*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~Sadaukarwa Page~
*Aunty Baraka Rabi'u Sani*
Son so😍 domin Allah☝🏻~*DEDICATED TO*~
'''My Hubby Hafsat A Garkuwa💖'''~Tukuici Gareki Hajiya Nandalee Mrs Sulaiman. Marubuciyar *Ran gini Ran Zane* Nida Hajiyar Sule Nandalee akwai Amana😂🤝🏻😻~
~Yaufa pagen ba yawa taba ka lashece😋🤣😆😜~
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 10*
Ruwaida sosai take cikin farin ciki, yanda kujerar ke juyi da ita sai murmushi take saki, hankalinta kwance. Hannuta ta ɓeka ta ɗauki wayar Safuwan da ya bata, ta iya fitar da passward ɗin, ta fitar ta shiga wajan gallery, ta fara kallon pictures nasa, iri² harda na Rahma ta gani kala² wani tana dariya wani murmushi wani kanta ba ɗankwali ta baza gashi, haka kawai Ruwaida ta rinƙa jin ɗaci a zuciyarta, sam taji bata sha'awar kallon, wani wanda take sanye da riga da skert na atamfa, ya bata haushi ta goge shi, ta goge wanda gashinta ke baje, ta fita daga wajan gallery ɗin ta fara game.
Acp kuwa tinda ya fita yana wajan Alhj Sabo ana aikin tuhumarsa, Safwan mugune, na gefe yana busa hayaƙi, dan yayi alƙawalin yau sai Sabo ya faɗi masu gaskiya.
Acp ya miƙe tsaye yace"Ku barshi tinda bazai faɗaba, nasan maganinsa, ku bani 3 minutse." ya faɗin haka iso gaban Sabo ya tsugunna ya damƙi fuskarshi da hannun biyu, ya ƙura masa shegun idanunsa, sai ya saka yatsotsinsa ya danne maƙa maƙinsa, iya ƙarfinsa yace"Tsakaninka da Allah waye ya ƙwaƙwalema yarinyar nan ido ɗaya?" ya tambayeshi yana matse masa su tamkar zai cirosu. Cikin azaba Sabo yace"Wlh Sale ne nima bansa ya akayi na fito da yarinyar ba." Safuwan yace "Bamu lbrn inda zamu sameshi?" Sabo yace" banida lbr a yanzu..." Safwan ya ƙara matse iya ƙarfinsa, sai ga Sabo ya suma, kallo ɗaya ya masu suka gane mai yake nufi ya sakeshi yabar wajan. Office ɗinsa ya nufa, zaune take saman lumtsumemiyar kujerasa tana game, kofar ya tura ya shigo. Ɗagowa tayi ta kalleshi, idanu suka haɗa ya harareta, yace"Kujerana ko...?" Ɗariya tayi ta sauko ta nufo wajansa, dab dashi ta tsaya tana nuna masa game ɗin da take. Baiyi mgn ya leƙe yaga game take ya ɗalle mata ɗan ƙaramin jajayen lips ɗinta, da yatsarsa, ɗan ƙara ta saki ta riƙo hannunsa, tana ƙwaƙwaɓe fuska, takai ƴar yatsarsa bakinta zata ciza sai ta fasa ta saki tana ƴar dariya, kafaɗa ya ɗaga yana hararata ya nufi toilet. Ruwaida ko ta koma ta zauna ta shiga gallery baki ɗaya ta shafe pictures ɗin Rahma.
Acp Alwalla yay ya fito yana kallonta, yace "Tashi kiyi alwala." ya faɗi ya juya ya nufi kofa, ya buɗe ya rufo mata kofar, ya nufi masallaci.
Ruwaida kuwa jin ana ƙiran sallah yasa tabar game ɗin, ta ajiye wayar ta miƙe ta nufi toilet.
Sosai toilet ɗin ta mata kyau ganin kome tsaf dashi, kamar ta mace, duk da batada girma sosai, Alwala ta ɗauro ta fito, ta ɗauki turaran Acp ta fesa ta ɗauki darduma ta shimfiɗa ta tayar da sallah. Tana gamawa bayan tayi Addu'a ta shafa ta miƙe tana kalle_kallenta, ta kunna Tv ta ɗauki wayar Acp tana salfie duk kalar yanda taga pictures ɗin Rahma haka take ɗauka itama tana cikin ɗaukar pic wani irin baƙin hayaƙi ya fara tashi daga jikin bango wanda ke haɗe da kofar shigowa, amman sam Ruwaida bata luraba, wata irin hallita ƙatuwa girmanta bashida misali mai manya idanu guda shida girmansu zaikai kwan futilar gargajiya duka a waje haƙora zaƙo² ƙafafunta ƙofaton dokine manya manya, ta baiyana a kofar wani irin taku halittar ta fara tana girgiza, kunnuwanta na ƙara girma, ga baki ɗaya office ɗin ya ɗauki wani irin mahaukacin amsawa da ƙarfin tafiyarta, dammm_dammm.
Sai lokacin Ruwaida ta jiyo wani irin abu wanda ya furgitata ta saki wayar a mugun tsorace ta juyo idanu takwas sukayi da wannan halitta ta saki wani giggitacccen ihuuuuu tace" Yaya Abbaye!! Uncle! Ya Yazeed!" Karaf acikin kunne Acp wanda yake shirin shiga motarsu ta aiki yaransa na tsaye suna jiransa zasu fita. Gabansa yay wani irin faɗuwa, Aguje ya nufi office ɗinsa cikin wani irin mugun ƙarfi yake gudu ya saita bindiga, suma haka duk sun saita bindigogi suna take masa baya dan kaf police station ɗin ba wanda baiji wannan ihun ba, har wajanta. Can kuwa Ruwaida na gama ƙiran mutane uku masu mahimmanci a rayuwarta ta zuɓe ƙasa a sume, bakinta a buɗe idanunta a buɗe, sai ga wani irin abu mai uban haske yana bada hayaƙi, ya fito daga ƙaton idon wannan halittar ya shiga bakinta da idanunta da kunnenta lokaci ɗaya. Dariya halittar ta saki tayi wata irin jijjiga baki ɗayan office ɗin ya girgiza sai gashina ya zama wani irin baƙin ruwa ya gangara ya nufi ƙofa sai kuma guguwa ta tashi 10 second ruwan sulala ta ƙasan kofar ɓat ya ɓata. Dai dai lokacin Abbaye ya banko kofar a guje ya shigo.
Idanunsa ya waro waje ganin Ruwaida kwance kamar gawa bata motsi, Aguje ya iso gabanta yana ƙiranta iya ƙarfinsa" Ruwaida!!" menene ya sameki?" ya faɗi ya sunkuyawa ya cicciɓeta sama ya nufi kujera da ita ya zauna yana rungume da ita, kunnensa ya kara daidai saitin zuciciyarta baiji alamar tana numfashi ba. A mugun zabure ya miƙe da ita jikinsa, ya kallesu yace"Gabaki ɗaya inaso a duba min CCTV camera tin daga na kofar gate ɗin shigo da na compound har zuwa tanan office ɗin naga uban waye wannan ta ina aka barshi ya shigo? Samir CSP yasaka ayi kome cikin gaggawa, ai duk abinda ya dace hospital kawai zan kaita na dawo yanzu." ya faɗi yana ficewa cike da dakiya da jarumta, Ruwaida na manne a ƙirjinsa. Kofa suka buɗe masa suna sara masa. Seat ɗin baya suka buɗe masa ya kwantar da ita gefe ya shiga ya zauna, aka rufe motar asp ne yaja motar aguje tare da ƴan sanda biyu sukabar police station ɗin. Nan ko ciki an fara binkitar CCTV camera, cikinta da wajanta, Dsp Samir kuwa sun shiga mota sun nufi gidan da Sabo ya kwatanta masu.
Safuwan ya ɗora Ruwaida a jikinsa ya rungumeta gama yana shafa bayanta tare da ɗora bakinsa cikin kunnenta ya fara karanto mata Addu'a.
A haka suka iso, *Well being clinic,* nan ake duba kaf family ɗinsu. Suna shiga bayan direba yay parking, suka buɗe mota suka fito suka buɗe masa kofa. Fitowa yay tana manne jikinsa, sai ga nurse guda biyu ɗauke da gadon ɗaukar marasa lafiya.
Amsarta sukayi aka kwantar da ita suka turata, ganin ba inda yake motsi ajikinta, suka nufi Emergency da ita. Safuwan na biye dasu, tare da maƙarrabansa, a kofar aka hanasu shiga, aka rufo Safuwan kuwa ba surutuba haka ya koma gefe ya zauna ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa ya ƙira Mummy. Bugo ɗaya ta ɗaga daga can tace"Abbaye ka dawo da Ruwaida gida mana, ai bazata iya ba wa yasan dawowarka ne." Cikin dakiyarsa da salon maganar sam bazaka taɓa gane halin da Ruwaida take ciki ba ya ɗaga masa hankali yace.
"Mummy please kuzo hospital yanzu haka ina kan aiki amman dole na barshi, Ruwaida ba lafiya...." ya faɗi yanajan dogon numfashi. Mummy ta zabura daga can tace" Subanallahi me ya sameta? Wace hospital? Ko can Well being clinic...?" Abbaye ya lunshe idanunsa ya jinjina kai yace"Eh Mummy wlh bansan me ya sameta ba, amman naji ta ƙirani da ikon Allah ina zuwa na ganta a sume." Mummy tace "Ok gamu har Abbanku yanzu." kai ya ɗaga ya tsinke ƙiran. Ya miƙe yana kai komo ya ƙira wayar Dsp ya sun sami Sale?? Dsp yace" Wlh yallaɓai bamu samesa ba a gidan da ya kwatanto mana, amman yanzu zamu gidan karuwar da ka faɗa mana..." Acp yace" No wannan barta nina zan haɗa mata tarko." yana faɗin haka ya kashe wayar kitt, ya laluɓo number Magajiya gwamma, yay dialing ɗin number tata. Tanata ringing ba'a ɗauka ba. Lips ɗinsa ya ciza ya tsinke ƙiran, ya koma ƙofar Emergency ya tsaya yana jiran fitowar dictor yaji meke damunta...A can Police station babu irin bincikar da basuyi ba, babu ko dabbar da ta shigo a boye, kome basu ganiba, nan take suka ƙira Acp suka faɗa masa sai jinjina kai yake cike da mamaki.
ɓangaran Gwamma kuwa, zaune take a tsakiyar karuwan gidanta tana busa sigari sai iya shege ake, ƴar libah na zaune kusanta nacin indomie. Gwamma tace"Wai ƴar libah Sale kwana biyu shiru ɗan iska tsohon najadu, wai har ƙiransa nayi amman yaƙi ɗauka." Ƴar libah takai spoon bakinta wanda ta lailayo indomie ɗin, ta tauna tayi fari da idanu, wata karuwa mai sunan Asabe tace"Shegiya ƴar libah kina bariki fa." ƴar libah tace" Ai kwananan zan faso gari mota zan fara hawa dan uwar masu ƙyashi." Gwamma tace"zanci kutumar ubanki tambayarki nake ina Sale?" Ƴar libah ta miƙe tace"Ƙarya kike tsohuwar kilaki ubana ba sa'an ubanki bane mai dattin hula wanda ya ƙyaleki kika fito yawon bariki tin da ƙuruciya gashi girma ya fara ba ɗa ba jika, wlh yanzu bazaki zageni na ƙyaleki ba, tsohuwar banza, kuma nasan inda Sale yake bazan faɗiba uwarki zai miki ƴar iska, to yanzu ɗan zaki ya girma." ta faɗi tana juyawa cike da tsantsar rashin kunya take tafiya tana girgiza ƙirji da mazauna. Gwamma ta waro ido waje cike da kunyar jama'a, barin yanda sauran karuwan suka cewa"Sai kinyi ƴar libah mai tashe kiyayi mai zamani." Gwamma ta miƙe tace" Narantse da Allah sai kinbarmin gidana ayau zakici ubanki baki san wacece Magajiyar karuwaiba ko...?" ta faɗi tana nufar ɓangaranta cike da ɓorin kunya. Tana zuwa ta ɗauki waya ta ƙira giɗaɗo, bugo ɗaya ya ɗaga. Tace"Baban shegu ni Ƴar libah zata tozarta, inaso kasan yanda zakayi kazo kacimin ubanta da sandar girmanka kamata fata fata yanda ko ruwa sai an bata, niko nai mata korar kare..."Giɗaɗo yace"Ke!! Gwamma ni ai nayi alƙawaƙin sai na kamo kurma ina nagama warkewa wlh banida ƙwari har yanzu ban warkeba, rass amman zanzo na gwada zataci ubanta." Gwamma ta kashe ƙiran tana dariya, nan taga ƙiran Acp har biyu ta ƙirasa jiki na rawa, amman kashhhh Network ya ɗauke bata samunsa.Ɓangaran Mummy Abbaye na tsinke ƙiran ta miƙe, islam tace "Mummy lafiya kuwa? Waye a hospital?" Mummy zatayi magana Abbah ya shigo parlon da sallama, ya fito daga masallaci. Mummy tace"Abban Taslim Abbaye ya ƙirani wai Ruwaida hospital ba lafiya kar zauna." ta faɗi tana nufar bedroom ɗinta. Abbah yace"Subahanallahi, me ya sameta? Yi maza ki fito muje to." ya faɗi yana ƙiran Ya'u direba yace a fito da mota. Widaad tace"Abbah zan biku." Abbah yace"Aa ku zauna."Fu'ad yace"To Abbah atafi dani..."Mummy ce tace"Bazaka ba ku zauna, islam ku kula sosai sai mun dawo."Islam ta ɗaga kai ranta sam babu daɗi. Fita sukayi tin daga nesa Ya'u direba yana cikin mota, yana hangosu ya fito ya buɗe masu mota suka shiga yaja ya nufi tamƙameman gate ɗin gidan, megadi ya buɗe masaya fice.
Can asibiti kuwa sosai babban doctor ke ƙoƙarin ceto ran Ruwaida kusan 30 minutes bata farfaɗoba, an jona mata na'ura amman banza kuma babu abinda take nunawa ga me da matsalar, kome nata normal na'ura ke nunawa, gashi babu wata alamar farfaɗowa ageme da Ruwaida, doctor yayi ƙokarinsa, har ya haɗa zufa ya ƙara jona mata wasu na'urorin.
Abbaye yana ta famar kai komo a kofar Emergency ɗin. Sai ga Nadeer sabida ya ƙirasa nan yake masa bayani shine ya taho. Isowa yay ya kama hannun Abbaye yace"My friend me ya sami baiwar Allan nan? Please muje ka zauna ai tsayuwar bashida anfani Allah zai bata lfy." ya faɗi yana janye da hannun Acp suka zauna saman kujeru. Abbaye baiyi mgn ba. Nadeer yace"Inaso Mummy ko baka faɗa masuba?" Safuwan ya kalli Nadeer yana ciza lips ɗinsa na ƙasa ya hararesa yace"Eh ban faɗa ba." Nadeer ya ɗanyi murmushi ya buga bayansa yace"Na gane ka faɗa Acp a rage jin kai fa ni dai ba ruwana Rahma zata zane mutum." Hannu ya ɗaga masa a hankali yace"Yanzu ba lkcn mgn bane, ina fama da ƙanwata ba lfy." Nadeer yace"Ƙanwarmu dai kuma matata ba." Safuwan guntin smile yay wanda ya fito da asalin ƙyan beautyfull face ɗinsa, dimples ɗinsa suka loɓa kafin ya kalli Nadeer ya watsar ya zura hannunsa cikin aljihu yana karkaɗa ƙafa. Doctor ne ya fito daga room da Ruwaida take, ya buɗe babbar kofar ya fito yana goge zufa. Abbaye ya miƙe cikin jarumtarsa ya nufo Dr sam bazaka taɓa gane yana cikin tashin hankali ba saboda taurin zuciya da yake da ita bai fiye fito da ɗamuwarsa ƙararaba. Isowa yay wajan Dr yace"Doctor ta farka ne...?" Dr ya bushi iska yace"Wallahi babu yanda banyi ba..." isowar su Mummy wajan ne suna magana da Nadeer shine yasa Dr ɗan dakatawa kafin yace"Kome normal ake nuna mani amman ana samun irin haka insha Allah zata farka..." Su Abbah suka iso suna tambayar Dr. " Dr lafiya me ke damun baiwar Alllah nan??" Dr Jabeer ya masu bayani. Safwan yace"Inaso ka kaini wajanta please." Dr yace "Me zaka iya mata Acp? kayi hkr zata farka." Haɗe rai Acp yay yace"Malam idan da yuwar hakan ka haɗani da ƙanwata kaji." Dr yace" Ok muje amman kai ɗaya dukan ku bazaku shiga ba." Abbah yace "Munji barshi ya shiga shi ɗayan." Doctor yana gaba Abbaye yana binsa a baya, har room ɗin da Ruwaida take...!😲Kut wai har na gaji😆😛😝 ~*Real Ladingo Ommu Fareesa😘*~
Amanar Hajiya Nandalee🤝🏻😻
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.