*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
_*💃🏻Tsokana Com.🤪 MUNA GEFE MUNA KALLON MANYAN MANYAN KU.........😂 💃🏻ALEEYA ME WAINA TAYI KWANTAI TANA ARAHA💃🏻🤣🤪🤪🤪*_
_*Ba Editing🧐*_
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 24*
Bugu biyu Aunty Ni'imah ta ɗaga ƙiran haɗi da sallama. Abbah yace“Sai yanzu kuka shigo Jalingo ne? Allah yasa lafiya ce ta ɓoye ki, shirun yayi yawa muna ƙira bama samunku?” daga can Aunty Ni'imah tace“ Haba bari kadai ɗan uwa, wallahi network ɗinmu ya ɗauke da safe lkcn da zamu fito, kawai sai ga tsautsayi auta Bahijjah garin ƙiriniyarta kasanta kamar wata ƴar beby gata dai shekaru 14 wallahi wai akitchen tana soyama yayanta dambun naman da zata kawo masa, ta ƙone bakaga ba yadda hannunta yayi, kaji abinda ya hanamu zauwa, gashi bamuda network bare na faɗama, sai yanzu ne ya dawo.... nace bazan bacci ba, bari na ƙiraku ya jikin yarona? Abbah yace. “Subahanallah garin ya ta ƙone ɗiyar kirki? To dan Allah karku taho ki tsaya ki kula da ita ku bari sai biki, Abbana yaji sauƙi sosai fa yanzu haka muna gida Musaddiq ne yake wajansa, shida Nadeer abokinsa.” Aunty Ni'imatu tace“Masha Allah naji daɗi yarona yaji sauƙi, insha Allah satinan da zaran taji sauƙi zamu taho, tinda bikin ya kusa. Abbha yace“Ok Allah bata lafiya ina my Sadiq ne? Aunty tace“Yana nan aiki ya sha masa kai ai tare zamu zo dashi.
Nan suka sha hira ta ƴan uwa sukayi sallama da juna. Abbah ya saka wayar a chaji ya rungume Mummy wacce take sharara baccinta, ya tofesu da Addu'a ya ja masu blanket, asubah ta gari.
Washegari Ruwaida fafur taƙi taje wajan Safuwan ta dai ƙirasa tana masa gunguninta haɗi da shagwaɓa, bayan dogon message da ta tura amsa, na fatan ya samu lafiya. Ɓangaran Acp yau yaji kewar Ruwaida sosai da bata zoba amma haka ya basar. Har tsawon kwana 5 Ruwaida taƙi zuwa hospital wajan Acp, ta kwance akan batada lfy, dole su Mummy suke bata kulawa taƙi aje asibiti, Abbah ya ƙirawo Dr Hanna take kulawa da ita, tace yarinyar damuwace ta mata yawa, abinda yasa suka ƙara sakata jikinsu kenan. Acp yayi kewarta sosai dauriya kawai yake, amma ta waya sunama juna text, wanda ya hadasa masu shaƙuwa sosai, shagwaɓarta ta kusa zauta Acp, masha Allah yayi sauƙi sosai ya murje yayi ƙara kyau, maƙiyan Acp babu hanyar da basu biba, acikin hospital dan kawar da Acp amman ina yanada mugun matakan tsaro atare dashi, yayin da gobe Dr yace zai sallami Acp sbd ya matsu ya koma kan aikinsa, yaji sauki sosai dan yau da kansa ya kai Alh Sale kotu. Wanda ayaune kotu ta yankewa Alh Sale hukuncin kisa ta hanyar rataya, yayin da gwamma giɗaɗo yayi tsaye wajan bincikenta, kuma tabbas Dsp Sameer ya gano batada hannu akan aika² da Sale yake, wanda hakan yasa kotu ta gamsu da shedun da lauwer gwamnati me kare wacce ake tuhuma, tanada hannu ya kawo, dan haka kotu ta wanke gwamma sbd an tabbatar batada hannu, aikuwa daga nan gwamma bata koma gidanta ba, tace tabar karuwanci har abadan , haka bata son gidanma dan ta sare kasheta za'ayi, tama giɗaɗo godiya sosai tare da masa nasiha ya tubarwa zuwa ga Allah. Shine ya sata amotar garinsu, ta tafi tana ƙara godema Allah da ba'a kasheta ta samu ta tuba tunda sauranta shekaru 33 tasan bazata rasa mijin aureba.
Rahma kullun sai tazo sun ƙara shaƙuwa da Acp dan yana jin daɗin yanda take kula dashi. Nazifa sau 3 tazo ganin Safuwan sonsa take kamar tayi hauka. Ruwaida na kwance bayan tayi sallar azuhur, tana bacci mai daɗin gaske wanda rabi mafarkin Acp ne, suna zaune awani tafkeken lambu mai cike da ciyayi tsanwa shar, yana zaune cikin fararan kaya masu kyau da laushi wanda suka ƙara baiyyana kyan surasa, ta ɗare bayansa ta zagaye hannayenta ruwan cikinsa ta saddo da kanta tana leƙen fuskarshi, tana murmushi, shi kuma yana faɗin“My life zaki karyani fa, My Angel zo kiga wani abu. Ya faɗa yana sanya tattausan hannunsa ya birkito da ita, ta dawo gabansa ya ɗorata kan cinyarsa, ta saki kukan shagwaɓa cikin wata irin amon zazzaƙar muryata tace *“Hayatie!* goyo nake so ni goyo nake so.....” Katseta yayi yana murmushi yace“Ok to shiru My Angel oya kiss me se na goyaki, buɗe idanunki kigani.” Ya faɗa yana sake manneta ƙirjinsa, yana sunsuna wuyanta, taji dumin harshensa yana tsotsar fatar wuyanta,yana shafa bayanta hannunsa ɗaya saman bom_bom ɗinta yana shafawa, tana mutsul² tana shasheƙar kukan sangarta, ta ƙara maƙaleshi. Cike da shaƙin ƙaunarsa ta buɗe dara_daran idanunta ta sauke su akan Acp, abin mamaki kawai sai taga....... Amugun tsorace ta fizge jikinta, tana faɗin “Ina Hayatie na?? Damƙota yayi yana murmushi yace“Kinada wani Hayatie bayan nine Bebyna? Nine fa...... Wani razanannan ihu ta saki tana ƙoƙarin ƙwace jikinta tana kuka tana girgiza kai.
Islam da Mummy da Taslim ne suka shigo da gudu suna faɗin Ruwaida! Lfy. Ihuuun kawai take idanunta arufe. Mummy ta zauna bakin gadon ta kamota tana girgizata, ta buɗe idanun nata ta jiƙe da gumi ta faɗa jikin Mummy ta maƙalƙaleta ta fashe da kuka ba bakin mgn ko akwai ma me zatace, cikin ranta ta fara karanto Addu'a kar Allah yasa abinda tagani amafarki ya faru da gaske, duk tasan shartin mafarkine, amman tana neman tsarin hakan. Mummy tace“Haba Ruwaida idan mafarki kikayi Addu'a zakiyi ba ihu ba, to ya isa yi shiru kinji. Kai Ruwaida ta ɗaga tana sauke ajiyar zuciya ta ƙara shigewa jikin Mummy tanajin son taje taga halin da Abbaye yake ciki. Taslim tace“Sannu Ruwaida ya jikin naki? Ruwaida dai tayi luf abinta jikin Mummy. Islam tace ko ki shirya muje wajan Ya Safuwan ne? Ruwaida ta ɗaga kanta da sauri idanunta arufe. Mummy tayi murmushi ta ƙara rungumeta tana shafa lallausan gashin kanta, tace“Ok kubari ayi sallar la'asar rana tayi sanyi sai ku tafi, gobe ake sakosa ai. Taslim tace“Acp rigima kana cikin jinya kaje shari'a. Mummy tana shafa kan Ruwaida tace“Eh naji daɗin hanka ƙarshan halewa ƙasa gashi yajama kansa asara rai, ai abinda mutum ya shuka shine zai girma me kyau ko akasin hakan, meye ribasa ayau, sana'ar tsafi. Haka sukayi ta hira su Ruwaida na manne jikin Mummy, daga baya suka dawo falo da niyar bayan la'asar islam da Widaad da Ruwaida zasu hospital. Misalin ƙarfe 4:30 pm na yamma innah nata aikace-aikacenta, Zainab na gyara masu kayan miyar girki suna taɓa hira. Innah tace“Rahma ki daure ki fito waje kisha iska mana, wai kinsha rubutun da malam ya miki ne? Ai tinda yau naga ba'aje asibiti ba, nasan ciwon ya tsananta, Zainabu tambayo mani ita tasha rubutun.
Zainab tace“Eh innah tasha kuma tasha wancan maganin da naga Ya Acp ya siyo mata. Ta faɗa tana nufar ɗakin nasu. Innah tace“Allah bata lfy insha Allah zata rabu da ciwon kwana nawa ya rage. Rahma na kwance saman ƴar katifarsu, babu lfy marata na mata ciwo, sai juyi take haka daman take fama idan tana period, tanajin innarta na mgn ta buɗe idanunta, batace kome ba sbd baji zatayi ba, tinda suna tsakar gida. Wayarta ce ta ɗauki ringing, ta kalli gefen da wayar take taga Acp ne ke ƙiranta.
Cikin dauriya ta beƙa hannunta, ta dauki wayar tana ciza lips ɗinta, tai picking ɗin call ɗinsa ta manna wayar kunneta, cikin sanyin muraya tace“Assalamu alaikum ya Masoyina, abin alfaharina ya ƙarfin jikin naka?” ta faɗa cikin jirumta. Acp daga can da yake zaune bakin gado, yana sanye da 3 quarter sai singleti yayi kyau sosai sai baza kamshi yake bazaka ce mai jinya bane, dan sosao ya ƙara kyau ga lfy da ya samu sosai, sai ka kalli wajan harbin ne ma zaka gane shine fa majinyacin. Ya ɗan muskuta yana shafa kyakyawan sajan fuskarshi zuwa sumar kansa, yace. “My dear yau najiki shiru ba ƙira? Kuma...... Yaja dogon numfashi yana lumshe fitinannun fararen manyan idanunsa, sbd jin mgnr tai masa tsayi, yana shafa yalwatacciyar sumar kansa.
Rahma taji daɗin yadda Acp ya damu da ita sosai yanzu, ta cije ta ƙara kashe murya tace“My Acp nawan! Bari na ƙarasa maka, kuma baki ƙirani ba, kiji lafiyata, baki zoba, Allah yasa dai kina lafiya my dear? Ta ƙarashe tana murmushin ƙarfin hali, sbd sosai marata ke mata ciwo. Taci gaba da cewa “To My Acp nawan banajin daɗine, kaina yake ciwo amman naji sauƙi sosai gobe zanzo me kakeso na kawo maka nawan?” ta tambayesa tana murmushin dauriya.
Acp ya buɗe kyawawan manyan idanunsa yana mijin duk duniya yafi kowa dace da mata ta gari, Rahma tasan darajarsa, haka tasan duk mgnr da idan yaso ya idar bai gama tasan ƙarshenta tsaf zata fassara masa. Cikin daddaɗar muryasa cike da kulawa yace. “Subahanallah my dear sannu, kinsha magani? Oya ki shirya zan turo yanzu a kaiki hospital. Ya faɗa yana shafa sajan fuskarsa, cike da tausayin Rahma. Murmushi tayi tace ogana karka damu wallahi jin muryaka ya ƙaramin lafiya sosai, fatan kana lafiya ya kakejin jikin naka? Ta ƙarashe mgnr tana kallon Zainab da tayi tsaye bakin ƙofar ɗakin tana kallonta, jin yanda ta zage tana hira. Zainab tace“Ya Acp barka da yamma ya ƙarfin jikin? Allah ƙara lfy. Ta faɗa tana juyawa ta fice. Daga can Acp yace“My zee ykk naji sauƙi pls ki shirya zan turo ki raka my dear hospital..... Yaja numfashi yaji gaba da cewa“Adubamin lafiyarta.
Rahma tace“Nawan ta fa tafiyarta wlh na warke gobe zanzo da safe na ganka. Acp yace“No bana son musu maza ki shirya za'azo ɗaukarku. Dole Rahma ta amsa da“Ok My Acp nawan. Murmushi yay ya tsinke ƙiran. Rahma ta runtse idanunta cike da shaukin Abbaye, tanajin ƙaunarsa na ƙara gudanya adukan jini da tsokarta, haka taji cikin kaso 100 na ciwonta kaso 70 sun kau. Tashi tayi ta shirya cikin gaggawa abaya baƙa ta saka, mai kyau ta fesa turare ta yafa mayafin abayar ta fito waje. Innah na girkinta taga Rahma tsaf cikin shiri, ta tafa hannunta tace.
“Me zan gani Rahma ina zaki bakida lfy, daga yin waya da mutum? Rahma ta duƙa gaban innarta ta dafa cinyarta tana ciza laɓɓanta, ta kalli Zainab tace“Maza ki shirya yace dole sai munje kin rakani asibiti an dubani. Zainab ta miƙe tace“To anty bari na shirya. Rahma tace“Innata kin yarda dani ɗiyarki bazan miki ƙarya ba? Inna tace “Ai indai akan Police ɗin mijinki ne kin koya..... Rahma ta katseta tace“ Allah gsky zan faɗa miki innata. Ta faɗa tana rungume innar tata, nan ta faɗa mata iya abinda ta faɗama Acp cewar ciwon kai take, da yadda ya matsa mata zai turo akaita hospital adubata. Inna taji daɗin yanda ya damu da ƴar tata tace“To naji ba naƙi ba ƙira babanki ki faɗa masa kinsan halin malam. Rahma tace“Toh innata.
Nazeefa ce take ta kai koma a tsakiyar ɗakinta, sanye take da wani ɗan guntin wando iya cinyarta, sai vest wacce ta fito mata da kyawun ƴan matasan breast ɗinta, sbd yanda ta matsesu, hakan wandon ya mata kyau fararan cinyoyinta duk a waje, masha Allah mazaunanta sai motsawa suke, ta saki gashin kanta har kafaɗarta. Dunƙule hannayenta tayi tana dukan junansu, sai kai komo take atsakiyar ɗakin. Cikin zafin zuciya tace“Rahma na tsaneki kece kika hanani cikar burina, tabbas da bake inaji ajikina Acp Safuwan Ishaq Sawaba zai iya saurarata, alamu sun nuna hakan, ƙarya kike ƴae talakawa, Safwan nawane!! Dna haka sai na rabaku...!! Ta faɗa cikin zallar ɓacin rai, ta nufi gaban dreesing mirror ta ƙarema kanta kallo tace“Me na rasa na ɗiya mace aduniya? Ta tambayi kanta tana ƙarema kanta kallo.
Kamar an tsikareta ta nufi gadonta wata lafiyayar doguwar riga naga ta dauka ta shadda pink colour ta saka ajikinta ba tare da ta cire vest ɗinba, har wandon, cikin sauri ta shirya ta ɗauki makullan motarta ta fice tabar gidan.
Acp acan kuwa hospital ya ƙira number Sani direban gidansu, bai ƙira yaransa ba, bugu ɗaya ya ɗaga nan ya faɗa masa yaje gidansu matar da zai aura ya ɗaukosu ya kasu nan hospital zataga likita. Nan ya amsa cikin girmamawa, ya ɗauki mota ya nufi gidansu Rahma. Yana zuwa lokacin ta tura Zainab ta ƙirasa yana ƙofa wajan almajiransa, ta faɗa masa ya amince yana mata Addu'ar samun sauƙi, Sani na zuwa ya ƙira Acp yazo shi kuma ya ƙira Rahma ya faɗa mata, suka fito suka shiga motar bayan sun gaisa yaja motar ya nufi *Danny's wellness clinic.*
_Ba Mamaki idan comments yamin gobe ma kujini insha Allah😄._
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.