Chapter 30

357 16 0
                                    

RUWAIDAH RahamaUmmuFareesa sur Wattpad https://www.wattpad.com/story/255574474?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=RahamaUmmuFareesa&wp_originator=SK1wG9yzwbPlqHQVWCYSMQN4wBgN%2F5ufrrJpQCfIy6m2nG0BFyVmRXirD0%2FdTm1AKg4zSUEXdSBTv49x3XNCo9LJmqJkFx%2FVLHb8lMAcjfajaBVaoTB2w5U%2B17jFUtqJ

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

Kyautar Page Gareku Kuma Ban Manta Daku Ba, Billahi Kuna Kasheni Da Zafafan Comments, Kunaba Sharhi Haƙƙinsa, Dan Haka Wannan Pagen Kyautace Sai Kunso Za'a Karanta.🤗
_Pheenar Abdallah_
_Mmn Ra'ees_
_Rabi'a s sabo_
_My Ƙawata Maryam A Tafida_
_Jameela Jameey_
_Mmn Khairi_
_Shema'u Sadi_
_Mmn Musaddiq_
_Queen Miemie_
_Fatuma Bintu_
_Mmn Samha_
_Aumar Rabi'atu_
_Aunty Zainab_
_Ummu Abdul Jabar_
_Halima_
_Meenal_
_Tawajena ƴar lelen mammarta_
_Faexa_
_Mmn Baffa_
_Momi_
_Zainab_

~*Afuwa wanda ban ambaci sunanku ba, Wlh zana suyewa wuya yake bani, yanzu ma dan tinda na fara Ruwaida ban taɓa ambatar kowaba, amasu comments, nayi dan na faranta maku, kamar yanda kuke faranta min, Ngd.👏🏼🙏🏼*~

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 30*

Rahma ta saki fuskarta tace“Eh wlh, bismillah ku zauna se ku sanar min da kanku.” farar kyakyawar ta murmusa tace“Mun gode Rahma.”  ta faɗa suna zama saman kujera me zaman mutum biyu.   Rahma taje ta kawo masu ruwa da lemo a fridge ɗin mmn Sabreena, ta tsiyaya masu.   Samira da Saudat da mmn Sabreena, kallon ƴan matan suke, saɓanin Rahma da take danna wayarta.  Bayan sun sha lemon sun gama, kyakyawar tayi gyaran murya tace“Da farko dai sunana Zulaihat ƴar uwata Zainabu, mun kasance ƴaƴan gata wajan iyayanmu, bamu nema ba muka rasaba, hakan yasa bamu aikata ɓarna, adoron ƙasa wa bil'adama, amman sakammakon ɓarnar da wani ɗan shegiya ya aikata ga kakan kakar ubanmu, yanzu haka  idan kinga halin da suke ciki zaki tayamu mu ɗauki fansa...”Rahma ta katseta ta hanyar cewa“To bayin Allah ni me haɗina daku, da zan shiga rikicin ɗaukar fansa?  Yanzu dai ku suwaye? A ina kuka sanni?
                    Me kuke nema wajena?” Rahma ta jefo masu tambayar, tana me karanto duk addu'ar da tazo bakinta, sbd sam bata ƴarda da wannan ƴan mata ba, neman tsarin Allah take daga wajansu.  Tace da Saudat“Ku kashe kiɗan ku kunna suratul Yasin.
             Haka ko Samira  ta kashe kiɗan suka kunna suratul Yasin suka zauna suna karanto addu'ar neman tsari daga Allah.
                                Rahma tace “Ina sauraranki Zulaihat!”   Zulaihat tace “Daman ɗazune A hospital... Sai ta miƙe wayarta na ringing ta ɗaga takai kunnenta ta fice tana mgn.   Zainabu ta bita abaya.   Rahma tace“Ikon Allah wai daga ina suke ne? Anya ba yarinyar nan Nazeefa ba, ta turosu domin su wargazamin farin cikina?”  Mmn Sabreena tace“Ba mamaki ke nifa kyawun ɗayar har tsoro yake bani, sai kace aljana, naji daɗi da kuka kunna mana karatun, koma suwaye li'ilah fi ƙuraysh aniyarsu tabisu...”Saudat “Wlh nima na tsorata.” Rahma tace“To ina kuma suka tafi?”🤔  Samira tace“Oho masu anzo gulma ne daman fa kuma ba'aga fuskar yinta ba.  Dariya suka kwashe da ita, sukaci gaba hira duniya.
                       Zulaihat suna fitowa waje, aguje tana riƙe da cikinta sbd yanda karatun ya fara shigarta, take suka rikeɗe suka koma wata halitta ta daban mai abin tsoro mai firgitarwa, wanda ace su Rahma zasu gani ba abinda zai hana basu suma ba.     Tsayinsu bai misaltuwa, ga wani irin manya kawuna da idanu ƙwala² harshe awaje, bakin mai wani irin tsini. Sai ga wasu manyan fuka-fukai sun baiyya a kafaɗinsu, suka tashi sama suna wani irin gurnani, kai tsaye niger suka nufa suna kuka.
                       Wato abinda ya faru A hospital shine, tinda aljannun nan suka ga Acp da malam suna mgn akan zasu zo asibiti hankalinsu ya tashi, daman arakuɓe suke sbd karatun.     Abbah da Musaddiq suna zaune, kusan Ruwaida bayan drip ya ƙara an ƙira Dr ya cire mata, har lkcn bacci take karatu na ta tashi aɗaki, sai suka ga Ruwaida jikinta na wata irin kyarrrma Abbah ya riƙeta yana ƙiran sunanta, Musaddiq na tofa mata addu'a atishawa tayi guda uku ajere, wanda suka fito da wani baƙin hayaƙi.  Kawai sai sukaga Ruwaida ta buɗe idanunta ahankali ta sauke su kan Abbah.   Abbah yace“Sannu Ruwaida me yake miki ciwo yanzu?”  Ruwaida ta girgiza kanta, tama Abbah nuni zatasha ruwa.   Musaddiq ya miƙe cike da tsoron baƙin haƙin da yagani ya fito bakin Ruwaida, ya buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin, ya ɗauko faro ɗin da ɗazu ya siyosa, ya kawo mata, ya zauna ya buɗe ya beƙama.   Amsa tayi ta gyara zamanta ta kafa bakinta saida ta sahnye tas ta janye bakinta tana maida numfashi.
                      Abbah kallonta auke ganin ta shanye ruwan, yace “Sannu Ruwaida zakici abinci?” kai ta ɗaga ta masa nuni zatayi sallah.   Bayan ta gama sallah Musaddiq ya zuba mata lafiyayyar jalof ɗin shinkafa wace taji kayan lambu, da busashan kifi.  Sosai Ruwaida taci girkin tasha lemo, ta tambayi  Abbah da hannunta Mummy da yayanta.  Abbah yace“Yanzu suka tafi gida ba jimawa bari aƙira Dr ya dubaki sai ya bamu sallama yanzu bakyajin amman?” Ruwaida ta kalli Abbah cikkn mamaki ta girgiza tana masa nuni da hannu bataji.
                 Musaddiq yace“Alhamdulillah wlh Abbah inaga kaidunsu ne daman, bari na ƙira Dr.” ya faɗa yana ficewa daga ɗakin. Ruwaida dai kanta aƙasa tana wasa da yatsotsin hannunta.   Dr yana zauwa yasha mamakin ganin Ruwaida kamar ba ita bace ɗazu a sheme, ɗakin gwaji ya kaita ya shiga mata gwajin irin na farko, bayan ya gama mata ya maidota wajansu Abbah kafin yaga abinda sakammakon zai bada. 
               Sukuma shegon bayan sunbar jikinta shine jikar ɗiyar Jodaaaaaaaah tace suje wajan matarsa matuƙar malamin nan ya iskosu wlh zai tarwatsa kome nasu ya ƙonar dasu, suje wajan matar da Safwan zai aura sai su tarwatsa masa farin cikinsa, sbd sunsan sonda yake mata da zaran tace ta fasa auransa, zai shiga damuwa kuma zasuyi anfani da ita har su sami damar cutar dashi, da Ruwaida.    Shine suka rikiɗe suka zama ƴan mata kyawawa suka nufi gidansu Rahma wanda canma basu sami nasaraba, suka fito kafin karatun ya masu illah kuma ƙarya suke ba wai sunayensu bane suka faɗa sbd su ba musulmai bane, shine yanzu sun nifi niger cikin tashin hankali su sake ɗaukarwa Acp shiri, dan yanzu yafi ƙarfinsu haka Ruwaida na tare da karyarsa baza su iya  da itaba, idan suka matsa zasu mutune ko anakasa masu dangi baki ɗaya...
               Acp yana shiga cikin hospital ya shiga parking spece yay parking, ya fito ya buɗe masu mota suka shiga ciki.   Abbah da Musaddiq na zaune Ruwaida na kusan Abbah zaune, suna jiran Dr ya kawo sakammako.   Acp ya turo ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, malam da Hamza da yaron malam suna biye dashi.
Ruwaida jin sallamar Acp yasa ta ɗago da kanta, karaf kuwa idanunsu ya sarƙe da juna wani irin abune sukaji atare idanunsu cikin juna.  Cike da mamaki yake ƙara kallonta gata rass azaune, ƙurr ya mata da fitinannun idanunsa, masu narkar mata da zuciya, yana wani lumshe mata su, ya mata nuni da idanunsa ta miƙe tsaye.
              Narai-narai Ruwaida tayi da idanunta tana kallonsa tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ta maƙale kafaɗarta.  Lallausan murmushi mai sanya zuciyar masoyi ya kuma sakashi shauki ya sakar mata ya maƙale kafaɗa alamar shikenan tinda bazata tashi ba.
             Ƴar siririyar dariya tayi tana kallonsa tana rufe fuskarta da tafin hannunta,tana langwaɓar dakai gefe.    Abbah kallon ikon Allah yake yadda Ruwaida ta saki ranta daga ganin Acp har dariya take masa, ya jinjina ƙarfin shakuwarsu, ya miƙe cikin fara'ah yake faɗin“Musaddiq kaga ƴar gidan Acp ko? Mun gama tsaronta kusan rabin yini, koda ta farka ɗazu bata mana murmushi ba,  amman yanzu ubangidanta takema dariya, to yayi kyau.” ya faɗa yana murmushi ya isa  taro  malam yana faɗin“Barka da zuwa malam sannu da hanya.” ya bashi hannun sukayi musabaha, ya masa jagaro har wajan kujera yaja masa yayi bismillah ya zauna.
                    Malam yace“Yauwa Alhj ina yarinyar take?  Abbah ya nuna masa Ruwaida tana zaune, rass ba alamar ciwo ajikinta.    Malam ɗan Asabe ya ƙura mata idanu yace “Kayi hƙr ka bani lbrn ya ta miƙe rass ba alamun jinnu atattare da ita?  Kaɗan mini bayani yadda zamu fuskacin lamarin.   Ya faɗa yana kallo Abbah.  Abbah yayi gyaran murya ya shiga faɗamasa yadda abin ya kasance ɗazu.
              Hamza jin irin  bayanin da Abbah yakema malam yasa cikin farin cikin ganin Ruwaida rass tamkar ba itaba suka bari asheme ɗazu, ya iso  yana faɗin“Musaddiq ya jikin nata? Masha Allah Allah yasa sun barta kenan, ina Dr? Ya lbrn cikin?”  Acp ya iso dab da gadon da Ruwaida take zaune cikin farin cikin jin abinda Abbah yake faɗama malam, ya tsaya gabanta ya beƙa mata farin lallausan hannunsa  yace“Oya taso.” Ruwaida ta sadda kanta tana maƙale kafaɗa tana murmushi.   Ƙara matsowa yay yana shirin sanya hannunsa ya kamo hannunta ya miƙar da ita Dr ne ya turo ƙofar ya shigo sallama ɗauke abakinsa.  Musaddiq da Hamza atare sukace “Dr me sakammako ya nuna?”   _*Kai Ƙwaranƙwatsi nifa yau ƙiwuyar typing nakeji,😂 ku kawomin gasassun zabbi maau ɗumi, yasin banason wanda suka fara hucewa,😉 da juice me sanyi naci nasha  ina bubbuɗe hanci irin na inna Zinaru, na ɗaga ƙafa sama sai naɗora maku daga inda na tsaya.😆🤪🤪🤪*_

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now