Chapter 7

425 20 0
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Sadakarwar*  ~Gareka Babban Yayanmu Muhammad AbdulNasir, Allah Yayima Rayuwarka Albarka Tare Da Iyallanka, Baki Ɗaya Nagode Nagode Ɗan Uwa Nagari💗💗💗~

~DEDICATED TO~ '''Aunty Nusaiba Allah ya saukeki lafiya Ameen.🤲🏻'''

*Tukuici Gareki My Sa'adatu ishaq, ƴar mutun Jigawa, Alherin Allah ya kai maki, Ngd da alherinki gareni.🤝🏻😍*


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 7*

Saida ya shiga mazaunin direba ya zauna, kafin ya bude mata front seat ɗin ta zauna, tana kallonsa murmushi ɗauke kan fuskarta tace.
                        "My Acp nawan!" Abbaye ya ɗan waigo ya kalleta ya ɗaga mata gira ya tambayeta  ya dai?" da idanunsa.
          Wani irin shauƙi ta shiga tai saurin kauda kanta tana murmushi.       Abbaye a hankali cikin cool voice nasa yace.
                       "My Rahma!" ya ƙirata yana ɗan rankwafowa dab da ita, yana hura mata iskar bakinsa dab da wuyanta zuwa fuskarta, ya ɗan beƙa hannunsa ya shafi fatar wuyanta, cikin wani irin salo ya kuma cewa.    My dear!"       Fitinanniyar muryashi da ƙamshinsa suka ɗimautata lokaci ɗaya, ta rinƙajin wani iri ta kasa amsawa, ta rumtse idanunta da karfi ta ƙame jikinta gam, zuciyarta na bugawa, taja mayafinta ya rufe mata jikinta.       Zaman sa ya gyara ya saki  ɗan guntun smile iya  laɓɓansa,  wanda yake masifar ƙara masa kyau.    Lips ɗinsa ya ɗan ciza a hankali yace"Dear raguwa, ki shirya fa." Rahma cike da shagwaɓa  ta ɗago, takai kallonta gefensa taga ya koma wajan zamansa yana kallon gefe, murmushi tayi a kasalance tace.
                      "To Nawan ba kai bane ba..." Juyowa yay ya ɗan harareta kaɗan yana ciza lips ɗinsa, ya kauda kansa, yace"My dear auran mu bazai jima ba insha Allah." Rahma cikin murna  tace" Sbd ina buƙatarki a kusa dani my dear, kuma daman Brother nake jira yazo, Abbah yace ya fito da mata, ko ba haka bane my Acp nawan Abokin rayuwata?"  Kai ya jinjina mata, alamar "Eh hakane dear."  Bata san lokacin da ta rankwafo ta bashi sumba ba a kumatunsa, tace"  Allah nuna mana, my Acp nawan ni kadai." kai ya jinjina, ya amsa da" Ameen" can ƙasan maƙoshi. To Haka suka taɓa hira duk itace ke surutunta, ko ta ƙarasa amsa hira, shiyasa yake son Raham saboda ba girman kai ga irin son da take masa domin Allah ba dan kuɗi ba, shiyasa take babban matsayi a zuciyarsa, ita da mahaifinta.   30 minutes yay mata ya sallameta ta shiga gida, cikin farin ciki suka rabu da juna  shi kuma ya nufi gidansu Nadeer, saboda ya ƙirasa da yamma bashida lafiya. 
Ɓangaran giɗaɗo kuwa bayan ya rarrafo yazo kofar falon ya samu ya fito, yayi² ya miƙe ya kasa, sai ƙiranta yake" Kurma! wlh kika tafi ranar da muka haɗu a waje zakici ubanki!" ya faɗi yana cizon baki sabida yanda, ƴaƴan marenansa suke masa zugi, ya kasa tashi, haka ya dinga rarrafe har ya fito yaga gate a buɗe, kukan baƙin ciki ya saki ganin ta gudu ya koma da rarrafen ciki ya ƙira direban gidansu, yazo ya kamashi da kyat ya miƙe suka nufi mota yana tambayarsa meye? yace" na manta na cika bath da ruwan zafi na shiga ciki na zauna." direba tausayi ya bashi ya sakashi mota, suka nufi hospital. A can kuwa Dr yace karya yake ba ruwan zafi bane matsesu ne akayi, bai musaba yace wai faɗa sukayi da wani ɗan daudu, nan likitan yayi masa allura ya bashi maguguna.  Yana zuwa gidansu ɓangaransa ya shige bai yarda kowa ya gansa ba, ya ƙira ɗan gambo ya bashi aikin nemo Ruwaida akan nera dubu dari biyu. Ɗan gambo yace" inda tana garin Taraba sai na samota, ko tare da uban wa take mune Jalingo."

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now