NA CANCANTA!
Na
Halimatu Ib Khalil
Wattpad@Halimatukhalil27..........
Suku ku na tashi gaba ɗaya kuma har lokacin kaina bai bar ciwon ba sai dai yayi sauqi mun samu ragowar tuwon jiya mun ɗunɗunma munci,ƙanne na da aka samu hutun term yau da ta kama monday duk muna gida,tunanin kuɗin da na ba Abbah da yaya Samir ya bani na shiga yi dan indai kam ya taɓa su zamu ga sauyi sai dai banji ya taɓa ta yiyu wani abun yake nufin yayi dasu dan indai ba'a juya ba to ƙarewa zasuyi bare ma ba yawa bane dasu sosai basu wuce dubu Ashirin ba a yadda na ƙiyasta nake jin kuma dasu za'a samar masa gonar da zaiyi noman dan nasan itama sai anbada wani abun,kowa a wannan lokacin yana fama da abinda ya dameshi,ina ma laifi in mun samu dukda zamu bada wani abu wani ko nawa zaka bashi bai yarda aci arziƙinsa ba ya gwammace ya aje gonar bai noma ba har damina ta wuce mutane iri iri gasu nan muna rayuwa a tare da su,Allah dai ya azurtamu da manufar alkhairi a zama mutanan kirki,saƙon da Mama ta aiko Rumaisa da shi wajena ya katse tunani na,cewa naje mu tafi ɗebo ruwa gidansu Malika haka na zari hijabi muka fice badan wai inajin ƙwarin jikina ba,dan dai ina cewa ga wata damuwata zan ja Mama ta tsareni akan damuwa na cireta Ita kuwa na ɗauke ta dole ce ko baka so sai ta ziyarceka,haka muka tattara kayan ɗebo ruwan muka fice,gidansu Malika muka shiga muka gaisa da iyayenta muka fara ɗibar ruwa banga Malika ba ban kuma tambaya ba,"can muka ji ƙarar buɗe kofar da nake tunanin nan ne bayin gidan da bucket ta fito jikinta 'daurin ƙirji ne da alamun ruwa a jikinta da yake shaida wanka ta fito ta kalleni da nasa Rumaisa da ja ruwan na tsugunna a gefe
"Sumayya ashe zaki shigo yanzu nake niyyar na shirya kafin na wuce inda zani na leƙo gidanku",nayi murmushi na ce"Eh kin ganni dai kaɗan ma zamu ja ruwan zaki iya shigowa ai"Malika ta dawo inda nake ta zauna saman bokkitin qarfen ta cigaba da cewa"kinga ba fa lallai zuwan naji labarin mai ya faru,zullumina kar ace gulma ta kawo ni, yara suka shigo suke faɗa"Ni dai kallan Malika nake kawai banjin ta cancanta na zauna bata labari haka dukda yadda naga alama daga ita har iyayen ta suna da kirki,amma sai naga kamar akwaita da sanjin zance ko dake da abu na faruwa bakasan dalili ba gwara kaji ba'asinsa yadda yake ko ka samu natsuwa kuma abune da za'a kallemu bahagon kallo dashi,amma saina ga lokacin ta sani baiyi ba na dubeta da canza zancen"zafa ki bushe fa kinzo kin zauna haka"Malika ta miƙe "Au namanta saboda zafi mah shiyasa"
Rumaisah bayan wucewarta ta ce"Yaya Sumayyah wannan Malika ɗin kamar munafuka wallahi" Nasa dariya jin abinda Rumaisah ta faɗa na ce "Ba wani munafunci son jin zance gareta kawai"
Rumaisa ta ce"uhmm aji daɗin bada labari ba ansan daga A har Z"na girgiza kai na ce"oh Rumaisah ai bamu tabbatar ba ai,kawai nafi tunanin tana cikin mutane ne da sunfi san suji labari daga farko har ƙarshe don hankalinsu ya ƙarasa kwanciya hakan ma kulawa ce nake gani"Rumaisah ta ajiya gugar gefe"gaskiya dai banga ma yarda da itaba kina gani saboda gulma bucket ta kafa ta zauna",Ni dai nakasa sanin a inda zan aje Malika ɗin,da haka muka ɗauki sauran ruwan bayan mun musu godiya muka fita, takalma dana gani ƙofar ɗakin Mama yasa ina aje Bucket ɗin na shige dan nasan baƙin namu ne na arziƙi ne waɗannan dasu Aunty Zainab ƙannansu Mama na ci karo a ɗakin Zainab ta kalleni kafin na ƙarasa zama "To zauna mutanan cell kai Sumayyah ƴan uwansu Abbahnku basu da kirki,ai yanzu muke tambayar Yaya Hauwa'u ta ce kuna ɗibar ruwa makwabta,gidan ma da ta mana kwatance gidansu Malika Tukur Bello ne ƙawa ta ce ma,a boko,"
Ni dai na zauna gefensu iyayen labari sunzo kuwa kafin na fara bawa su Aunty Zainab labari"Kai kadai bari Aunty Zainab mun sha cell jiya ashe labari har ya kai muku"
Omm Habiba ta kalleni"lallai Sumayyah ai yanzu mutum ake kiwo duk wani mutsinka a idan mutane yake kuma kaɗan suke jira,Yaya Jabir yazo da labarin nan,ni nama rasa mai kuka musu ma, wulaqanci ne kawai,kudai Allah ya kare ku sharrinsu" na ce"Amin" ,Aunty Zainab ta ɗaura "Allah ya kawo muku canji na alkhairi dukdan baku da shi ne,Allah shiyasa kuma ko a littafi ban ci karo da yanayin wannan zumunci naku ba uwa ɗaya uba ɗaya hakan ke faruwa,ko littafin Zumuncin Zamani banajin yakai naku labarin ƙunci dukda dai akan Zumuncin yake magana ai a wannan yanayin fa in fa bakada shi ba'ayi dakai karka ɗaura ko nauyi ne"Nanfa labarin littafin aka buɗe shafinshi su ne dai masu karantawar ni saidai naji labari,yadda muke firar ka shigo gidan zaka ɗauka su Aunty Jamila ne suka zo saboda yadda muke firar tare,yini sukayi a gidanmu kasancewar sunsan yanayin da muke ciki ko ƙorafi basu yi ba,har Abbah ya dawo da ɗan wani abun dafawar dai,sai da yamma sai ga Malikah ta shigo gidan nan ta shiga mamakin ganin su Zainab gidan bayani suka yi mata, nan fa fira ta ɓalle,Mama ta koramu ɗakinmu,nan muka cigaba da fira sai lokacin n ski jiki fiye da da Malika ɗin,sai dare suka tafi gida.Abubuwan yanzu sai nace sunyi sauqi ba kamar da ba Abbah ya fara sana'a saida kayan miya duk da ba wata riba musamman ko dan qaramin jari garesa ga gasu kayan gwari wasu duk ruɓewa sukeyi da cinikin ba duka kowa yasan yana saidawa ba a kofar gida yake zama,wani lokacin Ahmad a lokacin Mamah ta fara dafamin awara ina soyawa a kofar gida kasancewar layin mu babban layi ne muna dawowa islamiyya nake fara soyawa Malika kullum tana wajen ita da take 'yar fira hakan yasa itama mamarta tace ta dinga mata dankali da zaman da takeyi haka muke sana'ar mu asirinmu rufe,muna samu,batun Yaya Samir bama wani waya dashi ko yana kirana bansani ba dan wani lokacin kashe wayar nakeyi, tayi kwana biyu ma kashe babbar ce dai Ahmad yafi anfani da ita dan shi dama mayen waya ne,niko saidai nayi kallo ko karanta Novels da ita hakan yasa na maida Sim din da yke ciki a wayar,ganin ban fiya anfani da itaba tafi zama flightmode,Yaya Samir inashan faɗa wajenshi wai in dinga kashe wayata nace masa matsalar caji ne wai su Halima naga ya dace na kira tun dawowa ta bamuyi waya ba
Duk muna tare ɗakin Mama ni da ƙannena da ita yau gidan Aunty Maryam yayarsu ta tafi dubo jikinta bata jin daɗi kasancewar juma'ah ma yasa jin rashin lafiyar ta ta lokacin za'a jiqa wake Mama ta ce abari ayi gobe insha Allah tunda yau juma'a ma,Ahmad dake game shida Sadiq d Khalil a wayata su na kallah na ce"Ahmad bani wayar nan na kira su Halimah,tunda na dawo bamu taɓa gaisawa ba"Ahmad yasa game pause ya tsaidata ya miƙomin wayar yana cewa"Gaskiya Yaya Sumayyah baki kyauta ba"na amsa ina"toh yaxa'ayi Ahmad hankali ba kwance ba bari na kira dai"duka nayi rashin sa'a wayoyinsu a kashe,
Na miƙa masa wayar "cigaba da game ɗin ka ba sa'a duka wayoyinsu a kashe suke"amsa yayi yana cewa"yawwa niko Yaya ana yawan kiranki da wata number idan wayar na wajena ganin baƙon number yasa bana faɗa miki sai jiya ne ma na ɗaga akace ke ake nema nace bakya kusa da wayar shine yace mai kiran in kindawo na ce Hamid ya kira"
Tunma kafin yakai ƙarshen zancen nasan Hamid zai faɗa dan Yaya Samir munfi gaisawa a ƙaramar waya tunda nace masa Ahmad yafi anfani da babbar da ɗaya sim ɗin shi ko Hamid number na ɗaya gareshi,na dai kawar da tunanin na ce ma Ahmad "Malam Hamid ne fa ,da ya mana service a makarantar mu", Ahmad yace "Ok naganeshi wanda kuka haɗu a Katsina kwanaki har Abbah Hashim ya dokeki akansa"na ce "Eh shine fah"Ahmad ya ce"lallai ai Yaya kwarya bin kwarya take tunda kikaga haka dagaske masu kuɗi ne,gwara ma karki saurareshi,dan kayan saiti ma complete Abbah bashida shi saidai a dangin Mama ayi karo karo" na ce "Hakane kam ,kawai inya ƙara kira kace masa wrong number ne ko kaƙi ɗagawa, kawai a rabu lafiya,Allah ya bani daidai dani"
"Haba Yaya Sumayyah yana sanki Allah uncle Hamid Kuma yanada kirki,ba lallai suyi mana yadda su Abbah Hashim sukayi ba ,tunda wasu keyi masu kuɗin ba duka suka taru suka zama ɗaya ba"Rumaisah ke wannan zancenHarara na galla mata rai ɓace na ce"Banza sakarai dake nake magana ,in Kuma kinga ban kyauta ba kije ki auresa tunda kinfini sanin waye Hamid ɗin"Tsaki na mata nama tashi daga wajen Rumaisah ta na cewa"Allah ya baki hakuri"ko takanta banbi ba na ma shiga ɗakinmu na ɗauki hijabi na shige gidansu Malika da mukai matuƙar sabo yanzu, tana yanka dankali da zata fitar na sameta.
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.