Chapter 29

352 17 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

_*SADAUKARWAR WANNAN   PAGEN   BAKI ƊAYANSA RANKATAKAF*_  _Gareku Ne, Mutanan Special Room Ummun Fareesa, Wollah Ina Jin Dadin Sharhinku Da Comments ɗinku Billahi bazan manta dakuba, Har Abadan_ *Musamman👉🏼 Mum Sayyeed&Noor💗*, _Auntyn Yara😘,_ '''Suwaiba😍, Fareeda💋, Nafeesat Mariga🥰, Fa'eezation💙, Omu Abdul🤍, Raheenat💖, Ƙawata Hadeeza❤️ me🤰🏻😅 Mom Asas🤎''' Da duk sauran afuwa wlh kunada yawa bazan iya lissafoku ba, amman insha Allah next page zan sako wasu, dan karkuga na waroku, I love u Tafka-Tafka.😻😻😻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 29*

“Kana isowa nan zan nuna maka kuranka Abba mune zaka tozarta, a idanun duniya? Kaci mana mutunci kaciwa kanka...?” Hamza ne ya katseshi ta hanyar cewa“Haba Yaya ishaq abi kome asannu zargi kawai muke ba tabbacin shine yayima yarinyar nan cikin nan, ka nutsu anutse mu binciki yaranmu na roƙeƙa, ni jikina na bani ba lallai shine ba, sanin halinsa tin yana ƙanƙane, ba wai kuma zan ɗaure masa gindi bane...” ya ƙarashe mgnr yana kama hannun Safuwan suka isa bakin gadon.   
                             Acp ya zama kamar wani butum butumi, zuciyarsa bugawa take sosai akan wannan lamari.  Abbaye ya zauna bakin gadon da Ruwaida take kwance, idanunsa ya ƙura mata, yana mi jin sam bai yarda da cikin nan ba fa.   Hamza yayi gyaran murya yace“Abbanmu! Dan Allah ka bamu hankalinka, muyi mgn ta fahimta, kaifa jami'ine babba wanda kakeda kima, a idanun jama'a, bayan haka kewaye kake da mahassada da maƙiya, masu son ganin bayanka, masu son ganin ka wulaƙanta!! Numfashi yaja yaci gaba dacewa“Don girman Allah wace alaƙa take tsakani ku da baiwar Allah'n nan, har tsautsayi ya gifta ka mata ciki, ko tausaya mata bakayi??”  Acp ya dafe kansa cike da ƙunar zuciya yana faɗin“Hasbinallahu wani'imal Wakil!!  Wlh na rantse da Allah Kawuna babu abinda ya taɓa haɗani da Ruwaida, itaɗin amanar Allah ce agareni, na ɗauketa tamkar Widad da islam  suko taya zan cutar dasu? Wlh zan iya alwala muje gida na rantse da AL'QURA'ANI, me girma ban aikatawa Ruwaida ɓarna ba...” Dogon numfashi yaja, kusan Abbah ya matso ya kama hannayensa yace“Abbana! Ka yarda dani wallahi azeem bansan komeba,  kuma ni sam banma yarda da cikin nan nata ba, saboda wannan tsinannun zasu iya ta ɓullo mata tabayan gida, zasuyi hakan domin nina ƙamaceta, kuma ku ƙyamaceta, mu korata sam ban yarda da cikin nan ba.. Dan Allah Abbah karkayi fushi dani, ka yarda da ɗanka, nasan me nake bazan aikata ɓarna ba, ga ƴar wasu sbd nima inada baya, kabani izini na nemo babban malami ayi mata ruƙiyya sai asake aunata muga ko akwai cikin, duk da nasan ba lallai su ciresa anan kusa ba.. Amman ai Allah yafi ƙarfinsu.”Acp ya faɗa yana rungume Abbah yana ƙara bashi haƙuri.   
                      Abbah yaja dogon numfashi yace“Na fahimceka Abbana amman taya zakace jinnu zasu iya mata ajiyar ciki, likita fa ya auna yaga kome, Abbana kaji tsoron Allah karka ɓatamana zuri'a karka bani kunya a idanun duniya...” Hamza ya katseshi ta hanyar cewa“Muyi na'am da mgnr sa kar mu musa masa, tabbas jinnu ba ta inda basa sharri dan haka bari da kaina zanje na kawo malamin har nan asibitin Malam ɗan asabe yayi nisa indai wajan ruƙiyya ne daga ƙasa² ake kawo mutane.”  Abbah yace “Ok ba damuwa na baku dama, amman wlh akasin hakan Abbana zaka fuskanci hukuncina.” Abbaye ya ƙara rungume mahaifinsa yana faɗin“Insha Allahu hakan zata kasance tinda nasan ban aikata ɓarna ba, haka zalika Ruwaida ba fita take ba, ciki sati 5 ai akwai ayar tambaya, ni ina tare da Allah ina tare da manzo Allah ba abinda zai sameni na sharrin mutum ko aljan, sbd na riƙe babban makami tarwatsa ko wani irin halitta, matuƙar ba na ƙwarai bane, Ruwaida nayi alƙawalin tarwatsa duk abinda zai cutar da ita kome ƙaramtarsa da izinin Allah sai na gano gaskiya ta hanyar alqira'ani mai girma...” ya faɗa yana sakin Abbah ya kama hannun Ruwaida ya damƙe cikin nashi, ya rankwafa dab da fuskarta, yana murza tafin hannunta ya shiga karanto mata addu'a, ya mata ƙurr da fitinannun idanunsa, mugun tausayin Ruwaida yaji ya mamaye masa zuciya,  yawo dukan jinin dake yawo ajikinsa, ji yake akan Ruwaida zai iya yin komai domin ceto rayuwarta, yana jinta fiyeda yanda yake jin islam da Widad, duk da ƙaunar yaya da ƙane sai Allah.. Amman zai sadaukar da kome nasa akanta.    Sosai yake tofeta da addu'a, yanayi yana murza tafin  hannunta, cike da tsantsar tausayinta.
                                Abbah da Hamza sosai zuciyarsu tayi rauni, kuma sun yarda da cewar eh tabbas ɗan nasu kaifi ɗayane, baya ɓoyewa sunsan yanda yake mata yanzu agabansu to ko bayan idanunsu hakan ce zata kasance, bazai mata wani mugun riƙoba.     Yajima yana mata addu'a kafin ya ɗago yana maida numfashi jin jiknta ya ɗauki zafi matuƙa kuma ko ina kyarrma yake, harda wani hayaƙi baƙi ke fita ta bakinta, da kuma hancinta,yayi murmushi yace“Abbah kunga soma taɓi ko? Wlh sharrin sune kuma da izinin Allah sai na karya duk ƙullun da suka ƙulla mata.” Ya faɗa yana ciro wayarsa cikin aljihu ya amshi wayar Abbah ya tura suratul  bakarah cikinta, ya kunna ya ajiye daidai saitin kunnenta saman fillow.  Acp yace“Abbah karku kashe, nabar ɗayar wayata can gida wannan kuma bazai yuba na barta anan shiyasa na kunna ataku.”   Abbah yace“Ok ai ba matsala, ina fa banga hayaƙin ba Abba....? Hamza yace “Kawai ya gani ɗin tinda ya faɗa ba lallai ba fa mu mugani.”  Abbaye yace kawu kawai katashi muje akawo malamin, Abbah ka kula da ita da izinin Allah basu isa su mata kome ba har mu dawo.” Abbah dai har yanzu baiji ya gamsu da ba ciki bane Ruwaida gareta, amman kuma ya yarda da ɗan nasa tabbas zaiyi wuya ya cutar da Ruwaida.   Dogon numfashi yaja yace“Ok Abbaye kuje ku dawo Allah ya mana magnin abinda yafi ƙarfin mu.”Cikin farin ciki Abbaye ya amsa da “Ameen yana sakin lallausan hannun Ruwaida da yake hannunsa suka masa sallama suka tafi.    Abbah yayi tagumi yana kallon Ruwaida bacci take amman sai zaɓura take ko karatun ne ke shigarta.
                          Can kuwa gidansu Abbaye'n bayan sunyi sallah, aka saka kaya acikin rantsatsiyar mota motoci biyu suka tafi da su, sbd ɗayan bata ɗauki mutanan ba.   Haka na Aneesa duk gidajan ajere mota akasa kayan aka shiga.  Mummy tinda ta idar da sallah take addu'a akan Allah ya fitar dasu daga wannan lamarin, maƙota daketa shigowane yasa dole ta fito parlon tana amsa Allah yasan Alheri da ake masu, amman damuwa fall aranta.  
                       Gidansu Rahma an gama shirya kayan baƙi, inna an sake wanka a saka lace mai kyau, an kashe ɗauri abin sai wanda ya gani.  Rahma Asma'u ta tashe daga baccin tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗɗan material maroon colour tayi masifar kyau ya kamata ya mata cif ɗinkin doguwar riga ne ta ɗora takalmi me tsini iya kyau Rahma tayi, saidai sam bata wata walwala, sbd abinda Acp ya mata, amman haka ta saki jikinta ta fesa turare ta ɗauki wayarta ta ƙira ƙawayenta Samira da Saudat tace su sameta agidan maman Sabreena, ta faɗama maman Sabreena ta kai masu kayan motsa bakin can.
                   Zaune yanzu ma suke an shimfiɗa manyan tabarmi gidan sai ƙamshin turaren wuta yake sbd yanda inna ke zuba turare cikin kasko duk bayan ƴan mintina.
                 Maƙota sun kusa cika gidan, yawansu kuwa duk ƴan gulma ne.  Inna ta waiga tana cema Asma'u“Asma'u wai ina Rahma ne ko baccin ne?”Asma'u tace“A'a itada ƙawayenta suna gidan mmn Sabreena fa.    Mmn Sabreena tace“Eh inna suna can suna shan kiɗa fa.” inna aka saki murmushi aka gyara ɗaurin ɗan kwali.
            Wasu mata 2 suka sunne kai suna dariya.     Inna tsaf ta gansu, dan tana lure da kowa, murmushi tayi tana miƙewa tana wata irin tafiya da gaiyya fa.🤣Asma'u zatayi mgn sukaji sallamar baƙi.  Amsa masu akayi aka miƙe ana masu sannu da zuwa.   Akwatina suka ga anata shigowa dasu kamar Allah ya aiko.  Guda goma sha biyu cif aka jeresu shaƙe da kaya.  Inna da ƴan uwanta sai hidima suke masu, bayan an gama gaisawa aka fara buɗewa.     Ai jama'ar wajan sun tsorata da kayan, Asma'u kanta ta tsorata da kayan bare inna wace ƙaton hancinta sai ƙara bajewa yake.  Taslim sosai suka kwashi gara girki yayi daɗi sosai hakan yasa inna taji daɗi da ƙara buɗe hanci.  Maman Sabreena vidoe tayi ma Rahma ta tafi ta kai mata.  Shatara ta arziki inna da ƴan uwanta suka masu Taslim sunji daɗin karamcinsu suka masu sallama suka tafi. Nan ƴan uwa da abokan arziki suka baibaye kayan Rahma ana faɗin anjima ba'aga irinsu ba, sosai matan unguwar da suka shigo suke mamakin wannan uban kaya haka, wasu sayan alheri wasu kuma hassada ta ɗarsu aransu sunajin daman sune ɗiyansu suka samu.  
                    Inna dakyat  A  daddafe aka watse sai na jikinta, da ƴan uwan malam wanda batajin nauyinsu, sun kuma san halin inna Zinaru hali ajikin rai.. Tako rinƙa kallon kaya sai washe baki take tana faɗin  “ Masha Allah Rahma kin amsa sunanki  Rahmar ɗiyar albarka, Allah ya kareki da dukan sharrin abin ƙi...”Asma'u tace “Kai inna ke kama kiyi shiru mana.”Inna ta riƙe haɓa tace“Toh uwata na ƙyale.” ta faɗa tana danna number malam Ɗahiru ta ƙirasa bugu ɗaya na biyu ya ɗaga da sallama yana faɗin“Zinaru! lfy dai ko? Ya hidima da baƙi?”   inna ta shige ɗaka tana dariya tace“Malam albishirinka goro fari ko ja? Ta tambayeshi tana dariya.   Malam ya riƙe baki yana mamakin wannan farin ciki na Zinaru.  Gyaran murya yayi yace“Fari tass me ya faru?” Inna tace“Rahmatu anyi goshi ƴar albark kaga kuwa uban lodin akwatin nan da aka kawo...”  Malam ya katseta yace“Dan Allah Zinaru ki daina wannan rawar ƙafar to meye na ƙirana ina cikin malamai ƴan uwan addu'a ma muƙe akan Allah ya dawwamar da ita gidanta, ya kuma sa ayi biki cikin sa'a...” cikin jin haushi tace“Haka fa akarmakallah naji sai anjima.” kitt ta yanke ƙiran tana faɗin“Humm mutum shi sai aƙida, nida nayi tunanin kazo mu ɗan taka rawa sai wnai neman kamin wa'azi sai kace na saɓi Allah, wlh shiyasa wasu matan basa son auran malamai.” ta faɗa tana fita ta isko su Asma'u suna rufe akwatinan, taja bakinta tayi gum, daman taga Lubabatu ƙanwar malam ta saka mata ido.
        Rahma da mmn Sabrena ta nuna mata video'n ganin uban kayan da Acp ya mata, saida tayi ƙwalla ko kusa bai nuna mata ko rabi ba.  Ƙawayanta sai rawarsu suke tana zaune tana rausaya kai, murmushi tayi tace “Samira bakida dama wlh, sai kace yaune auran.   Ta numfasa tace“Acp Nawan harda cewa zan ƙiraki anjima, ko jikin ƴar jaririyar ce yayi tsanani?” ta faɗa tana yamutsa fuska, ta ɗauki wayarta tayi dialing ɗin numbersa.    Acp Acan gidan malam ɗan asabe mai ruƙiyya,  Acp na masa bayanin abinda ya sami Ruwaida tin farkon haɗuwarsu zuwa yau da akace tanada ciki na sati 5 itako tafi wata 3 atare dasu, gashi iyayansa sunce shine yamata, sai bayan da suka fito daga sallar la'asar.   Malam yana gama jin bayanin yace“Tabbas akwai sharrin jinnu haɗi da mugun ƙulli, kuyi duba da rashin mgnrta, kuma kace sau ɗaya kaji muryata ta ƙiraka, to aranar da ta gamu damu da sai bakinta ya buɗe yar da izinin Allah, sai shaiɗanun nan sun barta..  Amman yanzu bazan yanke hukunciba sai munje.” Acp cikin murna yay masa godiya, malam ya ɗauki alqura'ani mai girma suka fito.
        sun fitone Acp ya buɗe masa gaban motar ya shiga ya zauna, Hamza da wani yaron malam ɗin guda suna a seat ɗin baya, Acp ya shiga mazaunin direba yama motar key, daidai lkcn ne Rahma ta ƙira, yana hawa saman tit yaga ƙiran nata.   Kansa ya dafe yana ɗan lumshe fitinannaun idanunsa ya ɗauki ƙiran, yay ƙasa da murya wajan faɗin“Ranki shi daɗe amaryata, pls ki ƙaramin hƙr zan ƙiraki da zaran na nutsu.” Rahma ta ɗanne ɓacin ranta tace“Ok My Qalbina fatan kana lfy?” Acp ya sake ƙasa da murya yace“Alhamdulillah zan ƙiraki ki kularmin da kanki bye.” ya tsinke ƙiran yana ajiye wayar ya maida hankalinsa kan dirving, ya ɗauki hanyar hospital.    Canma gidansu Aneesa an baje kolin kayan lefen da Musaddiq yama Aneesa abin gwanin burgewa.  Can kuwa asibiti Abbah ya ƙira Musaddiq yazo hospital suka zauna.  
         Bayan Acp ya kashe ƙiran  Rahma tayi murmushi ta miƙe tana shiga tsakiyar Samira da Saudat, tana ɗan duƙa ta riƙe guwowinta da hannunta tana rawar bom-bom ɗinta da albarkatun ƙirjinta na motsawa, sosai Rahma take son waƙar ta flavour me suna *Turn up* inda sukayi shi da jimmy jatt.  Sosai take masifar son waƙar ganin Acp nason waƙar yace zai koya  mata rawar ta rinƙa masa idan sunyi aure har yanda matan kema flavour.  Rahma ta koya a ɓoye so take sai bayan auran ta basa mamaki duk da tasan zataji kunyar saka kayan da taga ƴan matan sun saka.   Ai kuwa ƙawayensu wanda Samira ta gaiyato suka kwashe da shewa sbd yanda ta iya bin salon rawar dan sosai Rahma ta iya rawar. 
                                Sallamar wasu ƴan mata biyu ne ya katse  ma Rahma rawa, ta ɗago tana kallonsu irin na rashin sani.  Farar doguwa kyakyawa tace“Sister nasan baki sanni ba ko?

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now