Chapter 34

403 13 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''





*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 34*

Wani irin ihuuu Samira da Fadila suka saki atare, suka nufi wajan Rahma suna ƙiranta.  Direban ya rikice sosai yana ta faɗin“innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!  Ya take burki da kyat. Sauran motocin da suke  biye da motar, suka take wani irin burki da ƙarfi. Direban ya rikice ko takan su Mai martaba bai biba, ya buɗe motar ya fice, wajan Rahma da sauri.  Dogaran sarki tuni suma sun rufa masa baya. 
                         Mai martaba, Abdulhakim sarkin Jalingo, shida mai martaba Sulaiman sarkin damagaram ba abinda suma suke faɗi sai faɗin “innalillahi wa'innah ilaihir raji'un!! Mai martaba  ya bada umarnin a buɗe masu ƙofa  su fito.  Yarima Al'amin yace“No ku zauna bari mugani.”ya faɗa cikin izzarsa, yana bada umarnin a buɗe masa mota.  Cikin takunsa na ƙasaita ya iso wajan, yayin da dogarai ke take masa baya.  Samira  ta rungume Rahma tanata sharɓar kuka, cikin masifa take faɗima direban“Kai bakada hankaline? Baka iya tuƙiba? Jibine auranta gashi ka kasheta... “Wayyo inna daman saida kikace karta rakomu amarya tsautsayine da ita...”  Yarima ya zabgama Samira harara yace“Ke!! Dallah matsa atemaka mata tana zubar da jini, ta hancinta nima ai angon ne ta jaza mana masifa ai idan ta mutu.”  ya faɗa yana isowa dab dasu ya rankwafa, cikin dauriya ya sanya hannun zai ɗauketa, sai yay saurin janyewa yace da Samira“Kamata keda ƴar uwarki kusa amota.”yanayin da yayi maganar ne yasa suka kasa musawa, sai lkcn Samira ta gane ashe yarima Al'amin ne.  Cikin dauriya suka cicciɓi Rahma suka nufi wajan motar.  Mai marta da ido ya bisu sai yaga kamar yasan fuskar.  Suna isa aka buɗe masu mota ta tsakiya suka kwantar da ita suka sakata A tsakiya. Yarima ya koma motarsu ya zauna yana faɗin“Ku kwantar da hankalinku bata bugu dayawa ba.”Sarki Sulaiman yace“To yaron kirki Allah yasa.”Sarki Abdulhakim yace“Ameen.”  Kai tsaye hospital suka nufa. A bakin gate ɗin *City clinic* motocin suka faka ana zuwa horn. Suna shiga ciki babu ɓata lkc aka amsheta aka shiga bata temakon gaggawa.  Bata wani ji rauni sosai ba, tsaɓar tsorata ne da tayi yasa ta suma, sai hancinta ya bugu, sai goshinta ya ɗan tsage an ɗunki, ɗinki biyu, ƙafarta ta ɗan bugu kaɗa amman bata wani gwalje sosai ba.
                                 Bayan likitan ya gama mata duk abinda zaiyi, ta farfaɗo sai kuka take tana ƙiran innarta, kamar wata jaririya.  Dr ya fita waje dan ƙiran wanda suka kawota.  Samira da Fadila suka taresa suna faɗin“Dr ta farfaɗo?” Dr yace“Eh jikin nata da sauƙi...” Yarima yace“Munaso mu ganta zamu wuce gida.” Cikin girmamawa Dr yace“Bismillarku, sai kuka take.” Cikin takunsu na nuna isarsu suke takawa suka nufi ɗakin da Rahma take.  Su Fadila na take masu baya.
                        Hawaye kawai ke tsiyaya a foskar Rahma tana dafe da goshinta.  Da sallama suka shigo.  Bata iya amsawa.  Kanta ta ɗago yayi daidai da kallonta da sarki Sulaiman yake, idanunsu suka sarƙe waje ɗaya.  Rahma ta ware idanu atsorace ta sake murza idanunta, still dai abinda ta gani copy Ruwaida kawai dan dai shi namijine, kuma shi ba baƙi bane ba.
                         Kansa ya ɗauke daga kallonta yana me jin faɗuwar gaba me tsanani.  Kallonta  ta maida kan yarima ya zabga mata harara yace“Ke!! Bakisan ki nutsu ki tsallaka titi ba, kin kusa samu a uku ni kam wlh da baza'a wani ɗagamun biki ba, sai anyisa agobe ko da kuwa ace kin sheƙe...” Rahma  ta haɗe fuska ta kauda kanta tana kallon Samira cikin kuka² tace“Ki ƙiramin innata da Babana ki faɗawa Acp kinji.” Mai marta yace“Ɗiyata ya jikin? Hope bakiji ciwo sosai ba ko?”Rahma tace“Eh Abba da sauƙi ngd kuyi haƙuri ba da gangan na hau kan titi ba.” Sarki Sulaiman yace“Sannu Allah baki lfy.” Rahma ita tsoronsa ma take bata iya amsawa ba ta jinjina kai.  Dr ya shigo ya masu bayanin kome amman yace bazasu saketa ba yau sai zuwa gobe.  Nan suka mata ya jiki sukayi tafiyarsu sai dare zasu dawo domin subama iyayanta haƙuri.
                              Suna tafiya Samira ta ƙira inna ta faɗa mata.  Wai karkaso kaga masifa wajan inna, nan suka shirya har malam suka nufo asibitin.   Ruwaida kuwa kusan rabin wuni tayi tana bacci zauwar Acp biyu tana bacci, sai ya koma wajan aikinsa lokacin da ta farka, kusan lkcn da aka bige Rahma ne, wato yamma bayan la'asar, ta farka cikin ikon Allah batajin kome.  Mummy ta sakata tayi wanka taci abinci, Dr ya kuma dubata ras da ita, ya basu sallama Mummy ta ƙira Sani direba yazo ya kaisu gida, tinda Abbah sun fita da Mussaddiq.  Suna hanya ne Acp ya ƙira Mummy take faɗa masa yanzu suka taho suna hanya.
                           *Anguwar Gadi*   manya mayan moticun suka nufa.  Tin kan su iso kakejin kiɗa da algaita na tashi tamkar yaune auran ba gobe ba.  Wani tamfatseysan gidane kana kallonsa kasan gidane na sarauta, tsayawa faɗar gidan mai martaba sarkin Jalingo Abdulhakim ɓata lokacine.  Suna shiga da motocin ai kuwa masu busa algaita suka baibaye motocin suna busawa ana watsamasu ƙirarani.  Wani ƙaton lallausan kilishi ne aka shimfiɗa tindaga jikin motar da zasu fito har  zuwa ƙofar da zasu shiga.  Dogarai suka rufesu ba wanda yaga fitowarsu sai yarima Al'amin.  Ta ko ina sannu da zuwa babban aminin sarki Abdulhakim yake sha, wato sarki Sulaiman.  Cikin sakin fuska yake ɗagawa jama'a hannun sosai yayi farin cikin irin wannan tarba da ya samu, ta ko ina sunansa kakeji ana ambata.  Haka suka jera ana kakkare dasu dogaransu na take masu baya amman su ba su hau kilishin ba.  Yarima sosai yake farain cikin zauwar abokin mahaifin nasa sarki mai dattaku.   Wani lafiyayan falo suka shiga wanda yake tamkar aljannar duniya, duk da ko kusa bai kamo ƙafar nashi ba amman sosai yanayin inda aka tarbesa ya burgeshi. Saman kujera ya zube ya dafe kansa, Ruwaida ta faɗo masa“Ko tana wace duniya ayanzu?” Mai marta yace“Ka ƙara haƙuri yarinyarmu zata baiyana bi'izinillah.” haka yay ta masa nasiya har ya saki jikinsa suna mgn tasu ta manya. Iyalan sarki aka masu iso suka kawo gaisuwa wajan sarki Sulaiman. Hakan ya ƙara masa jin daɗi sosai.
                       Inna suna zuwa hospital ganin Rahma harda ɗinki agoshi ta fashe da kuka, ta rungumeta tana faɗin“Ashe da ya kasheki? Wai shiɗin ɗan uban wanene ma...” malam ya katseta yana faɗin“Zinaru kinada hankali kuwa? Ke kome ya fito bakinki  faɗi kike? Haba mu godewa Allah ma da abin ya tsaya a haka, idan yaso da gawarta kawai zamu taras, to muyi yaya? Hƙr zamuyi kuwa dole... Rahma ya jikin naki? Sannu.”  Rahma tace“Da sauƙi Baba, innata kiyi hƙr zan warke, yarima Al'amin ne fa ɗan sarkin garin nan.. Dan na sansa yana zuwa makarantarmu, kuma naji anata shela agidajan Tv da redio gobe ɗaurin auransa, aikuwa kinga ba da gangan ya kaɗeniba.. Iyayansa har hƙr suka bani...”Samira tace“Wlh da farko na ruɗe ban gane shibane, dan na zata an kasheki fa.” Inna tace“Allah takaita amman shine dan suna sarakai bazasu bari iyayanki suzo ba, sai suka ɗauki hanya suka tafi, ai ko dogarai sa abari ayi tsaronki kafin muzo...”Malam yace“Ya ilahi!! Zinaru! Zakuwa kiyi hankali aduniya? Wannan fa ƙawayan ɗiyarki ne, amman kike zuba hauka, me kuka haɗa dasu za'a ba ɗiyarki dogarai su tsareta?” Inna ta bushi iska tana ɗaga hanci tace“Malam kaci bashin mgn yanzu bazance kome ba wlh.” Rahma ta fashe da kuka tace“Dan Allah inna ki barni naji da ciwona, haba dan Allah.”
                Inna tace“Allah baku haƙuri.” Samira tace“Inna bari muje gida sai mu faɗawa su umma zamu dawo zuwa dare, tinda Dr yace sai gobe zai saketa.” Inna tace“To sannunku yaran kirki adai dingajin mgnr iyaya, ai kunga na hanata rakiya tayi gashi abinda ya sameta, gobe ta ƙara.”  Su Samira dai basuce kome ba, sukama Rahma sallama suka tafi. 
                               Rahma ta kwanta tana danna wayarta ta shiga wajan message ta turama Acp saƙo kamar haka _“Aslm My Qalbi yau da ka rasani, naje raka su Samira bakin titi zasu tafi gida, motar sarkin garin nan tayi ciki dani, wani ɗansa maras imani kuma yazo yana min faɗa,😥 amman iyayansa masu dattaku. Yanzu haka ina hospital.😭_   Haka ta tura masa saƙon, ta ajiye wayar tana rufe idanunta sbd baccin da takeji. 
                   Zaune yake cikin office ɗinsa, yana haɗa wasu files, yana amsa waya.  Bayan ya gama amsa wayar ya miƙe yana ɗaukar ɗayar wayar, ba tare da ya dubaba ya sanya su aljihunsa, sam bai lura da danjar wayar ke nunawa ba, alamar saƙo ya shigo, makullaun mota ya ɗauka, yana manna glass kan fuskarshi, ya nufi ƙofar fitowa.  Yana buɗe ƙofar suka shiga sara masa. Duk inda ya wuce gaishesa auke, tamkar shine commissioner ɗin.   Seat ɗin baya aka buɗe masa ya shiga ya zauna dan agajiye yake yana buƙatar a tuƙashi.   Bayan an buɗe masu gate sun fito direban yake tambayarsa“Sir ina muka nufa?”Safuwan ya lumshe fitinannun idanunsa yana shafa sajansa cikin daddaɗar muryashi yace.    
               “Gida” 
Cikin girmamawa ya amsa da“Ok Sir.” ya harba motar kan titi suka nufi gida.    Ruwaida na kwance saman 3seater kanta saman cinyar Mummy tana mata susa. Idanunta ta lumshe tanajin daɗin susar, saidai zuciyarta A cinkushe take.. Sam bata jin daɗin yanda ta ɓatawa yayanta rai, saidai itama tayi fushi dashi.. Sbd yanda yafirgitata da tsawarsa.   Muskutawa tayi tana cinno ɗan ƙaramin bakinta gaba, tana musum² da baki kamar wacce zatayi mgn.
            Su Widad sunata hira biki, itada islam Nadiya Ummu na mata kitson ƴan mali, yayin da Lailah kema ummuh tsifa.  Fu'ad yace“Mummy da gaske Aunty Ruwaida haka zata zauna baza tayi adoba....?”Mummy tace“Shiru da wani ƙaramin bakinka irin na Ruwaida, maza kuje ku ɗauro alwala lkcn sallah ya kusa.” Dariya su islam sukayi, suna faɗin“Fu'ad me bakin mata.” ummuh tace“Kubar faɗa masa, ko na faɗawa Abbaye.”  Ruwaida ta ɗago da kanta ta kalli Mummy tayi murmushi tana tutturo ɗan ƙaramin bakin nata gaba.  Musaddiq ne suka shigo shida Acp.  Kallonsu yayi yana faɗin“Kuko uban me kuke jira kunaji ana ƙiran salla baza kuyi alwala ba? “Ko nan gidan silima ne da zaku cika mu da surutu....?”  Ai kafin ya rufe baki sun miƙe agauje sun nufi bedroom.  Ummuh tace“Yauwa jami'inmu saitasu sun ishemu daman da fitina.” da yaren fulatancin mali ta masa mgn, dake kowa yaran gidan sunaji, hatta Mummy ta iya sosai. Acp yace“Ummuh kuma ku tashi lkcn sallah ya gabato fa.” miƙewa sukayi suna murmushi suka nufi ɗakin da aka saukesu.   Ruwaida jin murya Abbaye ba ƙaramin daɗi abin ya mata ba. Ahankali ta miƙe zaune bata ko yarda ta kalli gefensa ba, ta tamƙe fuska tam ta nufi bedroom ɗinsu tana takunta anutse ko ina na jikinta motsawa yake kamar tarwaɗa. Daman riga da siket ne na atamfa  Ja ce me ratsin fari ɗinkin ya kamata kaɗan sai mayafi sharan² bayada kauri, ta yafa.  Mummy tace “My dota idan kinyi sallar kiyi fa karatu kinji.” juyowa Ruwaida tayi tana sakin murmushi ta jinjinawa Mummy kanta, alamar to ta juya ta tafi.   Abbaye baki ya taɓe yana ɗauke idanunsa daga gareta, ya zura hannunsa cikin aljihu.  Mummy tace“Ƴar gidanka fushi take ma fa, dan bata ko tambaya da kai ba.” ta faɗa tana miƙewa domin ɗauro alwala.  Abbaye ya taɓe baki yana takunsa na isassun maza ya nufi part ɗinsa, ya ɗauro alwal dan Musaddiq ya tafi bai tsayaba, ganin lokaci na ƙurewa.  Mummy murmushi tayi tace“Kunfi kusa.” ta nufi bedroom ɗinta.  Acp agaggauce ya cire uniform ɗinsa, ya shiga bathroom.  Bai jimaba ya fito ya zura jallabi ruwan toka sabuwa ya fesa turare.  Ya juya yana sauri zai fita, yaji wayarsa na ringing.  Tsaki yaja ya juyo yana dubawa yaga Nadeer wayar ya ɗauka, ya  sakata A selint ya zura aljihunsa ya fice, zuwa masallaci.... *Yasin ba wani editing🥴*

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now