Chapter 8

432 20 5
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 8*

A hankali yace"Mummy yarinyar  bata mgn, amman ta iya  takura." ya faɗi yana kwantowa jikin Mummy.       Mummy tace.
                 "To mudai bamu iya zancan kurame ba, yanzu dai ka  sake tambayarta ina ne garinsu..." Abbah yace"Eh haka nake son ji." Musaddiq yace"Na iya mgnr kurame ni." Widaad ta ƙumshe dariyarta ta miƙe ta nufi wajansu Islam ɗin.        Safuwan ya kalli Musaddiq yace.           "Ok bro." bai sake mgn ba, ya mike ya nufi wajan Abbah ya zauna, ya jin gina da jikinsa.       Ruwaida sosai taci coscos ɗin dan ma'abuciyar son coscos ce.  Spoon ɗin ta ajiye ta ɗauki cup tasha fruit ɗin sosai, ta kalli islam tana mata kwatancan fitsari takeji.         Islam tace"Wlh ban ganeba me kike nufi ba?" Ruwaida kallon hannun islam tayi taga ba waya.  Widaad tace" Wlh nima ban ganeba." Ruwaida ta kalleta ta kalli islam ba waya a hannunsu bare ta gane, kawai sai ta miƙe ta kamo hannun islam suka nufo parlon Widaad na biye dasu.
              Abbaye ya kallesu ganin zasu wuce, a hankali yace"Ke!! Zo nan." Ruwaida ta waigo ta kalleshi tana matsar ƙwalla ta saki hannun islam ɗin ta tako a hankali ta iso dab dashi ta zauna ƙasa saman caepet kusa da ƙafafunsa, ta sadda kanta.  Abbah yace"Ɗiyata kina son wani abune...?" Ruwaida da sauri ta ɗaga kanta, alamar "Eh"  Abbaye ya ɗan sunkuyo da kansa dab da fuskarta yace"Ok meye?" kwatance ta fara masa sai taji kunya ta zare wayarsa dake hannunsa, ta cikin sa'a a buɗe, kawai sai ta fara rubuta masa.     *"Yayana mai kirki inajin fitsari ne😿.* Ta beƙa masa.  Abbaye ya karanta, ya ɗago ya galla mata harara, kanta ta sadda tana wasa da yatsotsin hannunta.
                  Ya rubuta mata *"Idan kika sake faɗamin irin wannan sai na mareki ni kike so na kaiki toilet ɗin ko na maki madaɗin ke? Oya maza tashi kije kiyi ki dawo zaki amsamin tambayoyi, kujita ƴar baƙa."*  bata wayar yayi ta amsa ta karanta.  Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba a ɓoye, yanda ba wanda zai lura.       Itama rubuta masa tayi.
*"Yayana ɗan fari mai kirki to kayi haƙuri bazan kuma ba "* yana amsar wayar ta miƙe a ladabce ta kama hannun islam sukayi bedroom.
               Suna zuwa ta shiga bathroom tayi fitsari ta fito. Widaad tace"Ina zaki?" ta nuna mata Yayanta.
          Murmushi tayi tace"Yanzu dai na gano jeki." kai Ruwaida ta ɗaga ta fice.             Yanzu ma zaune take  kusan ƙafafunsa ƙasa kan carpet dab da ƙafar Abbaye tana satar kallonsa.
Musaddiq yace"Me sunanki?"  da sauri ta ɗago ta kalleshi, ta maida kanta.          Mummy da Abbah atare sukace" Abbaye ka mata tambayoyin da muke son ji mana."  Safuwan ya jinjina kai, ya shiga mata rubutu.
                             ''' "Meye sunanki?  Ina ne garinku? Ya akayi kika fito, bayan kince auranki ya kusa, bakya son mijin ne ko sha'awar yawon danɗi kikeyi?"''', wayar ya bata, ta amsa ta karanta, hawaye ya fara zuba daga idanunta, ta rubuta masa.             *"Sunana Ruwaida! Wallahi tsakanina da Allah, yaya ɗan fari mai kirki nima ban saniba kawai na fitane, ni yanzu ko garin namu wallahi na manta sunansa, ku yarda dani".😥*

Beƙa masa wayar tayi tana shasheƙar kuka, ya amsa ya karanta.  Ya masu Abbah bayani.     Abbah yace"Tashin hankali watakon an fito da itane sannan an rufe mata baki kar ta faɗi inda take bare har wani yayi yunƙurin mayar da ita, kokuma can daman ta jima bakin a rufe, fitowar ce sai yanzu, insha Allah zamu riƙeta amana, da kuma dagewa wajan tayata Addu'a da izinin Allah sai ta fita daga wannan ƙullin da aka mata, zata dawo daidai, ki dage da karatun Alqura'ani kinji ɗiyata Ruwaida ko...?"  kanta ta ɗaga.   Mummy tace"Da izinin Allah wanda suka miki wannan ƙullin abin sai yadawo kansu."
        Musaddiq yace"To Abbah yanzu bazaku aurar da itaba wa wani, dole sai ta warke ta koma gidansu, a bata wancan mijin?"   Abbah yace"Ina ka taɓa jin haka kawai shikenan yarinya ba lafiya sai na aurar da ita, ai ko iyayanta a yanzu bazasu aurama wancan ba, dole zasu jira suga abinda Allah yayi."
Abbaye dai baice kome ba, ya kalli Ruwaida yace"Oya je ki kwanta." da saurinta ta ɗago bata yarda ta kalli ƙwayar idonshi ba, ta ɗaga hannunta biyu tana masu godiya.
                 Abbah yace"Ba kome, daga gobe zaku fara zuwa islamiyya dasu Islam haka nan ma kina karatun tinda idan an koya miki zaki iya bita a cikin ranki ko?" cikin murna ta jinjina kanta.   Abbaye ya ɗan kalleta suka haɗa ido, ta masa murmushi, hararata yay ta ɗan turo baki gaba ta sadda kanta.
             Mummy tace"Abbaye me tayi maka kuma, yanzu dai ka sayo mata waya ko hira ta dingayi da ƴan gidan ta wayar, nima zan shiga kasuwa a kwaso mata kayan sawa da uniform ɗin islamiyya su takalma hijabai da dai sauransu." Kai ya jinjina.  Musaddiq yace"Ko muje da ita sai ta zabi kome da kanta."  Abbah yace"Musaddiq ka kama kanka wlh na baka sati ɗaya idan baka fito da mata zan baka Aneesa." Acp ya miƙe yana kallon Musaddiq yace"Abbah sun dace."yana faɗin haka ya rankwafa yay ma Abbah kiss ya koma wajan Mummy yamata sallama yace"bro good night." Ruwaida ta waigo ta kalleshi taga bai ko kalletaba, ta miƙe ta nufi bedroom.    Musaddiq ya sosa kai yace.
       Abbah ko dai ku kuka saka take addabata da ƙira, ɗazu ma ta shigo fa." Abbah yay murmushi baice kome, taya zai saka Aneesa ta ƙirasa.  
                Ruwaida hijab ta cire ta haye saman bed tayi kwanciyarta tanajin daɗi zatayi waya sai suna fira da yayanta mai kirki  kullum.  Tin tanajin hirasu Islam akan yayansu Musaddiq, wai ko da gaske Aneesa za'a bashi ɗiyar kawunsu, Hamza har bacci mai cike da nutsuwa ya saceta.    Safuwan yana zuwa yaci gaba da aikinsa a cikin laptop, Musaddiq ya kawo masa hira, sune basu nemi gun kwanciya ba sai karfe ɗaya na dare.

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now