗin ya ɗauko ruwan ya tsiyaya A cup ya beƙama malam.   Abbah da Hamza ƴan kallo suka koma.
                     Yasin da Amanar rasulu da Ayatul kursiyyu, ya karance mata aruwan ya beƙama Safwan yace“Ta shanye yanzu.   Safwan ya beƙa mata ya tsareta da fitinannun idanunsa. Bakinta ta kafa cup ɗin tare da bismillah, har ta shanye Abbaye ya amshi cup ɗin ya ajiye.
                                 Malam ya fara ma Ruwaida karatu babu ƙaƙƙautawa, kowa ya nutsu sun zuba masa idanu yanda ya keba kowane harabi  haƙƙinsa.  Tsawon 1 hour yayi yana mata karatu duk wata aya me zafi wacce akema mutum rukiyya dashi sai da ya zaƙulosu yana karanta mata, amman babu alamun aljannu zasu tashi jikinta.  Malam yace“Wallahi sai an dage fa, dan mugayen matsafane ke turo mata mugayan aljannu, yanzu ko kafin muzo sun gudu, amman da izinin Allah sai mun wargaza tawagarsu, da ƙarfin Qura'an akwai addu'ar da zan mata kan wannan ajiyar da suka mata, insha Allahu ajiyar zata tarwatse, sai fa an hana ido bacci an dage da ibada da karatun Qura'an sbd  sam basason karatun, hakan zai temaka wajan tarwatsasu.. Sanna arinƙa kaita can gidana safe da yamma ina mata karatu tana shan ruwan addu'a wanda muke zuba garin habbatul'sauda da  garin zaitun, kuma nan wajanku kunayi wallahi nan kusa, zakusha mamaki, indai rashin mgnrta na sihiri ne shima sai ya wargaje, ta buɗe bakinta  bi'izinillah.”☝🏼
                              Abbah sosai sukaji daɗin godiya suka ma malam ɗan asabe. Abbaye kamar zai goya malam jin Ruwaida zata warke sannan tayi mgn.  Ita kanta Ruwaida daɗi takeji tanaso taji ta buɗe bakinta tayi mgn.   Abbaye ya tafi mayar da malam ɗan asabe gida.  Yayin da Dr yaba Ruwaida sallama, Musaddiq ya kwashesu amota sai gida, Abbah ya ƙira Acp akan ya wuce wajan aikinsa su sun tafi gida.       
                    ( *Niger*)
Cikin ƴan mintina sai gasu A niger cikin ƙasurgumin jeji.   (Sinaye)  tana tsaye cikin shigar tsafi, da jajayen kaya, saman wani ƙaton tsauni kai kayi mamakin yanda mutum zai hau wajan, ɗauke yake da zanen ƙaton gumki, wanda ya kasance bashida kyawun gani.. Wani irin sambatu take tana zaro idanunta, ƙwala-ƙwala, jikinta na kyarrrma.
        Gabanta suka diro, saida tsaunin ya girgiza, ita kanta ta fara sarewa lamarin, cikin jarumta ganin karsuce ta kasa ta juyo cikin wata irin murya tamkar ba mutum ba, tace“Garin yaya kukayi irin wannan saken? Ina kukeso mu dafa yanzu? Ga Ƙundariiiiii Ƙundaaaaa ba lfy, na rantse da Jodaaaaaah da Gumazuniiiiii sai munga bayansu...”  ta faɗa jikinta na kyarrrma, cikin ihuuuu saida jejin ya amsa baki ɗaya.     Da ƙarfi suka fara mgn cikin muryasu marar daɗin sauraro  suna mgn wuta na fita abakunan su.
                           “Mun Rantse da Gumazuniiiiii sai mun ƙarar da dinginsa mun kasheta yanzu kasheta zamuyi, na rantse da Jodaaaaah ni Nazizilu sai na ɗauki fansa mafi muni akan yaron nan, koda ni zan rasa raina sai na kashe Ruwaida ayanzu rantane banaso, adoron duniya, zan kasheta sai muga ƙarshan son da sarki yake mata da kuma wannan la'ananen yaron zai bitane, ayanzu na shiryama abin zan shigeta na azabtar da ita, sunacan suna shirya mana gadar zare, na ƙarar da danginmu...”Sinaye ta kece da dariya tace“Kaf abinda suke ina kallonsu, ina ganin shirinsu, yanzu kasan me? Tinda har ta sami wannan kuma inaga alamar sonta yake, so me zai hana mu barta haka muyi ma abinda zai saka ya aureta, kaga da zaran ya aureta shirinmu yayi, burina ya cika, ba ita ba auran da zai wargazamin zuri'a da tonon asirin da duniya sai tayi Allah wadare dani, idan aka san me na aikata, kuma ai kunga auren da zamu haɗa na haram wanda muka joye hankalin jama'a akansa shima ya ƙare, saidai wannan sheɗanin tsohon nafi son ya mutu ayanzu fiye da kowa...” ta faɗa cikin ɗaga murya, saida tsuntsayen wajan suka tashi.  Nazizulu yace“Ƙarya kike tinda kika fara sai mun ƙare kina nufin mubar yarinyar da ta nakasa mana uwaye da kakanni akan burinki? Kawai kasheta zamuyi, yanzu kika gama faɗin sai kinga bayansu fa...” Sinaye ta bushe da dariya tace“Zanfi nutsuwa Ruwaida da tsoho idan suka mutu, aci gaba da gashi.   Ihuuuu sukayi suna wani urin surkullansu, suka zama guguwa suka ɓace ɓat, Sinaye ma ta ƙarasa tsafinta akan tsaunin ta ɗauki ƙoƙan tsafin nan ta sake rikiɗawa sai gata ta ɓace ɓat.
                          Mai marta sarki ya dage da addu'a akan Allah ya baiya masa Ruwaida, yayin da suma matan nasa suna iya daidai gwargwadon su.  Ɓangaran Mabaruka kuwa ta sakama wannan ƙofa idanu ta gidan sarki addu'a take Allah ya bata izinin shiga, so take taga meye acikine, har yarima Yazeed taima hira a waya, dan ya bata haske kaɗan ya gwasaleta bata sake ƙiransa ba.
                      (Nigeria)
Ruwaida suna zuwa gida wanka tayi ta saka riga da zani na atamfa ta saka hijabi, ta fito falo kafin ayi magarib.  Nan suka baje Abbah naba Mummy lbrn abinda ke faruwa.  Mummy wani irin daɗi taji cewar ba ciki bane Ruwaida gareta, daman ita sam batason ɗaurewa yaronta ginɗi ne.. Gashi kuma Ruwaida batada wani abokin hira sai shi.   Rungume take da Ruwaida bakinta yaƙi rufuwa dan murna, tana shafa bayan Ruwaida, tace“Dota ki dage da addu'a muma munayi, insha Allahu babu abinda zai sameki aniyarsu zata koma masu kinji.”Ruwaida kuwa da son jiki kamar mage ta ƙara lafewa jikin Mummy ta ɗaga kai alamar
                       “Toh”
Abbah yace“Wai ina yaran ne?”Mummy tace“Ai fa suna zuwa suka cire uniform suna gidansu Aneesa kallon kaya, har Fu'ad.”  Hamza yayi dariya ya miƙe yana faɗin“Bari naje nayi alwala lkcn magarib yayi.” Abbah ma ya miƙe yana faɗin“Allah dai ya sanya alkhairi.” suka amsa da “Ameen.
               Ruwaida ta janye jikinta tana murmushi tama Mummy nuni da hannunta zataje gidansu Aneesa wajansu islam.    Mummy tace“Wajan ƴan uwanki kike son zuwa su Widad ko..?”  da sauri ta ɗaga kanta.  Musaddiq ya miƙe yace“Aa Mummy malam yace karfa abarta ko farfajiyar gida ta dinga zuwa ita ɗaya.”Mummy tace“Ok shikenan ɗiyar kirki yi haƙuri zo muje muyi alwala.” ta faɗa tana kama hannunta.   Ruwaida ta shagwaɓe fuska tana diddira ƙafafunta, alamun sai taje.
           Dariya Musaddiq yayi ya fice.  Mummy ta kama hannunta suka nufi bedroom ɗinta tana faɗin“Ƙyale yayanki sai kin faɗawa Abbaye'nki.   Wani sanyi Ruwaida taji jin an ƙira Ya Safwan ɗinta.
                           Ɓangaran Acp kuwa yana maida malam gida, ya wuce wajan aiki kamar yanda mahaifinsa ya umarce sa.. Yana zuwa ya shiga dube-duben tilin files ɗin dake gabansa, ƙiran magarib ne ya dakatar dashi, yaje yayi sallah, ya dawo yaci gaba da aikinsa, bayan yayi sallar isha yayi shirin tafiya gida.  Yanzu ma shi ɗaya yake driving ɗinsa cikin nutsuwa, yana so ya isa gida yaga lfyr Ruwaida duk Musaddiq yace masa ras take yanzu suka gama lunch suna falo zaune ita dasu Widad wajan Mummy.   Ɗan gunti smile ya saki yana shafa sajan fuskarshi, wayarsa ya ɗauka ya ƙira Rahma.  Bugu ɗaya biyu shiru bata ɗaga ba, har ƙiran ya gama ringing ɗinsa ya katse, saida ya mata misscalls 3 bata ɗagaba. 
                 Acp ya ajiye wayar yana dirving da hannunsa ɗaya ɗayan ya tura cikin sumar kansa yana shafawa.  Zazzafar iska ya fesar daga bakinsa, can ƙasan maƙoshi ya furta“Rahma!! Fushin me kuma?”  ya ƙarashe mgnr yana ɗaukar hanyar gidansu Rahma ɗin.
                      Can gidansu Rahma kuwa bayan kowa ya watse sai ita da ƴaƴanta, dan ƙwayen Rahma ma sun tafi, ta dawo gida inna ta tisa kaya gaba sai albarka take sawa.  Ahaka malam ya iskota da ya shigo alwala, bai kulata ba yayi alwalasa ya fice,bai dawo ba sai saida akayi sallar isha.  Zinaru ganin baice kome ba yayi zaman saman tabarma yanajan casbaha, inna ta miƙe tana gyara ɗaurin zanenta, ta isa wajansa tace“Malam wai meyasa kake haka ne sbd Allah? Malam Ɗahiru yace“Ikon Allah Zinaru! Me nayi? Dan Allah ki zauna muyi mgn.” Zama tayi kusa dashi tace“Ga kaya can baka saka albarka ba, abinda ya kamata ace ka tattaro malamai ƴan uwanka sunzo sunga abin arziki sunsa albarka, amman sai ka wani share abun, kamar baka farin ciki.” Murmushi yayi yace“Zinaru nayi murna mana ai idan kina irin wannan halin bana son biye maki sbd abin naki ƙara hauhawa yake...”  Ni ɗin malam? To naji Allah baɗa haƙuri ɗiyanka ne kayi yanda kaga dama dasu...” Rahma da take gefe haushin Acp ya cikata yace zai ƙira tin kafin la'asar har dare ba ƙira. Tace da inna“Haba innata kina hƙr dan Allah Babanmu fa har addu'a ya tara jama'a akayi fa...”Katseta tayi ta hanyar cewa“Ke!! Rahma!! wlh zan ɓata miki rai sannu uwar iyayi.”  ta faɗa tana shirin miƙewa daman ba wuta nefa basu dawo da ita ba, malam ya riƙo hannun inna yace“Ki dinga abu anutse zaki so ƴaƴanki surinƙa abinda kike agidajansu? Yanzu dai kawomin abinci naci sai nazo na sakawa kayan albarka.
                  Inna ta ƙwace hannunta ta miƙe.  Zainabu tace“Innata! Innata! Allah ya barma ke.” Rahma tace“Amin.   Inna tace“Ai kuwa bazai barni ba.”  Malam dariya yayi.
Bayan ta kai masa abincin nasa ta zuba ita da yaranta sunaci.  Alkcn ne Safuwan yake ƙiran Rahma wayar a silent take amman ta gani sarai taƙi ɗauka.  Suna gama lunch bayan ta wanko hannunta, malam ya gama ya sama kayan albarka atare suka jide kayan aka saka aɗakin malam, malam na mamakin wannan yaro ya kashe kuɗi sosai.  Acp na zauwa ƙofar gidansu Rahma yay parking ya fito ya rufe motar ya nufi cikin gidan.  Asoron ƙofa ya tsaya yayi sallama.  Malam ya gane muryar ya amsa yana faɗin“Ah Safwan! Bismillah shigo mana.” Ƙarasowa yayi ya rusuna ya gaishe da malam da inna.  Inna ta amsa cikin sakin fuska tana faɗin“Ya aikin? Acp yace“Umma Alhmdllh.”  Zainab tace“Ya Acp ina yini ya aiki? Abbaye ya amsa. Ya miƙe yana faɗin“Baba Allah ya hutar da gajiya, Zainab sai da safe ko?” Malam yace“Zainabu ina Rahma ba yanzu naganta ba?” Zainab tace“Eh ta shiga tayi sallah.
Baba yace
               “Toh.”
Abbaye fitacewa yayi yaje mota yana jiranta.  Rahma kuwa jin sallamar Abbayen yasa ta shige ɗaki.  Inna tace“Kaiko malam baka rabo da abu wlh, meye na cewa yanzu ka ganta salon yace dan taji yazo ta shiga ta kintsa, wlh ba'a haka malam.”  malam banza ya mata ya shiga ƙiran “Rahma! Karfa na iskoki ɗakin nan banso shagantaka fa.”  Rahma fitowa tayi sanye da hijab tana baza ƙamshi tace“Babana yi hƙr sallah nayi.” Ta faɗa tana istigifari tinda ko sallar batayi.
       Malam yace“To maza jeki ku gaisa ki kula da kanki Rahma.”Rahma tayi murmushi tace“Toh Babana ngd.”  Inna bata samasu baki ba ta miƙe domin tayi sallar isha. Zainab da babanta suna hirasu.  Rahma fuskarta bazaka ganeba tana jin haushin Acp fuskarta wasai, wayama ta ɗaga tana mgn da Samira tana sakin murmushi haka ta nufi motar, tana takunta me cike da nagarta.
                       Acp ya hasketa da fitilar mota da gangan ganin yanda take wata irin tafi mai cike da kamala, kashe fitilar motar yayi yana jinjina kansa ganin mutanansa sai kaɗawa suke ahijabi. Fitinannun kyawawan idanunsa ya ƙuramata, ta ɗan hasken da yake ganinta yana shafa kwantaccan sajan fuskarshi, can ƙasan maƙoshi ya furta“Uhmm dear Rahma manya ko fushin me ake min? Tazo naji...” Ya ƙarashe mgnr yana sauke numfashi...

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now