*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
'''ALHAMDULILLAH ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI NA GODE MUKU, SOSAI BISA ADDU'O'INKU GARENI, MASU ƘIRANA DA MASU TURAMIN SAƘONNI WALLAHI WASUN BANSAN INA SUKA SAMU LABARI BA, NAGODE SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCI, ALHMDLLH JIKINA YAYI SAUƘI, DUK DA BA WAI NA GAMA WAREWABA NE, AMMAN YANDAN MASOYAN RUWAIDAH KE ƘIRANA, WLH KUN CANCANCI NAI MAKU TYPING KO BA YAWA KU LASA.😺😸😸'''
'''Zan So Kar Ayi Babu ke!! A Wannan Labarin'''
*👉🏻TUN RAN GINI RAN ZANE Wai Wai Wai Ko daga Jin Sunan Hummmm Akwai Abubuwa Cike Da Wannan Tafiya. To Real masoya, Kar Na Cikaku Da Surutu, Albishirinku Masoyan littafan Real Ladingo, Nasan Dai Kunsan littatafanta, Ba Sai Na Tsaya Nayi Maku Dogon Sharhi Ba.....So Dan Haka, Yanzu Ma Ina Ɗauke Da Sabon Labari Shima Salon Na Daban Ne. Karda Kuyi Rauni Ko Gazawa Wajan Siyan Wannan Book Mai Suna Tun Ran Gini Ran Zane... Nasan Wasunku Sun fara karanta Labarin Banyi Nisaba Na Tsayar Dashi, To Na canza Salon Labarin Yanda Zai Ƙara Tafiyar Da Zuciyar Mai Karatu, Akwai Abubuwa Masu Tarin Yawa cikin Labarin Na Daɗi Da Akasin Hakan, Sannan Akwai Rikitacciyar Soyayya Mai Zafin Gaske Tare Da Sadaukarwa Akwai fa Badaƙala Akwai Akwai Akwai....Kai Kundai San Ladingo So Karku ji Shayin Siyan Wannan Littafi Akan Nera N200 Kacal Ga Mutanan mu Na Niger* *zaku Biya*
*300F Ne Kacal. Insha Allah 22 ga Watan nan na October Zan fara baku Free Page, 💃🏻 Ku Garzayo Ku Kwashi Rabonku, Zaku Fadakartu, Zaku Kuma Nishaɗantu, Da Wata Sansanyar Soyayya. Ga Masu Buƙata Ku Tuntuɓeni Ta Wannan Number👉🏻22796515805. Wannan Salo Shima Na Dabam Ne...🤙🏻*~Dubin Gaisuwa Da Fatan Alheri~ '''zuwa Ga masoyan Ruwaida na nesa da na kusa Ban ware kowaba...😍😍😍'''
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 16*
Wani irin kukan kura mai haɗe da kwance-kwance, Safuwan yama Alhaji Sale, duk da baya ganin sa sosai, ya saita bindigarsa, ya hankaɗe Samir yay ƙasa, cikin iya ƙwarewar iya harbi da jarumtarsa ya danne sharan kafaɗarsa wajan da Sale ya harbeshi, jini na zuba, ya harbi Sale a kafaɗa da ƙafa, cikin nasara.
Ihuuu Sale ya saki bindigar hannunsa na faɗuwa ƙasa, yayi kukan kura ya wawuro wannan ƙahon tsafin nasa. Abbaye ya masa wata wawar ƙafa sai gashi a ƙasa wanwar, ya taka cikinsa da ƙafa, ya ɗora ƙafarsa wajan harbin ya taka da karfin gaske, sai ga sale na fitsari a kwance, yana sakin wani irin ihun azaba, ya ɗora ƙafarsa, a kan wuyansa yana huci. Samir ya riƙeshi yana faɗin. “Oga jini na fiti jikinka, sosai ka barni da jakin nan.” ya faɗa yana riƙe da Acp. Abbaye yace.
“Sakeni zan iya tsayuwa.” daidai lokacin rundunar ƴan sandar suka shigo, sun haske ɗakin da lampe ɗinsu mai masifar haske. Ganin Acp a haka hankalinsu ya tashi, saura sukyi kansa, cikin girmamawa, suka kamashi, yaƙi da kansa cikin jarumta ya ƙarasa sumar da Sale cikin irin muguntarsa launi-launi. Sai da yaga baya motsi ya basu umarnin ɗaukansa, da ɗaukar gawar ƴar libah. Suna riƙe dashi ya rinƙa bin kowace kusurwar ɗaki yana dubawa, babu wani ko wata gawa sai ta ƴar liba, sai kayan tsafinsa, da wani akwati maras misaltuwa, a a girma ana buɗeahi kuɗi suka rinƙa ambaliya, haka aka kwashesu duka aka zuba a mota, aka nufi police station.
Samir dakyat ya sha kan Acp suka nufi hospital, dashi. Suna zuwa aka shiga bashi temakon gaggawa sabida irin jinin da ya zubar, amman sabida jarumtarsa, saida ya gama binkitar gidan Sale, kafin su nufi asibitin. Yaci azaba wajan ciro da bulet ɗin da ɗinkin da aka masa, amman ko fuska ya kasa nunawa, Acp ba ƙaramin jarumi bane, gashi yama Samir ƙwaƙwaran kashe kar ya kuskura ya faɗawa ƴan gidansu. Dr ne yace “ya rabu dashi shine zai ƙira su Abbah ɗin, ya za'ayi a barshi hospital shi ɗaya, gashi ma sai an masa ƙarin jini, dole sai ƴan gidansu sunzo, an ɗebi jininsu an gwada an saka masa......ana gama masa ɗinkin Dr Junaid ya haɗa allurai yay masa ya ɗaura masa ƙarin ruwa ya saka alluran bacci 4 minutes yay bacci. Nan ya ƙira Abbah lokacin yana can wajan, Alhaji Dalhatu, amininsa suna wani lissafi, yaga ƙiran Dr Junaid jikinsa na rawa ya ɗaga tare da sallama yace.
“Dr barka da warhaka lafiya kuwa?” Dr Junaid yace“Yallaɓai barka daman Acp ne ya samu ɗan rauni ta hanyar kamo wani mugu har aka harbeshi, yanzu haka an ciro harsashin guda a kafaɗarshi yana buƙatar ƙarin jini...” Abbah ya miƙe, jikinsa na rawa, yana faɗin“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! “Ina zuwa yanzu.” ya faɗi yana fita aguje, Dalhatu ya bishi yana faɗin.
“Sawaba lafiya wai?” Abbah bai saurareshi ba ya nufi wajan motarsa, kafin ya shigo har direba yaja motar sun tafi, shima direbansa ya buɗesa masa mota yashiga yaja sƴka bi bayansa.Canko police statoin bayan sun gama bincikar gawar, ƴar libah akaje gidan karuwan ana bincikar iyayanta, ba wanda yasan asalin garinsu, wani saurayinta yayi tsaye yace abashi gawar, bayan dogon binkice suka bashi gawar ya tara abokanan ya samo wasu tsafi biyu suka mata wanka, haka aka tarkatata bayan an tambaya tanayin salla? Akace tanayi tabbas haka dai aka mata salla ƴan tsurarin mutane haɗe da ƴan sanda biyu wanda suka tsaya akayi kome a gabansu,umarnin Dsp Samir ne aka kaita gidantana gaskiya.
Wannan mutuwar tayi mugun shigar karuwan gidan gwamma wanda ta saka dayawa da masu yawon karuwanci, sun tsorata dayawansu sun saduda sun fara shurin barin gari wanda kuwa sukayi nisa basajin ƙira. Can kuwa police statiin Gwamma taci ubanta azaba suke mata launi-launi suna tambayarta tin yaushe suke wannan aikin itada Sale suna kashe ƴaƴan jama'a? Rantsuwa gwamma take bata ma taɓa sanin yana yanka mutane ba, amman sam basu sauraretaba, cikin ƙanƙanin lokaci, magajiya anji jiki, amman taƙi amsa laifin da bata san dashiba. Alhj Sale kuwa, bayan Samir ya kwarara masa ruwan sanyi ya farka daga sumar da Acp ya sakashi, suka dinga cin ubansa, suna, tambayarsa shegen yaƙi amsawa, tin yaushe yake harakar mafiya. Dsp yace su barshi zai amsa...Ruwaida har yanzu bacci take tana ta famar sauke ajiyar zuciya. Su islam kuwa sun jima ɓangaran ummani kakarsu a parlo, sunata hirasu sunaɓtsikarta itako tan atsokanar Rahma ta mata kwacan miji, sunata dariya tana tambayar Ruwaida sukace tayi fushi yau da kowa sunyi faɗa da Abbye ya mareta” Aikuwa ummani tasha faɗa kamar bakinta zai cire ta ƙirasa waya na ringing ba'a ɗagaba. Sun jima sosai a ɓangaran nata har Bappa ya shigo suna tsokanarsa, kafin su koma ɓangaransu Mummy.
Ƴanzu ma suna parlon suna hirasu. Raham duk ta ƙosa Abbaye yazo so take ta tafi gida, gashi sam batajin daɗin zuciyarta akan abinda Ruwaida ta mata.
Muskutawa tayi kanta ƙasa a sadde, Widaad na kusanta tace.
“Aunty halan kin gaji ne kinaso ki tafi?” Rahma tayi murmushi tace“A'a Widaad.” Mummy tace“ Wlh shima Abbaye ya jima, tashi kawai islam ta kaiki gida, amman kiyi driving a sannu.” Taslim tace“ Ai nima tafiya zanyi ta tashi sai na ajiyeta, Mummy bana son anaba, yaran nan masu rawar kai mota.” Islam tace“ Kai anty kimin buƙulu.” Rahma tayi murmushi kanta aƙasa. Mummy ta miƙe tana faɗi“Wai Ruwaida baccin ne take har yanzu? ” Ki fushi taje da Yayanta? Sunfi kusa.”ta ƙarashe maganar tana nufar hanyar bedroom ɗinta. Aneesa tace“Yau Ya Abbaye yayi laifi sosai wa ƴar gidansa fa.”Taslim tayi murmushi tana miƙewa tace“Bari na leƙota na zugata tazo muje gidana.”Ta faɗa tana nufar ɗakin na ƴan matan. Har yanzu baccinta take Ac na ratsata ta naɗe cikin blanket.
Taslim ta shafi kyakyawr fuskarta, ta cinno ɗan ƙaramin bakinta gaba, tayi murmushi ta fito ita dai tan son Ruwaida. Mummy turaruka da sabulu dasu mai masu sanyin ƙamshi ta haɗoma Rahma, ta bata ƙin amsa tayi dakyat ta amsa tana godiya Aneesa na tsokanarta tamkar ita ba suruka bace agidan. Sun gama sallama zasu tafi, Mummy na riƙe da hannun Ihsan suna tafiya, Fu'ad ya kafa rigima se yabi Taslim gidanta.
Suna zuwa bakin ƙofar parlo ta rungume Rahma tace“Allah ya miki albarka mun gode, karki damu zanma rigimamme magana, nice na saka aka kaiki gida kar malam da inna suga kin daɗe.” ta amsa da. “To Mummy Allah ya ƙara girma da lfy, a gaishe da mai jiki, idan ta tashi.” Fu'ad yace“Mummy zanje gidan anty.”Mummy ta kama hannunsa tace“A'a wlh zan haɗaka Acp.”
Taslim tace“ Mummy don Allah kibarshi muje tinda weekend ne pls.”Mummy tace “Ai kam ya na iya da kwawarsa kuje ɗin...” Wayarta dake hannunta ce ta ɗauki ringing ita ta katse mata hira, ganin Abbah ne yasa ta ɗaga ƙiran tana murmushi ta masa sallama.
Abbah kuwa daidai lkcn suka shugo asibitin, yace“Bahijjah Abbana ne fa ba lafiya an harbeshi wai gamu mun shigo hospital kuyi sauri kuzo agwada jini wanda za'a saka masa acikin mu.”Mummy ta rikice hankalinta amugun tashe take faɗin. “Innalillahi wa'inna alaihir raji'un!! “Abban Taslim kodai an kashemin yaro ne?” Abbah yace“Yanzu na shigo hospital ɗin kuyi maza kuzo.”Ya faɗi yana tsinke ƙiran. Ya ƙira Hamza ya faɗa amsa shima hankalinsa a tashe daman ya fito yana kusa da asibitin dan haka ya nufi asibitin. Mummy har ta fara hawaye. Taslim tace"Mummy lafiya? “Wa aka kashe?” Mummy ta juya cikin parlon a guje. Suka bita sun fara kuka suna tambayarta. Rahma kuwa gabanta yake mahaukacin bugawa har wata zufa taji ta keto mata, so take taji waye aka kashe. Mummy hijabi ta saka. Tace“ Taslim maza kaimu hospital, banso kowa ya tambayeni, sai munje. muga abinda Allah yayai.” Haka suka fice daga parlon san sun matan da Ruwaida na bacci, daɗin abun da ƴan aiki a gidan. Suna fita Suka shiga motar Taslim, tama masu kaɗan haka suka matsu suka shiga, alhalin ga motoci nan amman saboda tsabar ruɗewa haka suka matsu taja suka nufi hospital ɗin. Babu Editing😌Kuyi manage, *Real Ladingo ce☺️*
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.