*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
*~💃🏻💃🏻💃🏻Waouh mes fans je vous~* *~remercie infiniment pour vos commentaires, en~ ~vérité ~je vous adore. Continuez à~ ~commenter et moi je~ continue~ ~à vous faire plaisir dans~ ~l'histoire de Ruwaidah.~*
*~Toujours mon merci😘😘😘~**Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 3*
Kauda kansa yay daga kallonta, Idanunsa ya lumshe yana fesar da zazzafar iskar bakinsa waje, har ta iso jikin motar, saida ta ɗan ƙwanƙwasa glass ɗin motar, ya buɗe fitinannun idanunsa yana jan guntin tsaki, A hankali ya ɗan ɗago da kansa ya beƙa hannunsa ya buɗe mata murfin motar ya kauda kansa gefe, yana ciza lips ɗinsa na ƙasa.
Da sallama ta shigo ta zauna fuskarta ɗauke da murmushi, sallamar ya amsa can ciki, bai kuma tanka taba, tamkar bashi bane ya gama ƙare mata kallo, ya wani basar da ita.
Gaishesa tayi tace. "Abokin rayuwata ina yayanmu ai masa barka da zuwa." ta faɗi tana ƙureshi da idanunta, sbd yanda yay mata wani irin mugun kyau, ga wani fitinannan ƙamshisa dake tashi acikin jikinsa da motarsa, ya cika mata hanci.
A hankali yace" Ok" daga haka bai sake mgn ba, ya sanya fararan hannunsa ya ɗauki ledar ya beƙa mata, yace"Amshi zan..." bai ƙarasa ba ya kalleta, fuskarsa babu wani walwala.
Murmushi ta saki ta sanya hannunta biyu ta amshi ledar, tayi sauri kauda kanta saboda mugun kwarjinin da ya mata tace.
"Zaka wuce ko? My Acp shine baza'a iya ƙarasa faɗa ba, please kaji ma mana." ta faɗi tana ɗan satar kallonsa, dan bataso su haɗa idanu. Wani kallon ya watsa mata yace"Naƙi." murmushi tayi ta kifa kanta saman kafaɗarsa, tanajin tsananin ƙaunarsa aranta...Kanta ya matsar ya buɗe mata kofar motar dakyat yace.
"Bye" dole ta fito sanin halinsa, tana murmushi ta rufe masa motar tace"Tnx nawan." kai ya jinjina ya fizgi motar yabar lungun. Cikin gidansu ta nufa. Tana zuwa ta ajiye ledar gaban mahaifinta tace.
"Baba gashi ka ɗauka se kabamu sauran." Malam Dahiru ya fara faɗa yace"Au daman roƙonsa abu kikayi Rahma?" risinawa tayi tace"A'a ɗazune munyi waya yace me nakeso , nace ba kome yace ƙaryace ina so, shine nace to ya kawomin ice cream bari na buɗa na gani, nasan abubuwane dayawa zai siya."
Ta faɗi tana buɗe leɗar ice cream ɗin ne kuwa da ta tambaya ya kawo mata shi kadai....idanu ta waro tana dariya tace"Wlh Baba ice cream ɗinne kaɗai kuwa Ta faɗi tana dariya Zainab ta iso ta ɗauki roba ɗaya, ta fara sha.
Innah talatu tace"Hummm yo wai kin manta hudubar Malam yake ɗauka ya ƙame hannunsa ƙam fa yaron nan, baya wuce abinda kika ce, an hanashi to ya zamuyi da ƙaddara se haƙuri..." ta faɗi tana ɗaukar robar ice cream guda ta buɗe tana cewa"Uhm bari na rage zafin ciki, Allah ya kyauta kawai shi zance." Malam Dahiru yace"Ameen nidai wlh bana buƙatar kome kuma na hana ma ƴata roƙo, idan kika zugata a ɓoye ban yafe ba....keko Rahma kici gaba da biyayya zakiji daɗi, ko ice cream ɗin karki sake nema wajansa ya burgeni hakan ya nuna ko agidansu shi mai biyayyane ya nunamin kowa nada daraja wajansa ba sai mahaifinsa ba..." Rahma ta miƙe ta koma saman tabarma tana dariya.
Zainab tace"Allah innah ki daina hakan babu kyau."
Ta faɗi tana komawa wajan Rahma. Innah talatu haushinsu duka takeji shiyasa tayi shiru bata tankaba, se ba malam takeso duk taci mutuncin su tana ta shan ice cream ɗinta bata ce kowa kome ba.*Ƙasar Niger*
Bayan su yarima Yazeed sun gama duk wata sanarwa, da ta dace ayi, aka tara masu kakaf bayin dake cikin wannan babbar masarauta, mai daraja bayine bila adadin, wanda basusan hawaba basusan sauka ba....Yarima Yazeed ne tsakiyar bayin idanunsa jajur, se Hajiya kilishi sai Sarauniya suna zaune saman wasu irin kujeru, masu kyawun gaske.
Gefe Ashiru ne magajin yarima, idanunsa tamkar garwashin wuta, sai zurganiya suke tsakiyar bayin..... Jakadiya na nan zuɓe gefe guda ilahirin jikinta rawa yake dan zuwa yanzu ta fara tsorata da wannan al'amarin....duba da yanda aka ɗaure Mabaruka ƙafa da hannunta akan ma tana ƴar gidan Waziri guda......to ina ya bayi...... Hajiya kilishi ta dake tsaye guri guda tana ƙarema bayin da suke cikin wanan tafkeken fili a ɓangare guda daga cikin masarautar, kana ganin filin kasan an tanadeshine domin irin haka.
Yarima Yazeed ya fara magana cikin ɗaga murya wacce sam bata fita irin dayawa ɗin nan saboda rashin sabo yace.
Wallahi tallahi ina matuƙar tausayin wanda yake da hannun a cikin ɓatan Ruwaida ya yanke ma kansa hukunci mafi muni a rayuwa, da nayi niyar horakune baki ɗanyaku sai nayi tunanin zanci zalin Mutane dayawa a cikin ku wanda inada tabbacin akwai wanda basuda hannu akwai wanda suke da hannu dumu-dumu acikin wannan lamarin, to wallahi ku kuka da kanku ba mace ba namiji, duk wanda yasan wani abu ya fito ya faɗi gaskiya ayanzu wlh na masa alƙawarin babu abinda za'a masa, albarkacn masarauta mai adalci, zata maku uzuri, sbd kun faɗi gsky ba tare munsha wuyaba......ku nake saurare." ya faɗi yana dimfaru wajan Mabaruka wacce take rusar kuka. Waziri ne tsaye gefe tare da Ahalinsa, ransa yay matuƙar ɓaci ganin irin ɗaurin da akama ƴarsa, akan abinda babu tabbas, ta yaya Mabaruka zata ɓoye Ruwaida yarinyar da tafi so fiye da kowa da kome, ta ɓoyeta akan me? Itama jininta cefa...ko son Yarima take ta ɓoye Ruwaida sanin abinda zaije yazo.....Numfashi ya sauke da ƙarfin gaske zuciyarsa na masa zafi....Yana zauwa kusanta yace da Jakadiya. "Jakadiya zo ki tisa tambayarta ta ƙarshe..."Jakadiya jikinta na rawa ta ƙara rusunawa tana cewa.
"Angama yarima me adalci, godiya nake, Allah ya huci zuciyar Yariman damgarawa, ubangiji ya baiyana gimbiya Ruwaidah a duk inda take ya kuma tonu asirinsu duk wanda keda hannu cikin wannan lamarin ko suwaye." Ta faɗi tama miƙewa ta nufo wajan Mabauka ɗin. Gaban Mabaruka ta sunkuyo, cikin magana me taushi tace"Kece wacce kikafi kusanci da Ruwaida bata da wanda take mgn da ita sama dake da kuma Nanah, to gashi Nanah bata nan, se ke kuma a daran kinzo har kin mata tsifar kai....to yaya gari yana wayewa za'ace ba gimbiya, bayan kece mufi kusanci da ita? Kibani amsa ina Ruwaida ina ta tafi ko ince me kika mata? Kina nufi kin mata wani abune tabar gida wato albashi ke ki auri Yarima ko me....?" Mabaruka ta fito da idanunta duka waje tana rusar kuka tace"Wlh ko ɗaya bansan kome ba, amman abinda nakeso daku yanzu aje can cikin faɗa a ɗauko alqura'ani mai girma na rantse ko zaku yarda dani...."Yarima ya kalleta cike da mamaki yace"Kina nufi ki mutu akan kafiya da taurin kai...?" Ya faɗi yana waigoya yace da shamaki" Ina sarkin Fada aje a ɗauko ɗin bama ita ɗaya zata rantse ba ɗayawa zansa su rantsa, mutum ya kashe kansa da kansa...."Hajiya kilishi ita da Sarauniya suka miƙe suka nufo wajan alkabbarsu har tana jan ƙasa Sukace"A'a wannan lamari ko anki anso fa sai sarki yazo ya ɗauki hukunci mai tsanani, abar maganar Qura'an ɗinnan."Hajiya kilishi tace"Sinceta kawai muje can ɓangarena da ita zanci gabda da lallashinta ko xata faɗamin gaskiya."Sarauniya tace.
''Baki ɗayan ƙuyangun Ruwaida a sakasu ɗakin duhu zuwa gobe munafukai dole sunsan wani abu, akama sarkin kofa ma a kaishi ɗakin horo mai tsanani kowa ya koma ya kama gabansa kuje kuci gaba da aikinku sai mai martaba ya dawo..."Tana faɗin haka ta juya ta bi bayan kilishi tana share ƙwalla... Yarima Yazeed yay bayanin da Sarauniya tayi ya saka aka kunce Mabaruka Jakadiya ta nufi ɓangaran Hajiya kilishi da ita....gabaki ɗaya bayan wajan da ƙuyangun suka fara godiya. Nan take aka kama kuyangun Ruwaida baki ɗaya akasu ɗakin horo mai duhun gaske, Yarima Yazeed ya saka aka kamo sarkin kofa, aka kaishi ɗakin horo ana tuhumarsa, lallai yanada sanin fitar Ruwaida...! Abinda ba'a taba yiba a sama da shekaru ɗari da ashirin ana mulkin wannan masaraura sai yau, sam ba a fiye samun saɓani ba, Sbd masarautace mai cike da nagarta da zaman lafiya, tin daga kan sarkunan baya har zuwa sarki Ubaidullah Taheer Abdulsalam kuran daga, har zuwa sarki na yanzu *Sulaiman Taheer Abdulsalam Kuran daga*. Duk da dole asami manaƙisa, a cikin gidan sarauta.
Yazeed faɗawa na biye dashi suna zuba msa kirari tare da bashi haƙuri, babu wanda ya saurara, ɓangaransa ya na nufa. Ya kori kowa ya hana kowa tsayawa ko a kofar ya kori duk masu aikin ya zube saman wata kujera dirkekiya, wacce aka fi ƙira da jinin sarauta, ya dage kansa wanda hawaye ya gama cika masa fuska, ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro wayarsa. Screen ɗin wayarsa ya kurawa idanu yana kallon pic ɗinsu shida Ruwaida tana sanye da wata riga pink mai ɗogun hannun masha Allah tayi wani irin kyau ɗogon baƙin gashinta ya sauka rabi bayanta rabi gefen fuskarta, tana kallonsa tana murmushi suka ɗauki pic ɗin, kanta saman kafaɗarsa hannunta ɗaya saman fuskarsa. Pic yayi kyau sosai. Wani irin ihuuuu ya saki da ƙarfi yana ƙiran"Ruwaidah...!"
Ya faɗi jikinsa yana tsuma ya miƙe yana cewa"Akan me zaku hana a azabtar dasu." Ya faɗi yana ficewa. A funjanjan ya nufi ɓangaran Hajiya kilishi....
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.