8
Ana kiran sallar Azahar na farka daga barcin da bansan ya 'daukeni ba,da ambaton Allah na bu'de idona gami da 'dora idona tar a fuskar Halima da ta zuba tagumi hannu biyu tana kallona wanda nasan ba kallona take ba tunda har bata ji motsina ba,da Kuma maganar da nayi,tsabar tunani ta fa'da da nasan Halima akwai zurfin ciki,da kuma nuna damuwarta ga al'amarin kowa musamman al'amarin abinda take so,ta yiyu nice sillar taguminta ko dai wani abu daban,motsin da na qarayi yasa Halima a zabure ta kalleni
"Sumayyah har kin tashi"
Murmushi nayi Halima ba dai tsoro ba abu ka'dan zaka yi ka firgitata,ita ko fa'dama tsoro yake bata sai dai fa akwaita da fushi,ban bata amsa ba na dubeta
"Halima yaushe Kika zo ne?"
Kallonnata tayi ta kuma canza magana
"Kinga Sumayya ba batun zuwa na ba ki tashi ga abinci na kawo miki duk da nasan ba muradinki bane shinkafa da miya ne,dan Allah karkice bazaki ci ba,nasan da qyar idan kinci abinci kika kwanta,Habiba kina wasa da cikinki ina jiye miki ulcer ta kamaki"
Ta qarasa zancen da alamun tsoro
Banyi mamakin abincin da Halima ta kawanba da idan aka bibiyama shine dalilin zuwanta gidanmu da wuri haka gidannamu dan kuwa Halima macace mai kyautatawa duk wanda yake tare da ita,na rasa kulawar dangi amma na samu ta qawa,lallai Allah abin godiyane a kowanne hali bawansa ya shiga yakan kawo masa mafita,domin shine ya kawo min Halima a lokacin da na rasa kulawar dangina,bama ni ka'dai ya kawowa ba hatta 'yan uwana da iyayena duk ya kawo mana ita
Maganar Halima ta katseni
"Sumayyah dan Allah ki tashi kici abincinnan karya wuce,kular bata wani riqe zafi"
Murmushi nayi na miqe da cewa
"Bari na wanko hannuna da baki"
Daganan na miqe na fice daga 'dakin da Mama naci karo tsakar gida ta kalleni
"Hala yanzu Kika tashi wato Haliman bata ta shekinba da nace tana zuwa ta tasheki"
Murmushi nayi na ce
"Mama kema dai kinsan Halima bazata iya tashina ba,yanzu ma abinci tazo min dashi,ina tashi ta matsamin nazo naci".
Mama ta girgiza kai ta kalleni
"Sumayyah bansan yazan misalta qaunar da Halima ke miki ba da har muma ta shafemu,dukda Suma ba want qarfi garesu ba amma duk sanda ta samu saita tunkaroki,ta fahimci rayuwar da muke ciki fiye da danginmu,da su suka kasa fahimta,bansan da me zamu iya biyan Halima ba,sai dai kawai Allah ya biyata"
Na 'daga kai na ce
"Kwarai kuwa Mama dan yanzuma ta yiyu ko abinci bata ci ba ta tawo kawomin,saboda ta lura da wuya naci abinci na tafi makaranta da safe,nasan zai wuya ba haka za ta ce ba"Mama ta ce
"Sai kije kuci tare,karki shiga haqqinta da yawa, Halima akwai lura sosai,rayuwarta Mai burgewa ce"
Na ce
"Hakane Mama"Daganan na qarasa gefen banbum ruwanmu na 'dauki buta na wanki hannu muka da baki na koma 'dakin da sallamata,Halima ta amsamin na zauna kusa da ita da harta bu'de kular da qamshin miyar keta ta tashi kamar ansa kifi ciki,har zan fara ci,na dubi Haliman
"Kisa hannu muci Mana,inada tabbacin baki ci abinci ba kika taho kawomin"
Halima ta dubeni
"To fara ci ki ragemin,dan Allah karki sake magana kici abincinki kawai"
Bansake maganarba kamar yadda, Halima ta buqata na fara cin dadda'dan girki,da tunda Halima ta bu'de nasan zaiyi da'di saboda qamshinsa da tun kafin na fara ci na ha'diyi yawu,sai da naci na qoshi na ragewa Halim ta wanko hannu ta fara cin abincin da a lokacin qannena 'yan makaranta sun dawo,Ahmad da Rumaisa da Sadiq da Khadija da suka shigo a tare,kamar sun ha'da baki,Mama naji suna tanbaya abinci,sai dai ban sake jin mai Maman tace musu ba naji sunyi shiru da 'dai da 'dai suka riqa shigowa 'dakinmu suna gaida Halima suna kwasar kayansu suna fita da Ahmad a kofar 'daki ya tsaya suka gaisa yayi gaba saboda shi ganinsa yake babba kayan sa ma Rumaisa ta 'daukarmasa dan kayansa duk suna 'dakinmu kwana ne dai a zaure yakeyi,da idan ana ruwa sai dai yaje shagon da wani makwabcinmu 'ya'yensa ke kwana ya ra'ba ya kwanta,saboda yadda kwanon zauren gidannamu ke shata ta kamar me."Yanzu Sumayyah kin kyauta kinwa mutumin alkawari zaku ha'du yau amma ki cemin gidan Mama Atika zan rakaki,da nasan da haka wallahi da tuni nayi tafiyata,wannan ai abin haushine,kamar wadda bata zuwa islamiyya kice zaki sa'ba alkawari"
Na rausayar da kaina jin Halima ta Gama sababinta
"Dan Allah Halima karki ce komai a kaina kimin uzuri Mamace tace lallai sai naje Kena kinsan ba san zuwa nake ba"
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.