Chapter 27

363 15 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

_*Tukuici Gareki Aunty  Maryam Ta Malam Shaglinku Uwar Gida Kuma Amaryar Malam Musa💃🏻💜Son So Nake Miki.*_😘



*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 27*

Arikice Abbaye ya shiga jijigata yana ƙiran sunanta, “Ruwaida!! Keda wayene? Mummy su islam basuje school bane...?”  ya tambayi Mummy yana ɗaukar Ruwaida caɗak ya dagata sama ya rungumeta kamar beby, ya nufi saman kujera da ita, cikin sauri yana ɓoye tsantsar damuwarsa, amman hankalinsa a mugun tashe yake ganin bata ko motsi ta suma. 
                         Mummy ta iso arikice tana faɗin “ A'a basa nan abin mamaki bari aɗauko ruwa a yayyafa mata, Abbansu don Allah leƙa ɗakin kaga meke faruwa.” Monmy ta faɗa tana nufar kitchen da gudunta.   Abbaye kwantar da ita yay saman 3 seater ya zauna ya ɗora kanta saman cinyarsa, ya kama hannunta duka biyu yana murzawa, da sauri² yana ƙiran sunanta, ya shiga tofa mata Addu'a.  Musaddiq ya nufi ɗakin da gudunsa yaga ko meye ya firgita baiwar Allah haka.  Abbah yace“Ka tashi muje hospital zaifi asume take fa.   Bappa yace“A'a yaci gaba da tofa mata Addu'ar azuba mata ruwan mugani, idan bata farka ba sai muje asibitin, bari muga meye aɗakin.” dukansu har Hamza wanda ya tsorata da lamarin jin ba kowa aɗakin, sukabi bayan Musaddiq.
                                    Mummy ta kawo bottel ɗin water me sanyi na Faro, ta buɗe ta beƙama Abbaye, ya amsa ya tofa Addu'a acikin ruwan ya zuba ahannunsa ya shafa mata a fuskarta ya ɗan zuba mata daidai saitin bugun zuciyarta.  Wata wawar ajiyar zuciyata ta sauke da ƙarfin gaske, jikinta na wata irin kyarrrma.  Ta saki wani irin ƙara mai firgitarwa, ta kece da kuka, Acp ya manneta jikinsa yana buga bayanta, bakinsa dab da kunneta yana meci gaba da tofa mata Addu'a.
                                              Mummy ta zauna tana riƙe da hannunta, itama Addu'ar take mata, sai mutsu-mutsu take, tana son ƙwace jikinta ba hali saboda irin rungumar da Abbaye'n yay mata.   Can kuwa ɗakin nasu Ruwaida Musaddiq yana shiga ya fara waige² baiga kome ba, sam babu wani alamu dan shimfiɗa gadon agyara take tsaf.   Juyawa yayi arikice ya nufi bathroom yana faɗin.    “Mamaki ikon Allah me nake shirin gani....? Su Abbah ne da Baffa da Hamza suka shigo suna faɗin.    “Meke faruwa Mudaddiq?”
        Musaddiq yace“Wallahi babu kowa kalli shimfiɗarma a gyara, bari naga toilet.   Ya faɗa yana buɗe ƙofar toilet ya shiga da bismillah.  Wayam ba kowa, ya shiga leƙe ko ina ba alamun ɗan adam.
     Fitowa yayi yana faɗin“Ikon Rabbi wallahi iyayena ba kowa fa.”  Abbah da kansa ya shiga leƙa ko ina har window ƙasan gado da ko ina ba kome, ya ɗago yace“Ruwaida inaga mafarki ne tayi, ta tsorata wajan sauka daga gado ta faɗo ta fasa baki, dan naga jini abakinta.”  Hamza yace“Tabbas kuwa.    Fitowa sukayi falon.   Acp na cikin mata Addu'a yaji saukar numfashinta tayi lamo jikinsa, bacci ya ɗauketa.   Mummy tace“Anya ba aljanu ke damun baiwar Allah nan ba kuwa, Abbanmu?”  Abbaye ya ɗago zaiya magana,su Abbah suka iso, Bappa yana faɗin.    “Safuwan yarinyar nan mafarki kawai tayi, maras kyau ta firgita.”  Ummani tace“A'a wannan lamarin aikin jinnu ne, kalli Addu'ar da suka mata har tayi bacci, sannu me gidana Bahijjah Allah biyaku da gidan Aljannatul firdausi.”    su Abbah suka amsa da “Ameen.    Musaddiq yace“ Mamakin da nake fashewar bakinta...” Abbaye ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita saman doguwar kujera ya ɗauki mayafin da yagani ajiye saman kujera na Mummy ya luluɓeta, ya sanya hannunsa ya goge mata dan guntun jinin dake saman laɓɓanta, ya ɗan buɗe bakinta baiga kome ba alamar jimuwa, sosai abin ya bashi tsoro, fuskarshi yakai dab da tata ya ƙara buɗe bakinta ya shiga tofa mata addu'a cikin bakinta yana shafa kanta, ya ƙura mata tsumammun idanunsa, sam bai damu da iyayansa ba da suka zagayesu, saida ya gama mata addu'ar, ya gyara mata kwancinta ya rufe mata fuskarta, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsu ba tare da yama kowa mgn ba.    Da idanu suke binsa da kallo suna mai jin daɗin kasancewarsa jininsu, tabbas Safwan  namijine sunsan idan Ruwaida na tare dashi, tabbas sai abinda Allah ya ƙaddaro mata zai sameta, amman shiɗin garkuwarta ne.... Abbah ya zauna yana kallonta cike da tausayawa, yace“Allah kaɗai yasan dalilin fitowarki da kuma haɗaki da Abbana, dan shiɗin garkuwarki ne.” Bappah yace“Tabbas ishaq.    Musaddiq yace“Ina zargin fa aljannun nata nema suka rufe mata baki, ya Allah kabata ikon yin mgn.” suka amsa da“Ameen.
                                      Abbaye  bedroom ɗin yabi da kallo, yaga kome a muhallinsa ba wani alamar mutum, kai ya jinjina ya gyara tsayuwarsa yana zura hannunsa aljihun wandon unform ɗinsa, ya ciza lips ɗinsa, yace“Tabbas sheɗannun aljannu ke bibiyar kanwata, kuma nasan kuna kusa kuna jini tabbas na kusa tarwatsaku kuda zuri'arku baki ɗaya, koda kuwa kunfi kome yawa afaɗin duniya wlh wlh wlh matuƙar baku shafama Ruwaida lfy ba, zan kawo ƙarshanku idan kun fasa bibiyarta kunƙi Allah da manzon sa... Koda yake daman bakwa tare dashi la'anannu kawai.”  ya faɗa yana sauke dogon numfashi sbd doguwar mgnr da yayi, ya isa bakin bed ɗin ya ɗauki wayarta da take ajiye kusan pillow, ya kunna suratul baqarah ya ajiye kan gadon,  ya shiga tofa ma kowace kusurwar ɗaki Addu'a.  Gabaki ɗaya saida ya tofe ɗakin da Addu'a ga baqarah na tashi, ya buɗe wardrobe ya ɗauko mata doguwar riga da ɗan,kwalinta ya fito ya rufe ƙofar.
                                                              Zama yayi ya ɗagota ya zura mata rigar kan kayan baccin ya ɗaura mata ɗan,kwalin, ya kwantar da ita, bacci take sosai tana fitar da numfashi daki-daki.  Wayarsa ɗayar ya  sakata A (mode hors ligne)  ya kunna suratul baqarah ya ajiye kusan kanta.
               Ya kalli Mummy yace“Mummy! idan Baqarah nan ta ƙare ki tasheta tayi wanka pls ki bata abinci, zan tafi wajan aiki zan dinga ƙiranki naji ya take, pls akularmin da ita.” ya faɗa yana rankwafowa yama Mummy kiss ya dawo wajan Abbah ya masa yama Musaddiq, da Bappa da Hamza ummani ya masu sallama ya fita yana waya.   Abbah yace“Allah ya maka albarka babanmu.” Musaddiq ya miƙe yana faɗin “Ameen. Ya nufi bedroom ɗinsa domin ya kwanta ya huta.  Su kuma suna hira jifa-jifa.
             Cike da takunsa na jarumin namiji mai jin kansa ga kuɗi kyau nasaba ga uwa uba kwarjininsa.   Anutse yake takunsa har compound ɗin gidan, ma'aikatan gidan sai kwasar gaisuwa suke, yana ɗaga masu hannu, kasancewar yana waya da mai girma commissioner, akan ya zauna sai yaji sauƙi fafur Acp yaƙi.   Wata zafaffiyar mota me numfashi security ya buɗe masa, sauran suna sara masa alamun basa girmansa ya ɗaga masa hannunsa ya shiga seat ɗin baya ya kame, suka rufe masa ƙofa, suka shiga direbansa wanda ke sanye da unform ɗin police, bayan ya gaishe da Acp cikin girmamawa yama motar key yaja nufi bakin gate, megadi ya wangame masu ƙaton gate ɗin ya sulala motar waje.
                                      Kai tsaye ( *Police Headquarter*)   ya nufa yana tuƙinsa anutse.  Rahma ya ƙira.
       lkcn tana kwance sbd tsakar gidan ba laifi ƴan uwan innarta ne wasu na babanta har sum iso tarabar kaya, su Asma'u da maman Sabreen, sunata hidimar gyara kayan tarbar baƙi ƴan kawo lefe, Zainab na makaranta, itako bata tafi ba, sbd har yanzu batajin daɗin cikin nata shiyasa bataje ba  makaranta.    Ɗaga ƙiran tayi tare da sallama, tana faɗin “Amincin Allah ya tabbata agareka Nawan.”  Acp yace“My dear ya kika tashi hope kinji sauƙi?”   Rahma tayi fari da ido cikin dauriyarta tamkar tana gabansa tace“Alhamdulillahi My Qalbi.”  Acp yace“Masha Allah ki huta abinki, anjima fa ana kawo kayanki.” ya faɗa yana dafe goshinsa, sakammakon Ruwaida da ta faɗo masa, a ransa!  Rahma cike da jin kunya tace“Eh ga su Aunty Asmy nata aikin kayan tarbar baƙi.” ɗan guntin smile ya saki yace“Ok bye ina kan hanya zanje wajan aiki, ƙanwarki batada lfy yanzu haka na barota tana bacci...” Rahma ta yamutsa fuska tace“Allah bata lfy nima ai kwance nake ko my Qalbi?” Kai ya ɗaga kamar tana ganinsa yace“ Na sani my dear amman ai ita ƙaramace akanki sosai kuma ciwonku ba iri ɗaya bane, ita abin tusayice...” Rahma bata san lkcn da tace “Ni kuma abin haushice ko?” Acp ya dafe kansa sbd sam fa shi ya tsani ma doguwar mgn, cikin daddaɗar muryashi yay ƙasa da ita, yace“Uhm-uhm my Rahma ban ceba amarsuna afuwa bye zan ƙiraki anjima ki kularmin da kanki...” Kitt ya kashe ƙiran, yana murmushi sbd yaga kamar Rahma ta saka wani abu aranta alamar kishi, kuma shi kansa yasan tana sonsa ba da wasaba.  Sajansa ya shiga shafawa yana lumshe fitinannun idanunsa.
                                      Rahma ta ƙurama wayar idanunta tana jin wani irin kishinsa nabin kowane jininta da tsokarta, ta ciza bakinta ta miƙe zaune cikin zafi-zafi take faɗin“Ita yarinyace akanki sosai.... Ok! ok! ni na tsufa kenan? Shekaru 23 rak har yana ikirarin Ruwaida yarinyace saboda na bata shekarun da basu fi 5 ba dan zata kai 18 year koma 20 year😡shine har na wani girma hummm☹️ Acp kenan zan saka maku ido naga me nufinku kai da ƴar kurma.”😬ta faɗa cikin ɓacin rai tana jin jifa da wayar ta koma ta kwanta, tana sauke ajiyar zuciyar ɓacin rai, duk taji daɗin yadda Acp ke lallaɓata amman yau ya bata haushi ƙiran Ruwaida yarinya ce kuma abin tausayi ce... “Hummm tace ta rufe idanunta, kenan Innah ta shigo ɗakin tana faɗin“Rahma ba kince zaki ƙira ƙawanki su zo ba, naga shiru bakida niyar tabuƙa abin arziki, ko cikin ne? Sannu kinji.” Rahma ta yamutsa fuska tace“Innata ai ba yanzu ba, sai yamma, ba fa wasu gaiyya xanba, Samira ce da Saudat da ƙawayansu zasu zo, anjima zan daure na ɗan masu wani abun motsa baki, ko na ɗauka anaku.” ta faɗa tana kallon innarta da tasha sabuwar atamfa mai tsaɗa wacce Acp ya kawomata, tayi kyau sosai abinka da farar mace tasha ɗauri sai buɗe hanci take harda su handbag ta Rahma ta rataya.😄
                                   Inna tace“Ke!! Rahma! Lfy kika tsareni da idanunki irin na malam?” Rahma duk da tana cikin ɓacin rai saida ta dara tace“Kai innata to idan ban kalli uwata ba wa zan kalla naji daɗi?  Kinmin kyau ne.” inna tayi murmushi tace“Ai dole surukar Acp gudu ta fita daban da sauran mata, wani abun ma sai kin shiga, dan ma Allah yayi ubanku da son wani nuna dattakunsa fafur ya hana a maidamu inuwa muna rana...” Rahma tace“Alhmdllh inna dan Allah ki daina faɗin hakan sam bayamin daɗi, kuma ki tuna yau bamu kaɗai bane...” Inna ta isa wajan abinda tazo ɗauka tana faɗin“Naji kar cikani da surutu ga ɗan akuyan can an yanke fa, har an fara gyara naman.” ta faɗa tana ɗaukar ledar ta fice.    Rahma zanin rufar taje ta rufe duka jikinta, ta rufe idanunta sam bata jin daɗin zuciyarta, tanajin hirasu Asma'au sai raha suke abin gwanin burgewa, ahaka bacci ya ɗauketa.
                                       Acp bayan yaje wajan aikinsa jama'a basu barshi ya zauna ba, sai barka ake masa da Addu'ar Allah ya kiyaye gaba.  Masu baƙin ciki kuwa nayi wanda basu so ya miƙe ba, bayan sun gaisa da commissioner ya nufi office ɗinsa yana duba files ɗin jama'a ga ƙiran jama'a waya kan waya sbd  ya barma Ruwaida ɗayar ba'a samunsa, shiyasa aka addabesa da babban layin, ga ƙira da wayar office, yana aiki yana shan coffee, bai samu kansa ba sai ƙarfe 1 na rana.  Yana zaune saman lumtsumemiya kujerasa yana juyi ya ɗaga kansa ya kalli agogon dake manne abangon office ɗin nasa, yaga ƙarfe ɗaya da minti 10 goma cif.  Fitinannun idanunsa ya lumshe ya cire hula yana shafa kwantacciyar sumar kansa, ya buɗe idanunsa ya ɗauki wayarsa ya lalubu number Mummy ya danna mata ƙira.   Can kuwa tin fitar Acp Ruwaida bacci take kamar kasa bata farka ba, kamar yanda ya cema Mummy da karatun ya gama atasheta tayi wanka taci abinci haka kuwa akayi.    Mummy ta tashe tako tashi, ta kamata suna nufar ɗakin ta kafa kuka baxata shiga ba, jikinta sai kyarrma yake, Mummy ta kaita bedroom ɗinta ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗumi, ta shiga kafin ta fito taje ta ɗauko mata kaya, riga da siket na shadda blue da lotion da turare  ta ajiye mata.
Bayan ta fito ta shafe jikinta da lotion ta saka shadda ta zauna mata cif ta gayara gashinta ta tufƙeshi baya, ta ɗaura ɗan,kwalin Mummy na zaune na kallonta tace“Ɗiyata kinyi kyau sosai maza muje kici abinci, sai ki faɗamin me ya faru dake ɗazu da safe.” Ruwaida ta zauna kusan Mummy ta kwantar da kwanta kafaɗarta ta lumshe idanunta jikinta take ya ɗauki zafin zazzaɓi.
       Mummy ta tsorata da lamarin ta kamata suka fito ta haɗa mata abincin, tana bata da kanta taci ba yawa sai amai da  rawar sanyi , Mummy ta ƙara tsorata ganin yadda take amai, ga Abbaye aiki yaje bai kamata ta ƙirasa ba ta ƙira Abbah da suka fita da Hamza tana faɗa masa yace Musaddiq ko Sani direba ya kaisu asibiti zaibi bayansu.   Musaddiq ta ƙira kusan sau biyar bai ɗaga ba, ta ƙira Sani  tace ya fito ɗa mota zasu hospital.  Hijabi ta saka mata ta kama hannunta tama su larai sallama tana tamabayar me zasu dafa bata amsa ba taja hannun Ruwaida suka fito compound ɗin gidan.  Da Taslim suka haɗu itada ƴan uwan mijinta har sun iso.   Suka gaisa Mummy tace“Nasan yanzu maƙota sa fara shigowa dan na tura su larai sun farfaɗa, so gashi zamu asibiti Ruwaida za'a duba ki fito da kayan duk wanda yazo ya gani kafin masu kaiwa su iso.” tana faɗi haka taje Ruwaida suka shiga mota.  Taslim ta masu Addu'ar samun sauƙi suka shiga ciki su hudu biyu ƙannin mijinta ɗaya yayarsa.  Suna zuwa hospital aka shiga bata temakon gaggawa saboda yadda jikinta yake ɓari, ga amai.  Mummy sai kai komo take, ahaka Abbah da Hamaza suka sameta suna jiran fitowar Dr.  Bayan 1 hour sai ga Dr Junaidu ya fito bayan an gama mata gwaje² an ɗaura mata drip wanda yasha allurai.   Yana goge zufa da kuma mamakin wani abu, yake takowa.
       Mummy ta miƙe cikin rawar jiki ta taresa tana faɗin “Dr ya jikin na Ruwaida meke damunta haka?? Dr ya kalli Mummy dasu Abbah wanda suka miƙe suma suka nufosa.  Tofa adaidai lokacin ne Acp ya ƙira Mummy tana ganin ƙiran taƙi ɗauka.   Dr yace“Muje office sai na maku bayani yanzu jikin da sauƙi, ta samu bacci...” Mummy tace kamana anan mana in da hali ma sai asakemo yanzu ta daina aman? Ya zazzaɓin....”?Dr ya katseta yace“ Hajiya Wai daman Ruwaida tanada Aure ne..?”  Abbah ya ɗago Amugun mamakance ya kalli Dr yace......!!

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now