part 1

278 11 2
                                    


Dukkan godiya su tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga annabi Muhammad (SAW)

Sumayyah Abdallah Khalil sunana ni hafaffaffiyar garin gwarzo ce,da ta ke karamar hukuma ce  dake qarqashin jahar Kano da sana'a ta maida mahaifina cikin birnin Kano bayan haihuwata da muke yanzu zaune a cikin birnin kanon unguwar Gandun Albasa mahaifina Malam Abdallah Khalil da mahaifiyata Hauwa'u nice diyar fari a gurinsu sai kannena Ahmad shine mai bina daganan Rumaisa,Khadija,Sadiq,Khalil da a yanzu shine karaminmu,mahaifina karamin karfi gareshi yadika yake saidawa ficis a kasuwar kantin kwari a gefen kasuwa da runfarsu take wani lokacin kuma zagayawa yake cikin kasuwar,tun tasowata dana soma fahimtar yanayin yadda rayuwarmu take na fara janye jiki ga duk wanda ya fimu karfi,haka burina na zama ma'aikaciyar jarida duk na ajiyesa gefe,burina yau ace na kammala secondary da nake yanzu SS1a government Girls Gadun Albasa na cikin garin Kano badan komai ba saidan hidimomi su fara sauki daga kaina,Mamarmu macace mai zurfin ciki koda garinmu mu kaje sam baza kaji ta fadawa 'yan uwanta babu ba haka zamu yi kwanakinmu mu dawo dukda kasancewar danginta ba masu kudi bane haka suke kokarin hadomu da kayan abinci dana sawa idan mu kaje,a gurin mahaifiyata na koyi boye sirrina zai wuya maganganuna masu muhimmanci na fadawa wasu musamman rayuwar da muke ciki a gidanmu,danginsu Abba kuwa babu laifi duk masu kudine sai dai suda Abban sam babu taimako idan mukaje gidajensu koda munje Gwarzo ko gidajen wadanda suke anan cikin Kanon babu kyauta tsakaninmu sai jifanmu da maganganu marasa dadi,nasani tun ina karama Abbanmu mai zuciyar neman nakanshi ne sai dai har yau Allah bai kaddara zaiyi arziki mai yawa ba,dukda kasancewar yayi karatu aikin ne garesa yayi wuyar samu,bazance Abba baida sa'ar rayuwa ba,tunda yanada lafiyar fita ya samo na kansa harma ya ishi iyalansa mu shida dashi da Mama suka kasance na takwas kawai abinda na sawa raina arziki ne Allah bai kaddara zai tara ba,irin yanayin da muka tsinci kanmu na hantarar dangi yasa muke zaune guri guda babu mai sha'awar zuwa dangi da gani har kannena,dukda kasancewar mu din talakawane amma sam ba muda kwadayi irin na wasu daga cikin talakawa kamarmu,kai idan bakazo gidanmu ka gani ba dan kaganmu waje tunaninka bazai baka mu talakawa bane sosai dukda bawai kaya bane masu tsada jikinmu amma kullum zaka ganmu kayan jikinmu wanke goge,da ya kasance aikin Mama tun ina yarinya har na girma na dora da yiwa kannena,haka batun abinci babu maiwa Mama korafin abinci a gidanmu musamman idan munyi baki koda munajin yunwar har sai sun tafi,dukda saimuyi watanni ba muga bakinba domin dai da masu kudi akafi harka a yanzu mukam idan anzo kudin mota ma bazaka samu ba,masu kudi kuwa sam indai ba haihuwa ba Mama tayi ba bamai zuwa gurinmu shima haihuwar baza'azo suna dawuri ba da duk dangin Abba ke hakan to mai za suci daga garemu,dan sanin kowane irin rayuwar da talaka yake cikin dangi bama sai an fada ba,Mama idan tayi maganar ba'a zuwa gurinta mamarsu takance
"Hauwa'u idan anzo nauyi za'a dora muku,kinsan 'yan uwanki suma ba karfi garesu ba wata da kyar zata hada kudin zuwa,kuma tana zuwa daga gareki keda Abdullahi zatace tana jiran nadawowa"
Jin maganar Gwaggo da Mama taji gaskiyace yasa ta hakura da batun son 'yan uwanta suzo gurinta,batun gidan da muke na haya ne ina tausayin Abba da yadda yake biyan kudin hayar da sai Mama ta hada da nata kudin da take sana'ar cikin gida gishiri,ashana,maggi,Omo da sauransu dukda kasancewar cinikin kayan jefi jefi akeyi dan yawanci unguwar tamu mazajensu ajiyemusu kayan abinci suke komai sunadashi idan ba abun ya kare ba kafin a siyo anan ale cinikin,wasu kuma da su siya gurinka gwara su tafi bakin titi su siyo

Batun kawa sam ni ba maison tara kawaye bace dan kawata daya ce wadda muka shaku ba laifi Halima Farouk  tun daga JS 1 muke tare da yanzu muke SS1 Halimace kawai tun farkon haduwarmu na fahimci tamkar rayuwarmu zata zo daya wannan yasa kawancenmu dorewa,kasancewar itama Haliman bawai 'yar masu kudi bace,bawai ziyartar Haliman nake ba dan da tazara tsakaninmu,sai dalilin auren da kanwar Abbanmu Aunty Asma'u tayi unguwarsu Halima take ganina shima nakan dade banje gidan Aunty Asma'un ba dan mijin da Aunty Asma'un ta aura mai kudi ne itama kuma Aunt Asma'un tana auren ta fara business har kasar waje take zuwa hakan yasa naja baya da zuwa gidanta danni banison shigewa wanda muke da tazara dashi ta arziki dan na girmama tawa rayuwar,kuma Aunty Asma'un zan iya kirgawa tun aurenta a Kano baifi zuwa biyu tayi gidanmu ba shiyasa nima naja baya da zuwa gidanta dan dama itama baso take aje gidantaba hakan yasa bana sha'awar zuwa,dan tun daga Gwarzo zatayi waya azo a tayata zama idan mijinta bayanan muda muke a guri guda sam bazaka ji ta kirani ba saboda kada na shafawa rayuwarsu talauci nafi yakinin dalilin da take hakan kenan

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now