Chapter 4

442 20 1
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 4*

*Asalin su Acp Abbaye*

Ishaq Safuwan Al'ameen Sawaba, shine cikakken sunan mahaifinsu Abbaye, a salinsu ƴan ƙasar mali ne, wato fulanin mali ne Allah yay masu kyau na asalin fulani, gasu farare tass.
Kakansu ishaq Al'ameen shine ya fito yawan nema har Allah ya kawoshi niger, cikin garin ƙonni, wacce take cikin jahar Tahoua,  shida matarsa, Aminata, anan suke da zama,  ya shiga aikin siyar da shadda kala² irin tasu ta mali   har Allah yay ma abin albarka, baya cika wata se yaje ya ɗauko  wasu masu nagarta yana badawa sari, basu rufa shekara biyu ba.....Aminata ta haifi ɗanta ɗaya ƙwal, wato Safuwan, kyakywan gaske fari tass ya sami tarbiyya sosai iyayansa suke basa kulawa sun sakashi makarantar boko da islama, har zuwa girmansa, inda ya karanci fannin business, yana harakar kasuwanci kome idan ya samu wanda zai kawo masa ƙaruwa yi yake, har ya faɗa canji kuɗi wanda kafin me Allah ya ƙara arzirtasu, nan shima aka masa auran gida a Mali, da wata ƴar uwasa me suna Nadiya, kafin shekara biyu Allah ya albarkace su da ɗiya mace mai suna Ni'imah, tanada shekaru uku Nadiya ta haifi Ishaq jajir dashi mai masifar kyau da kwarjini kana kallonsa kasan bafulatani ne na asali, bayan shi sai Hamza daga kan Hamza Safuwan bai sake haihuwa ba, haka suka ba ƴaƴansu tarbiyya da karatu mai kyau ga gatan da suke samu wajan kakanunsu, ga arzikin Safuwan da na mahaifinsa yana bunƙasa ga ƴaƴan sa suna tasowa.
               Bayan su ishaq sun girma anyima Ni'imah aure ne, Allah yay ma Al'ameen rasuwa bai ko shekara uku ba Aminata tabi bayansa, sosai Safuwan yay marecin rashin iyayansa sai ƴaƴansa ne suka zama garkuwa agareshi, sai dangin su na Mali da suke zuwa ziyara, kamar bayan mutuwar iyayansa da shekaru biyar ne Allah ya ƙara yalwata arzikin Safuwan,  ga yawan shiga ƙasa shan waje da yake, shida Ishaq ya kowa masa tsantsar neman nakai duk ƙasar da zashi da ishaq yake zuwa, kuma ya ƙware a fannin ko wane irin business sbd karatun da yay kenan, anan ne suka saba da Alhaji, Jibril, ɗan Jalingo, saboda suna harakar business tare, Nan yay sha'awar komawa nigeria can Taraba ɗin tare da ƴaƴansa tunda sun kammala karatunsu......Ba'a ɗauki lokaci ba kuwa suka koma inda aka bar Ni'imah tana aure a Damagaram.  Tamfatsetsan gidane Safuwan ya siya,  Sosai sukejin daɗin zaman Jalingo yayin da suke tafiyar da kome cikin kwanciyar hankali, Alhaji Safuwan akwai temako kuma akowane kasuwancin sa baya riba baya cuta, ko canjinsa ya fita daban a garin Taraba, gashi baya yawan zama.   Amince ne me ƙarfi ke gudana tsakanin Alhaji Safuwan da Alhaji jibril, ta hakane har suka haɗa ƴaƴansu aure wato ishaq da Bahijja, yarinya ƴar shekaru 14 sbd Jibril cikakken bafulatani ne baya barin  yarinya budurwa ta wuce shekaru 15  gidansa yake aurar da ita....kasancewar, Bahijja da ta Ishaq, suna son juna tin haduwar farko agidansu abun yazo cikin sauƙi kowa murna yake, duk da tanada ƙaramcin shekaru.   Haka akayi bikinsu cikin farin ciki da walwala, soyayya mai tsafta suke gudanarwa, abin gwanin sha'awa,  kafin shekara ta zagayo Allah ya albarkace su da samun ƴa mace, santaleliya kyakywa fara tas lkcn shakarun Bahijja 15 cif a duniya murna ba'a faɗinta kyawun yarinyar ya zarce a faɗi, ta biyo iyayanta, dan Bahijja farace kyakywa son kowa ƙin wanda ya rasa bafulatanar asali gaba da baya, haka shima ishaq ɗin kyawunsa har yaso yafi Bahijjar, gasu farare tas.      
                  Sosai suke ba ƴarsu kulawa wacce ta zama ƴar dangi, watanta uku a duniya Bahijja ta samu ciki tayi kuka kamar me dakyat ishaq ya lallasheta, haka sukaci haba da renon ƴarsu da cikin su Taslim ta warware.   Wannan karon namiji ta haifa aka saka masa Musaddiq, wanda tare aka rinƙa basu nono da Taslim cikin ikon Allah babu abinda tayi saida ta isa yaye aka cireta.    Musaddiq yanada shekara biy da ƴan watanni aka haifi wani zankaɗeɗan yaron jajur mai kyawun gaske, duk kyan yayunsa ya kere su, haka iyayan nasa Allah ya dora masu son yaron fiye da kome, tun wajan zuwa barka zaka gane yaron yanada farin jini, haka kakanunsa ma kullum sai sunzo dubasa, ranar suna yaci sunan Safuwan wato kakansa, aikuwa gata ya ƙaru son duniya Alhaji Safwan ya ɗorama Abbaye, dan haka Ishaq da Bahijja suke gaya masa tun haihuwarsa bata sake samun ciki ba da wuri sai bayan shekaru goma cif, har sun cire rai aka sami cikin Islam, ko shekaru biyu bata cika ba a duniya Mummy ta haifi Widaad, yara kyawawa sunfi kama da Abbaye sosai shiko Musaddiq Taslim.  Safuwan mugun miskiline tin yana yaro baya walwala sosai amman akwai son ƴan uwa sosai yana kula da ƙanninsa sosai, amman mugun tsoransa suke matuƙa, jinin Abbaye da Taslim ya haɗu.
                      Haka ƴaƴan Safuwan suka taso cikin tarbiyya har girmansu, tin ƴan mata Mummy bata sake haihuwa ba seda su Islam sukayi shekaru islam nada 12 year Widaad nada 10 year cif tikun aka haifi Fu'ad, wanda har sun cire rai da haihuwar.
      Makarantu  masu tsada sukayi wanda faɗar kuɗinsu ɓata lkc ne,  sunyi karatun Addini mai zurfi Safuwan da Musaddiq rana ɗaya suka sauke alqura'ani mai girma,  Musaddiq yana da kyau sosai mutum ne me son jama'a gashi da walwala, bayada girman kai ko kaɗan, yayi karatunsa na sailor, wato matuƙin jirgin ruwa a Malaysia, inda ya gama cikin kwanciyar hanakali se da ya shekar acan yana bautar ƙasa kafin ya dawo ƙasarsa inda yake tafiya cotonou Ghana Lome congo kenya sudan  cameron da sauran ƙasashe, bashida wata budurwa, a yanzu tsayayya wacce ta kwanta masa, yarinya ɗaya ƴar cameron amman rashin tarbiyyarta, yasa ya watsar da ita, amman shi kansa yana buƙatar aure shekarunsa na haihuwa 30 year.
                                   Yanzu haka Bappa Safuwan da Ummani kakanin su Abbaye suna nan ras da ransu, part ɗinsu na ciki basa gari suna mali wajan rasuwar, yayar Bappa ɗin, Abbah na tare dasu, amman shi zai dawo cikin kwana biyu suko sai anyi arba'in sukace....masha Allah har yanzu da ƙwarinsu ras,  gidansu Abbaye irin gidanan ne kamar ƴar ƙaramar unguwa tamfatsetsan filine, Abbah ishaq da Bappa Safuwan su suka hana Abbaye da Musaddiq, fita gini wani waje, nan cikin gidan aka tamfatsa masu gini irin na zamani kowa ya zaɓi kalar da yakeso, idan kaga gidajan tamkar a saudiya, suma irin riƙakƙun gidajan nan fa, na manyan masu dashi....ajere suke su uku kowane da gate ɗinsa,gate ɗin kadai abin kallone dan ba sai megadi ya badeba, yana ɗan abin dannawarsa, yay sama da kansa.     Na farkone ƙaton yajeda masu gadi guda biyu.
                    Gate na farko su Abbah da Bappa se na Musaddiq sai na Abbaye, gidajan babu abinda babu, kowane da ƙaton Siwwing poll ga shuke shuke da lambu da manyan rumfunan ajiye motoci da ɓangaran masu aiki maza da kuma mata, ga rumfar shan iska mai ɗauke da kyawawan kujerun zama.    Amman har yanzu suna part ɗin iyayansu, sai sunyi aurene zasu dawo cikin gidajansu...
                            Masha Allah abin ba'a cewa kome, sai fatan Allah ya kawoma Musaddiq mata, a haɗa da Abbaye asha biki dan shi daman ake jira kawai.
*(Please inaso ku gane muƙamin da naba Safuwan na Acp shekarunsa basu kaiba sbd 28 year ne dashi shikuma Ac aƙalla zai kai shekaru 40 ko 38 so nasane kawai dan nishaɗi, da kuma ƙwarewarsa wajan aiki a lbrn ba wai dan azahiri zai kaiba, ehe)😉*.
                  
                    Kyawun  Abbaye kuwa tin pagen farko na faɗi irin kyawunsa. Kyansa
halittarsa, gashi ƙaton gaske, irin mai faɗin ƙirjin nan, ga mugun kwarjininsa wajan jama'a, gashi farine sosai har wani ja yake sawa, gashi kansa tamkar na indiyawa, saboda baya iskewa sosai haka zaka ga iska na kaɗashi gwanin sha'awa, haja jikinsa ko ina akwai yalwar gashi kirjinsa taf cike yake da gashi haka cinyarsa ƙwabrinsa, hannayensa, bayan hannunsa ma munas kwance yake da gashi gwanin kyau, abinda yake ƙara tafiya da imanin Rahma Dahiru kenan.....ga sajansa da guntun gemunsa, ga ƴar ƙasumba, kai gaskiya Acp Abbaye, na daban ne acikin maza. 
          A Germany yay karatunsa, wanda ya kwashe tsawon shekaru 6 ras, se idan yazo hutu, ko acan tin kafin ya daɗa girma yake fama da mata, amman shegen ko kallo har ya gama ya dawo bai taɓa koda aboki ba bare budurwa dan burinsa, zama babban police a ƙasarsa, yay aiki da gaskiya, koda zai rasa ransa, da Nadeer kawai yake abota tin secondary school seda yabar ƙasar suka rabu bayan ya dawo suka ɗinke, shi kadai ne abokinsa.
                       Bayan ya dawo ne ya fara aiki mai cike da ƙwarewa, da kuma gaskiya, wanda aka kaishi Minna, wata uku kacal ka ƙara masa girma, sbd ba ƙaramin ƙoƙari yake ba wajan kamo masu miyagun aiyuka, yana hana idanunsa bacci sosai gashi mutum mara tsoro ne shi akullum shirye yake ya bada ransa wa ƙasarsa, a haka haka ne cikin shekaru biyu kacal ya samu zama Acp sbd kakaf yanzu faɗin nigeria sunan Safuwan na yawo saboda mugun ƙoƙarinsa wajan dakatar da ɓarna, mai girma shugaban ƙasane da kansa yace a bashi Acp, ya kuma gaiyyacesa faɗarsa ta shugaban ƙasar, to fa (shiyasa Abbaye yakeda maƙiya sosai da sosai abokan aikinsa harda wanda suka kusa haihuwarsa, ganin ƙaramin yaro ya taka muƙamai da dama, wanda su basuda, dan wani ko DSP baida ko SP  ko  DPO, ko CSP bare yazo  APC, shiya duk suka tsaneshi, shiko ko ajikinsa, yo daman bai damu da sabgar kowaba, aikinsa ya saka gaba.)
                             wajan gari bakwai ya zauna kafin a kawoshi garinsu Jalingo, Safuwan  akwai tsafta, yanada kyankymi baya son ƙazamta ko kaɗan, gashi Allah yayishi mugun mabuƙacine yana da ƙarfin sha'awa sosai, ji yake ranar da ya samu matarsa kwana zaiyi bai koshiba, dan mugun mabuƙacine, yanzu haka mafi akasarin rayuwarsa kullum cikin azumi yake, asati wajan so hudu yake, dan ya rage ƙarfin sha'awa, baya rabo da shan lipton da lemon tsami ko kwayoyi, sbd yawan ciwon mara da yake, amman duk da wannan ƙarfin sha'awar tashi Allah ya tsareshi daga aikata zini, bai taɓa koda kama hannun wata mace ba da niyar jin daɗi ko wani abun, ɗuk kuwa da matan da suke kawo masa hari bila'adadin lalatattun da kimtsatsun, bai taɓa jin son wataba, sbd baici karo da mai irin abubuwan da yake muradi ba.....sbd shi yana mugun son manyan boobs yanajin babu abinda yakeso sama da nonuwan mace, yanaso yaji ya cika hannunsa yana wasa dasu yana tsotsa, to ji yake zai iya kwana ya wuni bai gajiba da tsotsa da kuma matsawa, se abu na biyu hips da bombom yana son wannan abun yay ta shafawa, dan gani yake halittarsa sai babban kaya, na uku kuwa gashin mace yana son yaga mace mai dogon gashin yay ta tura kansa ciki yana shaƙar ƙamshin ko bajeshi kan fuskarta yana wasa dashi......wannan shine burin Acp Abbaye, a jikin mace se kuwa Allah ya haɗashi da Rahma, amman yafita kyau nesa ba kusa ba, duk da  baiga gashinta ba amman yawan tulinsa yasan zaiyi wasa da gashi, shikam kaf cikin mata  halittar Rahma taimasa sosai, ga tsafta yanda yakesin mace ya samu, babu ruwansa da gidansu, sbd yaga sunaa wadatar zuci, gashi duk lkcn da zaije ko ina tsaf ashare, shiɓ yasan Rahma zata iya da jarabarsa, gashi yaga tana son jiki dan ma bai bata fuskar tana riƙe koda hannunsa ba, shima bai taɓa taɓata ba, dan gudun abin kunya, se dai ita, idan ya mata kwarjini takan ɗan kwantar da kanta a kafaɗara baya barin ko 1 munite tayi ajikinsa, zai ƙorata ya gudu dan kar yaje yay ɓarna.....amman yana sonta yana bata kulawa, sbd kamun kanta, dan duk inda zata shiga agarin Taraba, yanada masu bashi rahoto, ba'a taɓa kawo masa rahoton banza a kanta ba... Hamza yanada yara hudu maza biyu mata biyu, sun zama ƴan mata  Aneesa nada 19 year se  Nadiya me sunan Ummani, nada 17 year duk karatu suke suda su Widaad da islam, se Bahari da Jibril, ƴan kimanin 15 year, Abbah, Bappa ne ya roƙa ya saka sunan, Jibril amininsa, dan yanzu sun zama kamar ƴan uwa, kome tare ake, yi Hamza ƙanin Abbah gidansa na nan shima jikin nasu Abbah, tare da family ɗinsa gwanin sha'awa. 
                  Sai Yayarsu Ni'imatullah wacce take Niger damagaram Ƴaƴanta  6 maza uku mata 3 kaf sunyi sure sai auta Bahijja, me sunan Mummy ta saka saboda karamcinta, suna zumunci sosai dan ko Abbaye idan ya bushi iska yana zuwa damagaram wajan Ammie  haka suma suna zuwa, ɗaya  Mali take aure ɗayar cikin damagarm, ƴan mazan kuwa biyu Naimey suke aiki da matansu, ɗaya na tare da ita, a damagaram ɗin... 

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now