23
Humairah da take ta barci a bayan mama tunma kafin a fara rigimar ta fara kuka mama ta sauketa daga bayanta,daga ita sai pant jikinta nan mama ta fara bata nono,Gwaggo dasu Aunty Zainab suka kalleta "lafiya haka Aisha ba kaya jikinta"
Gwaggo ta 'dora"ko Bata da lafiya ko wani abun ya ha'da ki da surikan naki gama dai ansaba,hala qannan nasa suka ci miki mutunci ke sakarai Kika kasa ramawa Kika taho mana nan ki tayar wa da mutane hankali,shiyasa sam banji da'din dawowarku nan ba kinacan asirinku rufe muma namu haka Atika Kuma na 'dan taimaka muku,da koda aka koreku kunje gidanta ai zatasan yadda zatayi a samo muku wani gidan ko a unguwar ne,sai abu ya faru a kasa tunanin da ya dace to kundawo nan din,in dukan kawo wuqa zasu miki nidai da sanina qannanki bazasu je ba,inma rigimarce dasun kada Miki da 'yar taji ciwo da paracetamol bazasu taimaka muku ba, wannan jarabbabbun mutane hukuma ma sunfi qarfinta ,haka suke rigimar su dukansu da surikansu da qannan miji da yayye su Mubaraka da Maimuna haka sukeyi danma sun ha'du da daidai su ne abun ke zuwa da sauqin wulaqancin su Kuma duk laifin surikan naku ne da basasan laifin 'ya'yansu"haka Gwaggo ta cigaba da sababi,
Ita dai Mama haquri ta bata da cewa"Mama ni bama dani suke ba da 'dan uwansu sukeyi shine ganin ko kar haushin ya qarasa qarewa kaina ya ce na taho nan tunda yara suna nan",mama da jajayen ido take cigaba da maganar,"Gwaggo wallahi na gaji da zama da mutanan nan ko a can ban tsira ba su barmu ma da talaucin dake damunmu da ubangiji ya sa kasancewar mu haka maimakon su tausayama na ,shine dalilin da Allah ya Samar da Mai ku'di da talaka saboda mai shi ya taimaki mara shi koda da shawara da kwantar da hankali ne,amma babu dukkansu ba mai taimakon mu sai jifanmu da mugun alkaba'i basu ba 'yan uwanshi hatta da iyayenshi,wallahi sainaji kamar na zube musu 'ya'yan ko kotu naje a raba auren nan,indai nice matsalarsu" ta qarasa maganar tana rushewa da kuka mai ban tausayi dan Mama abar a tausaya mata ce,cikin yanayin tausayi su Gwaggo suke bata haquri harda Aunty Zainab Gwaggo ta ce"inkin kashe aurenki Hauwa'u kikazo nan wa Kika bawa ajiyar dauke miki duk dawainiyarki su Sha'aban suma buga bugace kina gani ba wanda ko maganar aure ya Fara ma da ya dace ace sun fara shekaru tafiya suke tayi,kuma kinada tabbacin zasu kula 'ya'yan naki sun riga basa qaunartaki kuma bama kece basa qauna ba Abdullahi 'dinne basa so har su iyayen nashi,dan da suna sanshi murna zasu yi dake da Allah yasa ya samu yayi auren,ya auri matar rufin asiri ai ita mace a wajen miji kamar katanga ce,kuma daraja da haiba take qarawa namiji kamar yadda itama yake zamar mata,in bakaso matar 'danka ba ba kasanshi kenan matar rufin asiri,in kinga ana qin surika anawa ganin sai baqin halin nata yakai iyaka,shima ace tana munanawa 'dan naka shine kake qinta,amma dan surika ta ta mai sauki ce sai taje inda suke ko ta sauraresu za'ayimata,saidai ko fitsararta ta takai qarshe,ni yanzu su Jabir nawa suke amma ji nake kamar ko da kaina na samu ku'din da Zan aurar dasu na huta naji da su ommu da Zainab,amma su sunfisan 'daga ma 'dansu hankali bare ke kisa ran naki zai kwanta shine basa so ba ke ba"Jin maganar Gwaggo yasa ni fara magana"wallahi Gwaggo hakane basa qaunar Abbah ne kawai"labarin komai da ya faru ni da akayi komai zai iya cewa a gabana na shiga basu,ransu in yayi dubu ya 'baci haka suka cigaba da mamakin su Abbah Imran 'din amma Gwaggo fa'di take Abbah dukda haka bai kyauta ba da ya farfa'dawa Hajiya maganganu su Aunty maimuna da Aunty Asma'u ya kamata ace ya zanesu duk abunda zai faru ya faru zata fi jin ciwan hakanma ,Ni dai shiru nayi Mai faruwa ta riga ta faru,haka muka cigaba da labaran duk na gidanmu ne,bamu muka bar gidansu Mama ba sai dare har Abbahsu Mama Saida yadawo Gwaggo ta shiga bashi labarin abinda ya faru shima duk labarin gidansu Abbahn yana dashi ko tantama baiyi ba yasan fiye da hakan zasu iya ma dan Abbansu shi cewarshi harshi Abban namu sai ya samu warwara za'a tantance shi nashi halin dan zumunci yanzu yana samu zasu shirya shima ya manta aibunsu tunda 'yan uwanshi ne,itadai Gwaggo ta ce wa Malam anya kuwa haka zata faru kuwa,haka muka tattaro da su Rumaisa muka taho gida,da sallama bakinmu muka tura kofar gidan muka shiga a tsaye kofar dakin Hajiya muka samu Abbansu Abbah yana kallon kofar gidan da alama shigowarmu yake jira tsaiwar da tsumayenmu tayi kama hasken wutar nefa ya haska mana fuskarta shi da take cunkushe ba alamun fara'a
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.