*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
'''Zan So Kar Ayi Babu ke!! A Wannan Labarin '''
*👉🏻TUN RAN GINI RAN ZANE Wai Wai Wai Ko daga Jin Sunan Hummmm Akwai Abubuwa Cike Da Wannan Tafiya. To Real masoya, Kar Na Cika ku Da Surutu, Albishirinku Masoyan littafin Real Ladingo, Nasan Dai Kunsan littatafanta, Ba Sai Na Tsaya Nayi Maku Dogon Sharhi Ba.....So Dan Haka, Yanzu Ma Ina Ɗauke Da Sabon Labari Shima Salon Na Daban Ne. Karda Kuyi Rauni Ko Gazawa Wajan Siyan Wannan Book Mai Suna Tun Ran Gini Ran Zane... Nasan Wasunku Sun fara karanta Labarin Banyi Nisaba Na Tsayar Dashi, To Na Canza Salon Labarin Yanda Zai Ƙara Tafiyar Da Zuciyar Mai Karatu,Akwai Abubuwa Masu Tarin Yawa cikin Labarin Na Daɗi Da Akasin Hakan, Sannan Akwai Rikitacciyar Soyayya Mai Zafin Gaske Tare Da Sadaukarwa Akwai fa Badaƙala Akwai Akwai Akwai....Kai Kundai San Ladingo So Kar kuji Shayin Siyan Wannan Littafi Akan Nera N200 Kacal Ga Mutanan mu Na Niger zaku Biya 400F Ne Kacal. Insha Allah 22 ga Watan na October Zan fara baku Free Page, 💃🏻Ku Garzayo ku kwashi Rabonku, Zaku Fadakartu Zaku Kuma Nishaɗantu, da wata sansanyar Soyayya. Ga Masu Buƙata Ku Tuntuɓeni Ta Wannan Number👉🏻22796515805. Wannan Salo Shima Na Daban Ne...🤙🏻**Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 15*
Mutuwar tsaye Safuwan yayi sakammakon wannan mata biyu, masu kayan aiki da suka manne masa gaba da bayansa, daman lallaɓawa yake, nan take yanayinsa yayi mugun sauyawa, hajiyarsa ta fara haniniya, tana ƙoƙarin fara harbawa, cikin ƙoshin lafiya.
Cikin jarumta ya sanya hannunsa ɗaya ya janyo Rahma ta dawo gabansa, yana watsa mata mugun kallo, da fitinannun idanusa.
Haka ya janye Ruwaida daga jikinsa, ya damƙe hannunta cikin nashi, ba tare da ya kalleta ba, yace da Rahma cikin nuna isa da ɗaga murya yace. "Me nace maki akan rungumata? Ina wasa dake ne...?" ya faɗi yana kafeta da shegun fitinannun idanunsa, masu mugun gigitats. Jikinta ya fara tsuma ta runtse idanunta. Ruwaida kuwa wacce sam bata haiyacinta jin ya rabata da jikinsa, ta fara ƙoƙarin, janye hannunta tana hawaye, dukansu mugun haushinsu takeji, daga Rahma har Abbaye'n, ga marin da ya mata wanda ya zama na farko a rayuwarta, (dan ita tinda ta tasa bata taɓa jin ko zaginta anyiba.)
Amman yau wai wani ya mareta saboda ta ƙyale budurwasa. Cikin ranta tace"Wallahi baka san halina bane ni shikenan na fita sabgarka yaya Abbaye zaka san wacece Ruwaida!" daidai lokacin yace da Rahma"Ke!! Ba magana nake maki ba!" Rahma bakinta na rawa tace"Kai... Hkr..."Mummy ce ta nufo wajan, a guje, Taslim nace mata"Mummy shida Ruwaida ne fa..." Ina bata tsayaba ta tafi, sabida sunji tsawar da akai ma Ruwaida, kasancewar tsakanin kofar parlon da can parlon akwai nisa har sai an karya kwana. Acp ya ɗauke kansa yace"Ki saita nutsuwarki mu shiga." ya faɗi yana kallon Ruwaida wacce tayi wata irin cika, tayi famm sai hawaye ke fita daga idanunta, tana danne kukan ne saboda kar ya sake marinta, amman ta ɗaukarwa kanta alƙawalin bazata sake shiga sabgarsa ba.
Fitinannun idanunsa ya lumshe yana murza tattausan tafin hannun Ruwaida, ɗan matso da ita dab dashi yay, amman sam bai iya mgn ba dan ba ƙaramin ƙoƙarin mgn yake ba.... Hucin juna suke ɗan shaƙa. Ruwaida ta fara ƙoƙarin janye hannunta tana kauda fuskarta, tana son matsawa, ya sanya yatsarsa ya ɗalle mata laɓɓanta, sam bata masa sangartar da take masa ba, duk da taji zafi, da kuwa idan ya mata hakan tana masa shagwaɓa, ko ta kama yatsarsa ta saka a bakinta, ta ciza.
Ƴar ƙaramar yatsarshi ya saka mata cikin bakinta, yana jujjuyawa ta sadda kanta ta fara shasheƙar kuka, yay saurin mannata ƙirjinsa, yana buga bayanta. Haka sukaji wani irin zirrrrr yarrrrrr shock ya jasu a tare, ya tura hannunsa cikin sumar kanta mai masifar laushi wanda ke fitar da azababban ƙamshi, yana shafawa yakai bakinsa dab da kunneta cikin wata kasalalliyar murya mai azabar daɗi, kai daga jin wanda akama mgn da ita, kasan ba ƙaramin nisa akayi ba a tafkin ƙaunarsa, ba ƙaramar ƙauna ake masaba.
A hankali ya furta "Angel! Yayanki ne ko?" ya faɗi yana huramata iskar bakinsa, cikin kunneta, haɗi da tallafe fuskarta, ya ƙurama kyawawan kumatunta idanu, ganin shatin yatsunsa akan kyakyawar fuskarta, sam ya shagala ya manta Rahma na wajan. Ruwaida wani irin yammm taji ajikinta lokacin da ya ƙirata da Angel, Yazeed ya faɗo mata aranta, kawai sai ta kece da kuka, tana ƙoƙarin janyewa daga jikinsa. Rahma ta kallesu ta kawar dakanta saboda yanda taji wani abu ya taɓa mata zuciya, wani matsanecin kishin Ruwaida ya baibayeta, wani irin baƙi take gani, amman ta danne ba halin nunawa ya mata masifa, amman abun yayi mugun ɓata mata ranta, kuma farat ɗaya ta gano yarinyar son mijinta take, duba da yanda take lafewa jikinsa.
Aranta tace"Tabdijam! Me yarinyar nan take nufi"? Azahiri kuwa ta cije ta taɓe bakinta dakyat ta buɗe baki a dak'ile tace"My Acp. Nawan na kintsa muje." Ruwaida tana sharɓar hawaye, ta ɗago ta kalli Rahma ta zumburo baki ta kauda kanta, tana ƙoƙarin fizge hannunta anashi. Rahma ta ciza lips ɗinta ta kauda kanta. Lokacin sukaji maganar Mummy tana cewa. "Abbaye waye kake ma wannan tsawar haka?" Ruwaida tana ƙoƙarin janye hannunta, daga riƙon da ya mata, yay saurin riƙeta ya kama hannunta da hannun Rahma suka nufo wajan Mummy. Abbaye ya tsaya gaban Mummy baiya mgn ba saboda ta cije sam yatsani magana a rayuwasa yau kuwa ya shata. Rahma ta isa wajan Mummy ta tsugunna har ƙasa tace"Mummy ina kwana." Mummy ta kama Rahma tace"Lafiya lau mu ai an yini ma kinji ana kiran salla, muje parlo, wai meke faruwane...?" Ruwaida ta fizge hannunta ta fashe da kuka ta isa wajan Mummy ta faɗa jikinta. Mummy tace"Rahma tsakaninki da Allah me Acp yay ma wannan baiwar Allah nan?" Safuwan ya taɓe baki ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa, ya nufi parlon.
Rahma tace"Wai dan na mata mgn ta ƙyaleni shine ya mareta!" Mummy tace"Ya ilahi wannan yaro akwai fitina wlh, to shikenan yi haƙuri ki rabu da yayanki , zan rama maki tana yuwa shigar jikinki tasa ya mareki gashi ba ɗankwali kuma kinsan ba lafiya ce dakeba Ruwaida! Kiyi hkr zan rama miki Muje to yi haƙuri." haka Mummy ta lallasheta tayi shiru se ajiyar zuciya take saukewa, taja su suka nufi parlo.
Su Aneesa kuwa bedroom suka shige, suka murza key har Fu'ad da ihsan da Saif, ƴaƴan Taslim, dan yau sun tsorata da uncle ɗin nasu.
Safuwan na isowa wajan, Taslim ya zauna ya jingina da kafaɗarta yana sosa sajan fuskarshi. Taslim tace.
"Acp bakada daɗi me ƴar gidanka tama ka keta mata tsawa haka? Yauwa ɗan kanina please bani ita mana kaga Abbansu Ihsan ba mazauni bane."Abbaye ya ɗago yana hararata, can ƙasan maƙoshi yace.
"Ko tanada lafiya bazan baki ba, bare batada." Taslim tayi murmushi tace"Ngd Acp da rashin kirki." Mummy ta iso tana kirta faɗa. "Wlh Acp baka kyautawa sam, ya zaka marar mani ƴa?" ta faɗi tana zama ta zaunar da Ruwaida kusanta, ta rungumeta tana buga bayanta. Luf ta laɓe jikin Mummy tana sauke ajiyar zuciya, ta lumshe idanunta. Rahma ta zauna kusan Taslim ta gaisheta. Taslim tace"Rahma ya haƙurin zama da miskilin mutum?" Rahma ta sadda kanta, batayi mgn ba.
Abbaye ya kalli Ruwaida ya taɓe baki ya miƙe yace"Mummy se na dawo."Bai jiraba ya wuce abinsa ya nufi ɓangaransa. Rahma tana so tace zata koma, amman sai taga daga zuwa bari ta jima. Mummy tace"To Allah ya tsare, amman sai na ramama ɗiyata marinta." bai ko juyo ba. Yana zuwa bedroom ɗinsa ya rage kayan jikinsa, ya shiga toilet, sosai ya jima kafin ya fito, yana fitowa ya sake wata shigar kananun kaya ya saka, sunyi bala'in dacewa da jikinsa, sai baza ƙamshi yake, ya ɗauki bindiga ya ɓoye, a jikinsa ya fito, ko wajansu Mummy bai kallaba ya ficewarsa zuwa masallacin gidansu, daga nan ya wuce farautar Sale.
Taslim ta ƙira Larai ta kawoma, Rahma lemo da ruwa da abin motsa baki, amman sam kunya ta hanata ci. Ruwaida ta janye jikinta ta miƙe, ta nufi bedroom ɗinsu. Mummy tace''Zaku shirya kunfi kusa." Rahma tayi murmushi. Mummy tace"Rahma ya wajansu malam da inna taki?" cikin ladabi ta amsa da "Lafiyasu lau Mummy."
Ruwaida ƙofar ta buga saida suka tambaya, jin shiru ba mgn sukaƙi buɗewa. Mummy tace"Rahma je ki musu mgn Ruwaida ce." cikin ladabi ta amsa da "To" ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu Islam.
Tana zuwa tace"Widaad ku buɗe yayanku ya tafi fa." jin muryata yasa islam tazo ta buɗe. Rungumeta tayi tace"Oyoyo Aunty." Ruwaida shigewa tayi taba Aneesa wayarta, ta shiga bathroom.
Rahma su Aneesa baibayeta sukayi suna mata sannu da zuwa. Nan ta baje ta saki jiki dasu suna hirasu, Ruwaida kuwa tana fitowa tayi sallar azuhur haɗi da ta ramuwa, ta haye saman bed ta shige cikin blanket, tana murza zoben hannunta tana sauke ajiyar zuciya ajere², tasa aranta bazata sake kula Ya Abbaye ba.
Babu yanda su Islam basuyi da itaba taki kulasu, ta masu nuni bacci takeji, dole suka mata uzuri. Suma salla sukayi sukaci gaba da hirasu, Rahma ta rasa me tama yarinyar ta nuna mata tsana ƙarara.....
Giɗaɗo hospital ya nufa akai masa dresing ɗin kansa, daga nan ya nufi gida ya kwanta, shi kadai yasan tsarin da yana Ƴar libah yanda zaici ubanta...!
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.