*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa''' https://www.wattpad.com/story/257022776
*_Wow!! My Fan's Billahi Kuna Sakani Nishaɗi, Sbd Zafafan Comments Ɗin Da Kuke Akan Wannan Book Na Ruwaidah, Ina Jin Daɗin Hakan, Shiyasa Nake Ƙoƙartawa Wajan Baku Update Kusa², Billahi Ina Ƙaunarku Fiye Da Yanda Kuke Ƙaunar Ruwaida,🤣😂Ina Maku Son So.😘_*
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 35*
Ana idar da sallah Safwan ya fito, domin ya ƙira Nadeer yaji lfy yake kwaɗa masa ƙira, da magarib. Nan bakin gate ya tsaya ya ƙira Nadeer, bugu ɗaya ya ɗaga yana faɗi“My friend! Awane hospital ne matar tamu take? Tana kuka da ta ƙirani ban tambayeta sunan asbitin ba...?” Abbaye ya katse Nadeer ta hanyar cewa“Wace matar taku kuma? Nadeer yace“Kana rainawa kanka hankali fa, kanada mata bayan Rahma....?” Abbaye yace“Me ya sameta? Wlh ban saniba?” Nadeer yace“Ikon Allah!! To ta ƙirani tace mota ta kaɗeta, tin yamma ta ƙiraka baka ɗauka ba, ta turama saƙo bakace kome ba...” Abbaye yace“Subahanallahi! Wlh ban ganiba, ina zuwa.” ya faɗa yana yanke ƙiran ya shiga wajan messages yana dubawa yaga saƙonta. Kansa ya dafe, yay dialing ɗin number ta yana shiga cikin gidansu. Bugu biyu ta ɗaga da sallama. Abbaye yace“My dear ya zaki kai ƙarana ba tare da cikakkiyar hujja ba? Me ya sameki? Oya faɗamin hospital ɗin da kike...?” ya ƙarashe mgnr yana jan ƙaton numfashi, sbd doguwar mgnr da yayi. Rahma tace“Wlh tsautsayi ya giftamin, naje rakiyar su Samira motar yarima ta bugeni, amman da sauƙi.. Kayi hƙr nawan wlh nazata ka gani.. Abin ya dameni ne yasa na ƙira amininka.... Muna *city clinic*.” ta faɗa tana dafe goshinta.
Acp rumfar ajiyar motoci ya nufa, yana faɗin“Ya Salam ganina zuwa dear.” ya ƙarashe mgnr yana yanke ƙiran, ya saka wayar cikin aljihunsa. Kai ya dafe babu makullin mota atare dashi, da sauri ya nufi cikin gidan. Parlon ba kowa, yaje ɓangaransa ya ɗauko makullai, har zai wuce ya koma ya nufi bedroom ɗin Mummy, ya faɗa mata. Tana zaune tana azkar, ya shigo da sallama. Mummy ta amsa tana kallonsa. Yace“Mummy Rahma ce babu lfy, tana hospital mota ta bigeta....”Mummy arikice tace“innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ta faɗi tana ajiye casbaha ɗin, hannunta ta miƙe tsaye. Abbaye yace“No Mummy zauna bari naje nazo...”Kaci gidanku wuce muje.” ta faɗi tana ɗaukar wayarta, ta kama hannun yaronta, tana faɗin Abbanku na masallaci muje idan mun isa zan ƙirasa.” falo ba kowa, ta nufi ɗakinsu Ruwaida ta iskosu duk suna kan darduma azaune, suna karatun Qura'an kafin aƙira isha'i. Mummy tace“Yauwa ƴaƴan albarka, mutafi asibiti antynku Rahma ba lafiya, dan Allah karkuyi rashin jin mgn.”tana faɗin haka ta juya. Gudu Safwan yay sosai bai jimaba, sai gasu A hospital ɗin. Basu sha wahala ba, wajan gano ɗakin da aka kwantar da Rahma. Inna nata kumfar baki, Asma'u tace“Inna don Allah kiyi hƙr, ai sai mugodawa Allah da abin ya tsaya ahaka fa...”Hindatu tace“ Gaskiya fa...”ƙaran buga ƙofar ya katse masu mgn, Asma'u taje ta buɗe. Acp tagani tsaye, shida Mummy. Cikin girmamawa ta gaishesu, ta basu hanya suka shigo. Inna ta saki fuska tana faɗin“Sannunku da zuwa.” Acp ya gaishesu cikin girmamawa. Mummy ta zauna kusa Rahma, ta riƙo hannunta, tana faɗin. “Sannu dota Allah tsare na gaba, ashe har ɗinki aka miki?” Rahma ta ɗaga kanta tana faɗin“Eh Mummy.” Mummy tace“To ina wanda ya kaɗekin? Fatan ba guduwa sukayi ba...?” Inna tace“Basu gudu ba kam, amman sun tafi.”Abbaye ya ƙurama Rahma ido cike da tausayinta, ganin goshinta ya kumbura. Itama kallonsa tayi ta sadda kanta. Acp yace“Allah mun godema da abin ya tsaya anan, Allah baki lfy bari na shiga masallaci.” Ya faɗi yana juyawa. Inna tace“Baban nakuma na masallaci.”Rahma ta kalleta, haushi kamar ya kasheta.
Mummy ta ƙira Abbah ta faɗa masa, shi da Hamza ba ɓata lkc suka nufo hospital ɗin. Can gidan mai martaba ana fitowa daga masallaci, ya bada umarni ashirya komawarsu hospital domin su duba jikin Rahma, sannan suba iyayanta haƙuri.. Yarima Al'ameen yaso yay musu, saida sarki ya taka masa birki, kafin su tafi.
Zaune suke ana hira bayan gaishe². Abbah sosai Rahma ta bashi tausayi ganin harda ɗinki agoshinta. Malam Ɗahiru yace“Alhaji an baro yara su kaɗai ai gwara ku koma, tinda jikin nata da sauki, likita yace gobe za'a bamu.....” ƙofar da aka ƙwanƙwasa yasa bai idar da mgnr ba. Acp da yake kusan ƙofar shine ya buɗe.
Ganin mai marta da yarima yasa, ya cika da mamaki, dan sam ɗazu baima ji abinda Rahma tace masa ba. Hanya ya basu haɗi da gaisuwar girma... Idanunsa suka sauka kan sarki Sulaiman saida yaji gabansa ya faɗi, sbd tsabar kamar da ya gani ƙarara, da Ruwaida. Su Abbah cikin girmamawa suka tarbesu. Mummy kallon mai martaba Sule, take sosai yay mata kama da Ruwaida, saidai tasan da Ruwaida ƴar nan kusace, da tuni anyi ta cigiyarta gidajan Tv da redio.
Yarima yaba Acp hannun sukayi musabaha, yace“Ƙanwarkace muka buge? Afuwa ba yanda direba baiba, ya tsayar da motar amman abin ya faskara...”Acp yace“Ba kome Allah ya tsare na gaba.” daga nan bai sake mgn ba, sbd ba damunsa mgn tayi ba.
Su mai martaba haƙuri suka sake badawa. Malam Ɗahiru yace“Haba ranka shi daɗe Allah yaja da kwananka, ai da ba sai kun dawoba, ƙaddarace abinda Allah ya ƙaddaro sai ya faru bawa baya tsallakewa ƙaddarasa.”Sarki Sulaiman yace“Hakane muna godiya Allah ƙara mata lfy.” ya faɗa yana kallon Rahma. Wacce itama shi take kallo tanaso tace wani abu amman ta kasa ta sadda kanta. Wata ƴar takarda ya faki idanun jama'a ya ɗorama Rahma kan cinyarta,yayi daidai da ɗagowarta, tai saurin kallonsa taga bama ita yake kallo ba, yarima yake kallo suna sakarma juna murmushi, suna jinjina kai. Yarima ya saci kallonta yaga shi take kallo, da alamun tambaya? Ya harareta ya kauda kansa. Ta kalli jama'ar ɗakin suna mgn hankalinsu baya wajansu.. Takardar ta ɗauka, ta jimƙe ahannunta. Ta kalli Acp yana gefe sai taga kamar sarki yake ɗauka picture. Kwanciya tayi ta lumshe idanunta. Alkhairi sosai sarki yama iyayan Rahma suka tafi, su Abbah rakiya har mota, dogarai sai kakkara su sarki ake har suka shiga mota. Abbah da Hamza sunyi mamakin tsantsar kamar da suka gani Ruwaida da mai martaba. Suna sallama sukama su malam suka tafi.
Dirving Acp yake amman hankalinsa wajan wannan mutum me kama da Ruwaida, yana so yayi wani ɗan bincike, akansa bazai bari wannan damar ta kuɓuce masa ba, duk da yasan ba wai lallai bane hasashansa ya zama gaskiya, shiyasa ya ɗaukesa hoto ba tare da ya saniba, yana so ya nunama Ruwaida ko zata tuna wani abu... Abbah yace“Abbanmu kako ga abinda na gani wannan sarkin na tare da sarki Abdulhakim yana kama da Ruwaida...” Mummy tace“Nina fara gani, amman fa ba wai hakan yana nufin sunsan junaba...” Abbaye yaja dogon numfashi yace“ Nagani Abbah zanyi bincike akai insha Allah, duk da ba lallai ya kasance ba, akwai alaƙar jini atsakaninsu, amman kamar mahaifinta, dan gskuya irin wannan kama bata tashi A abanza...” ya faɗi yana addu'ar Allah yasa mahaifin Ruwaida ne.
Abbah yace“Naso masa tambaya amman nayi shiru, bari zan ƙira waziri sbd muna harakar business sosai dashi, zan ɗan bincikeshi...”Abbaye yace“ Abbah nasan me zan tsara karka ƙira kowa......
Inna yau ba lfy fa🤣sai bubbuɗe hanci take, sarkin garin Taraba guda yazo gaishesu ya masu kyauta. Inna ta gyara zama tace“Rahma tinda na haifeki akullun cikin gamo kike na alkhairi, wai babban sarki guda yazo yana bani haƙuri tare da alkhairi, kai Rahma sunanki na bibiyarki, Allah baki lfy...”Malam yace“Kece Allah zai ba lfy, sbd haukanki yau ya fito ƙarara, Zinaru kin kusa kaini bango, wlh ki kiyaye fa.. Idan kikayi wasa wlh aure zan ƙaro kwananan, tana yuwa ta sanadiyar amarya ki dawo hankalinki, haba abunki ɗinan yayi yawa, wai ance miki ta haka ake arziki? Ko zama wani tsiya ta ƙarfi...?” Inna ta zaro idanu😳“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Malam Ɗahiru!!!! Nice zakama kishiya gotai² dani?? Ta faɗa tana tafa hannayenta, ta miƙe tsaya tace“Anzo wajan! Ashe akwai bala'i yanzu zakaga haukana...”Asma'u tace“Baba kayi hƙr ni kam na tafi gida bazan iyaba, da wannan abu.. Haba inna ke kamar ƙaramar yarinya, Babana ni bazan hanaka raya sunnar ma'aiki ba...”ta faɗa tana ficewa aguje sakammakon ɗan table ɗin da inna ta warta tayi kanta.
Hindatu ta riƙeta, inna tace “Sakeni banson harakar munahirci, bakinku ɗaya ƙilama ke kika sakashi.“ Sa'adatu tace“Ɗan Allah Aunty ki daina.” Rahma tace“Inna me kike haka? Asibiti fa muke, haba dan Allah ki barni naji da kaina, wlh kaina kamar zai faɗo ƙasa.”ta faɗa tana fashewa da kuka. Inna ta zauna kusan Rahma batace kome ba, sai huci take, ta rungume ƴar tata. Malam yace“Rahma ni zan koma gida, Zainab da Sabira muka bari.”Rahma ta ɗaga kai bata iya mgn ba. Malam yace“Haƙuri zakiyi Rahma, Allah baki lfy sai da safe.” ya ƙarashe zancan yana ficewa. Hindatu bakinta taja tayi gum, ganin yayan nata ya tafi, yanzu masifar zata dawo kanta.
Can ɓangaransu Ruwaida suna sallar isha suka fito. Ummuh da lailah suna falon zaune, nan suka baje suna hirasu, Ruwaida ta saki jikinta, suna sha'sninsu. Can ta miƙe ta saci jiki ta fice, kai tsaye part ɗinsu Bappa ta nufa. Zaune suke afalon suna hira, harda Aneesa amarya. Ruwaida ta zauna kusan ummani tana murmushi. Bappa yace“Ah yau matar kin tuno damu? Lallai. Ruwaida tayi ƴar dariya tana rungume ummani. Ummani ta shafi bayanta , tace“Har yanzu iyayan naku basu dawo daga asibitin ba? ”Su Ni'imah ma ahiru Musaddiq ya tafi can bayan gari tarbarsu, ko sun iso Ruwaida?” Kai Ruwaida ta ɗaga ashagwaɓe alamar basu zoba, tinda ita batama san su waye ba.
Aneesa tace“Allah sarki aunty Rahma Allah bata lfy, naji lkcn da Abbah ya shiga gida yana faɗama Dady suka tafi.” Bappa yace“Ameen” Aneesa tace“Ruwaida ba an hanaki fita ba, ke ɗaya? Shine kika sato jiki kika shigo nan ko?” Manyan fararen idanunta ta waresu akan Aneesa ta wani turo baki gaba. Aneesa tayi ƴar dariya tace“Wow!! Black beautiful.” Ruwaida ta harareta tana janye idanunta akan Aneesa ɗin, ta miƙe ta isa gaban Tv ta kunna tashar *Mbc Action* ana nuna wani film mai shegen daɗi, me suna (Blood Diamond) Ta zauna kusan ummani ta kwantar da kanta kafaɗarta, tana kallo sosai ta bada hankalinta wajan kallon film ɗin.
Acp ne tsaye gaban ƙaton gate ɗin gidan nasu, yana zuba uban horn. Megadi ya wangame masa, gate ɗin ya shige da motar. Tafkekiyar rumfar ajiye motocin ya shige, yay parking.
Yana fitowa ya buɗema iyayan nasa suka fito. Widad ce tsaye tana rawar india, yayin da islam da Nadiya da Fu'ad ke tafa mata, su ummuh na dariya. Sam basuji ana knocking ɗin ƙofar ba, har larai taje ta buɗe masu suka shigo.
Acp bakinsa yake cizawa ya harɗe hannayensa aƙirjinsa yana kallon ikon Allah. Mummy tace“Widad!! Wato shegantakar da kuke kenan idan bana nan? “Ummuh kuna kallonsu abin ku hanasu dariya ma kuke masu? Ina Ruwaida?” Atsorace!! Suka juyo suna rarraba idanu. Widad kaɗan ya rage bata saki zawo ba, ganin mugun kallon da Abbaye yake watsa masu. Zasu gudu ya daka masu tsawa da ta firgitasu. Cak suka tsaya. Cikin tsawa yake mgn “Yau zaku raina kanku, wlh sai na muku lilis muna famar kawar da matsala kuna ƙara jefamu wata ko? Zakuci ubanku wlh yau, inna Ruwaida?” Islam na rawar jiki tace“Tana ɗaki.” Hamza yace“Ashe yau su Nadidi za'a daku.” ya faɗa yana danne dariyarsa, sannin ƴarsa ba abinda take tsoro kamar duka, shiyasa batama fiye shigowa gidansu Acp ba, sbd da sanin halinsa.
Abbah yace“ Ai kuwa zasu daku har me sunan umma kai masu lilis ba ruwanmu, sbd gobe su kiyaye taka doka idan mun saka agida.”Mummy tace“Ina fa ruwanmu kaci ƙaniyarsu.” ta faɗa tana bin bayan Acp da ya nufi bedroom ɗinsu Ruwaida. Hamza ma yama ɗan uwansa sallama ya juya ya nufi gidansa. Su islam suka rungume Abbah suna kuka su dukansu,jikinsu tsuma yake, ba kamar ma Widad tinda ita aka kama tana rawa. Tako san ba dukan wasa Acp zai masu ba. Abbah yace“Ku sakeni wlh ba ruwana, ku ƙarata da Abbanmu...” Ummuh ta miƙe domin bin bayan Acp, tana faɗin“Kuyi shiru bari na lallasosa, laifinane amatsayina na babba da ban tsawatar maku ba......” Sallamar Musaddiq da Aunty Ni'imah da Sadeeq wani matadhin gaye kyakyawa fari. Itace ta katse ma Abbah mgn. Ummuh ma ta dawo da baya tana faɗin“Wai-wai- wai!! Manyan baƙin Niger.” ta faɗi tana nufar wajansu. Ai kuwa cikin farin ciki su islam suka saki Abbah suka ruga da gudu wajansu aunty Ni'imah suna faɗin“Ga momy shikenan baza'a dokemu ba...” suka faɗa atare suna rungume Aunty Ni'imah. Sadeeq ya nufi wajan Abbah da sassarfa yana faɗin“Tu me manque bpc Abbah.” ya rungumeshi. Bahijjah ta shiga waige waige tana faɗin“To ni ina Ya Safuwan?”
Acp ya morɗa ƙofar bedroom ɗin ya sakai. Dube² ya fara baiga Ruwaida ba. Mummy tace“Tana ina?” Kallonta yay ya nuna mata ƙofar bathroom gabansa na faɗuwa, yace“Mummy shiga ki duba ko tana ciki.” ina zuwa ya faɗa yana ficewa daga cikin bedroom ɗin.....
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.