Chapter 26

381 11 0
                                    

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''




*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 26*

Leƙawa yay yaga su Widaad na gudu sun laɓe bayan Musaddiq, suna maida numfashi Aneesa kamar zata shige jikin Musaddiq sbd tsoro, Fu'ad kuwa ya rungume Naddeer yana maida numfashi.         Musaddiq yace“He meye hakan kuka wani fito da gudu kamar an koroku...?”  Bai ƙarasa mgnr ba yay shiru ganin Abbaye tsaye yana riƙe da ƙofar ya zuba masu fitinannun lumsassun idanunsa, yana watsa masu wani mugun kallo, fuskarsa murtike ya haɗe rai!!
                                Musaddiq ya buɗe baki zaiyi mgn Abbaye ya rufe ƙofar ya juya ciki.   Musaddiq yayi dariya yana tambayarsu“Me kuka masa ne haka, islam?”  islam tace“Uhmm Ya Musaddiq wlh ba kome, kawai fa mun shiga da sallama, yana waya shine muka jeru muna kallonsa ya gama wayar, mu gaishesa yana gamawa ya miƙe yana zaginmu, wai mun tsaresa da idanu kamar mayu.
                                                    Dariya Nadeer yay yace“To ina ita Ruwaida?”  Musaddiq ya kalli ƙofar room ɗin ya girgiza kansa.    Ruwaidah na tsaye ƙiƙam bata gusa ba daga inda take, babu ko ɗar na tsoro atare da ita.    Acp ya kafeta da fitinannun idanunsa, yana takowa wajanta, yana mamakin taurin ran yarinyar.
                             Dab da ita ya tsaya yayi kicin² da fuska, yace“Ke!! Waye sa'anki? Ina miki wasa ne?” Ruwaida taji tsoron kusancin da yayi da ita, da yanda yake mata mgn cikin kakkausar murya, sosai taji tsoro  ga fitinannan ƙamshinsa da ya baibaye mata hanci.
                                          Cikin tsawa yace“Ba mgn nake miki ba?”  Ruwaida a ƙufule ta juya tana ƙoƙarin ɓoye tsoronta, tayi kicin² da fuska, ta fara takawa da nufin barin ɗakin.  Wata fizga yay mata sai gata a gabansa, yana riƙe da hannunta, ya zagaye ƙugunta da hannunsa ɗaya, ya saki hannunta ya ɗago haɓarta ya zuba mata fitinannun idanunsa yace.    “Bani amsa ina wasa dake ne? Me ya hanaki guduwa?”  yanayin yanda yayi mgn cikin wata irin narkarkiyar murya, duk da yana nuna ɓacin rai amman voice ɗinsa yayi mata sweet sosai.   Kallonsa  Ruwaida tayi wanda ya haddasa mata faɗuwar gaba, ga wani irin shock da yajata, haɗi da wani irin shaukinsa da yake ɗibarta, ta cije, ta kauda kanta gefe, tana zumburo ɗan ƙaramin jajayen laɓɓanta gaba, ta fara ƙoƙarin janye hannunsa da yake riƙe da ƙugunta.   Sakin ƙugun nata yay, ya kama fuskarta da dukan hannunsa biyu, bai mata mgn ba, ya ƙura mata rikitattun idanunsa, yana ƙara kusanto fuskarshi dab da tata, haka zalika numfashinsu na neman gauraya waje ɗaya, duba da yadda fuskarsu take kusanci da juna, har suna shaƙar numfashin juna, wanda hakan yasa sukaji wani irin yanayi atare.      Ruwaida ta runtse idanunta, ta fizge fuskarta da ya riƙe ta fashe da kuka, ta juya da gudu ta nufi ƙofar fita.
                      Taku 3 yay ya damƙota ya shigar da ita jikinsa, ya zagaye hannayensa bayanta, ya ɗora kansa akafaɗarta yana shafa bayanta, ya matsa bakinsa dab da kunnenta cike da rauni yace“Amanata nine na taɓaki ko?” ya tambayeta yana hura mata iskar bakinsa gefen wuyanta zuwa ƙofar kunneta yana ƙara shigar da ita cikin ƙirjinsa, yana shafa bayanta, haɗi da bubbugawa cikin sigar lallashi.   Ruwaida ashagwaɓe cikin shasheƙar kuka ta ɗaga kanta, alamar “Eh” tana ƙoƙarin ƙwace jikinta, bai bata damar hakan ba, ya ƙarasa kai bakinsa dab da ƙofar kunneta cikin lafazi me daɗi yace“Oya shiru wasa nake miki, ƴar ƙanwata Beby Ruwaida.”  ya faɗa yana isar da bakinsa ƙofar kunnenta ya bata lafiyayyan kiss mai tafiya da zuciyar duk macan da akaiwa shi to an gama da ita.... Take kuwa Ruwaida taji tamkar Acp ya zare mata jijiyoyin jikinta, ta haɗiye kukan, haɗi da ɗan zabura kaɗan ta ƙamkameshi tana sauke ajiyar zuciya, tana tura kanta cikin ƙirjinsa tana jero tagwayen ajiyar zuciya.
                  Safuwan ya saki guntin murmushi yace“Ƙanwata kin iya rigima ko?" ya tambayeta yana bubbuga bayanta cikin muguwar dauriya, sabida irin yadda ƙirjinta suka tokareshi ga wajan harbinsa na ɗan masa zafi sbd matsuwar da ya samu. 
                   Kamar an tsikari Ruwaida ta ɗago da kanta, tana ƙwaƙwaɓe fuska ta fara ƙoƙarin janyewa daga jikinsa, ta sanya hannunta tana shafa gefen kafaɗarsa wajan harbin, ɗaɗɗage ta fara tana hura masa iskar bakinsa, tana shafa wajan, cike da sigar tausayinsa.   Guntin smile ya saki yace“Uhmmm bayan kin gama famamun ciwo zaki wani damu....”Kai ta girgiza tana ɗaɗɗage tana hura masa wajan tana shafawa da hannunta hawaye yana shatata kan kumcinta, tausayinsa ya kamata sosai.
                                    Acp idanu ya kafa mata ya riƙe kafaɗunta, yana faɗin“My Happiness ki nutsu fa, ni banajin ciwon kome...”  shasheƙar kukanta yaji tana ƙoƙarin karɗe room ɗin, ahankali ya furta“Oh my god.  Daga nan sai kawai Ruwaida ta jita ya cirata sama yana juyi da ita da yaren ( *Mali*)  yana waƙa yana faɗin.    _“Kanwata Ruwaida me rigima, yayanki ayanzu ya warke, bayada wani ciwo cikin jikinsa, ciwonsa ayanzu kukanki!!_  ya ƙarasa cikin jan dogon numfashi, bai sake mgn ba amman yaci gaba da juyi da ita yana shillata kamar beby ya kafeta da idanunsa.
          Ruwaida duk batasan me ya faɗa ba, awaƙar sai gata tana ƙalƙala dariya tana harba ƙafa ya sauketa so take tayi rawa.   Ganin ya sauketa yana dariya ta ko fara tsalle tana juyi agabansa tana tafa hannayenta cikin farin ciki, hawaye duk ya bushe mata akan fuskarta.
                         Tunda Safwan yake bai taɓa jin farin ciki ba irin nayau.  Hannunta ya kamo yana faɗin“Ya isa zaki gajiyarmin da kanki Kanwata.” ya ƙarashe zancan yana sanya tattausan tafin hannunsa yana goge mata busassun hawayen fuskarta, sai  murmushi take, yaja hannunta suka nufi bakin gadon, tana gunguni.  “Uhmmm-uhmmm.     Zaunar da ita yayi ya zauna ɗan nesa da ita, ya lumshe idanunsa yana shafa kwantaccan sajan fuskarshi.   Ruwaida ta kalleshi sai taji kamar ta taɓa sajan nasa amman ta basar ta ɗauki wayarsa ɗayar ta shiga wajan camera, ta matso kusansa ta fara ɗaukarsu salfie, idanunsa lumshe bai buɗe ba, ta sakar masa kukan sangarta.  Idanunsa ya buɗe ya lakaci hancinta haɗi da ɗalle mata baki yace“Banson rigima, Oya ɗauki na buɗe.”  dariya tayi ta masa gwalo, ta ɗora kanta kafaɗarsa, ta ɗaukesu.  Kusan kala 20 ta masu, ta shiga whatsapp ta kunna data ta turama kanta, saƙƙonni taga suna shigowa rututu ba ƙaƙƙautawa, ta fita ta goge pictures ɗin,na wayarsa tana dariyar mugunta.
                       Kwanciya yayi yana kallonta ya girgiza kansa yace“Oya ɗaukomin lemo me sanyi a fridge.    Wayar ta bashi ta miƙe ta nufi ɗan ƙaramin frudge ɗin.   Wayar shiga dannawa, Rahma ta faɗo masa arai, yay dialing ɗin numbert.   Tana dab da tsinkewa ta farka daga naunauyan baccin da ya ɗauketa, ta ɗaga da sallama, tana yamutsa fuska bakinta ba daɗi.   Acp yace“Wa'alaiki salam  my dear ykk? ya jikin naki hope yanzu bakyajin kome?”  Rahma cikin jin daɗin kulawar Abbaye gareta ta ƙara gyara kwanciyarta ta narkar da murya tace“My Qalbina naji sauƙi sosai, to kai ya kk fatan kana cikin ƙoshin lfy?”  Acp ya murmusa kaɗan yana yamutsa kwantacciyar sumar kansa, yace“Uhmmm kome lfy lau ga ƙanwarki tazo tana kular miki dani, tace na gausheki.    Ya ƙarasa yana fesar iskar bakinsa waje.   Rahma saida taji ba daɗi sosai, amma ta share tace“Naji daɗi Qalbi nawan, kace ina gaisheta.      Ruwaida wacce tana jinsa, taji ba daɗi amman ta basar ta ɗauko lemo me sanyi na gwangwani, ta ɗauki gorar ruwan Faro, ta iso ta zauna ɗan nesa dashi, ta buɗe masa lemon ta kama hannunsa ta ɗora masa, tana murmushi ta masa nuni ya gaishe mata da Rahma.   Ido ya kashe mata ɗaya, haɗi da ɗaga mata gira, yaci gaba hirasa, duk da ba wata mgn sosai yake ba,  yanayi yana kurɓar lemon.   Ruwaida ƙirjinta har wani irin harbawa yake, ta rasa duk wani farin cikin da ya bata ɗazu, kawai jurewa take tana ɓoyewa dan kar ya ganeta, tinda itama bata san meke damunta ba.  Gorar ruwan ta kafa bakinta, tana ta ɗilɗilawa cikinta, ta lumshe idanunta, sosai sanyin yake ratsa mata zuciya.   Abbaye yay saurin riƙewa ya amshe robar ruwan, yana hararata.   Kai ta langwaɓar tana marerece masa.       Baki ya ɗalle mata yana faɗin“My dear Ruwaida ta shanye bottel ɗin  water guda...”  Ahaka suka Musaddiq suka shigo da sallama.  Musaddiq na faɗin “Wato abun zabintace ko? Kana nan kaida ƙanwarka, mu ka hargitsa mana kanne ko?” Acp ya tsinke ƙiran yana shan ƙamshi yana hararan su Widaad.   Aneesa tace“Ya Safuwan ina yini ya jikin?  Islam ma ta gaishesa, da Widad, Fu'ad ya iso kusan sa yace“ Ya Abbaye nayi missing ɗinka, Allah ƙara sauƙi.”Acp ya rungumeshi yana tambayarsa karatu.   Ruwaida ta riƙe hannun islam tana mata nuni suje gida, shareta tayi aranta tana faɗin“Tunda kin gama soyewa ba.   Saida sukayi sallar magarib kafin su tafi, Ruwaida taƙi yarda Acp ya fahimci halin da take ciki, cikin walwala suka rabu.   Tin A mota take hawayenta aɓoye ko bayan sunzo gida bathroom ta shige taci kukanta iya son ranta zuciyarta na tafarfasa ta rasa dalilin wannan abun? ganin kukan bazai mata ba, tinda idan  an kamata tanayi batada wata hujja ko taƙamemman abinda zata faɗa ita dai tasan haka kawai takejin ciwon wayar da Acp yake da Rahma agabanta yana wani lallaɓata, wai batada lfy.  Alwala ta ɗauro ta shiga karatun alqura'ani mai girma akan Allah ya kawo mata
sassauci.

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now