37.....
Gefen Mama nake zaune ina matsar ƙwalla gami da tunani mabanbanta da na ɗade da nasabarwa kaina dasu tun lokacin da Mama ta fara rashin lafiya mai zafin gaske kuma yau sati guda kenan dole na sallamar da zuwa islamiyya bokon ma karatun bana ganewa tunanina na wajen Mama dafa awarar da komai ninakeyi,A baya muna ganin farkon zazzaɓin nata da tasha paracetamol ya wadatar hakan yasa ko su Gwaggo bamu faɗa wa ba har saida mukaga paracetamol ɗin ya ƙare babu sauƙi Ahmad yaje ya sanar mata,maganar Gwaggo ta katsemin tunanin nawa
"Yanzu haka zaki zauna,ciwo fiye da sati ba a asibiti ba wani magani babu abinci takamaimai da zaki ci haba Hauwa'u,shine dalilin ƙin faɗa min ɗin kenan?"Cikin muryar ciwo naji Mama na cewa "A'a Gwaggo ba Sumayyah ta baki labari nasha magani ba sauƙin ne dai ya kasa samuwa"Mama ta ƙara sa maganar tanajan nishi
Gwaggo da yanayin damuwa tare da fusata ta ce"Dama ina zaki ji sauƙin da wani paracetamol tuni ciwo a jikinki yaci ya cinyeki daga ke har yarannaki gakunan a fukace a wahale,aini yanzu duk na gano gaskiya mijinnaki ne baya ƙaunarki shi ya akai bai koma haka ba iye?"
Hawaye nakejin na zubomin daga soma jin kalmomin Gwaggo,lallai itama ta kai ƙarshe wajen zafafa
"Gwaggo wallahi yanasona shima baki ga yadda ya koma ma ba laifin na wajen ƴan uwansa"Mama ce mai faɗin hakan cikin wahala hawaye nabin fuskarta
"Rufemin baki wallahi kona taso na make bakin naki,da bakisan ciwan kanki ba ki kwana da yunwa ki tashi da ita wanne ciwone bazaiyi nasarar kamaki ba da nayi zaton abun na mutuncine,yanzu ina muke da arziƙin kaiki asibiti a wannan yanayin dubunnai nawa za'a cajemu shi garemu ko wani muka bawa ajiya"
Sai yanzu na sa baki tare da cewa"Gwaggo Abbah ya tafi samo kuɗin ai"
Gwaggo cikin tsawa ta kalleni tare da wurgamin harara
"Ubanki zai basa kuɗinko,ya gama yawan ciranin nashi bai samo komai ba iyayensa ƴan uwansa sun koresa wa kike tunanin zai basa,Ni dai takama naje mu sami rance azo akaita asibitin,taji sauƙi kuma a rabata da ubannaku mara zuciyar neman na kanshi na gaji daganin ɗiyata cikin wannan tashin hankalin na yau daban na gobe da ban"Gwaggo na gama faɗar haka ta miƙe ta fice fuu kamar iska ko waigomu bata yi baKuka na kife kaina a jinyoyina inayi muryar Mama ta dakatar da shi tana cewa"Kingani ko faɗan Gwaggo nayi gudu yasa nace karku faɗa mata gashinan kun faɗa ai kunji daɗi"
Hawaye na goge na kalli Mama"To Mama ya zamuyi ai gwara su sani ɗin duk abinda zai faru yafi zuwa da sauƙi" bata bani amsa ba hakan yasa na ɗauki mafici na cigaba da yi mata fifitar da ita nakeyi Gwaggo tace na bari ta isa
Sallamar Rumaisah naji tare da kukan A'isha da ta ɗauke ta ta fita da ita tun ɗazu dama da kukan aka fita da ita gashinan an dawo dashi,kuma Mama ko Nono bata iya bata kwana biyu sai dai mu dinga ɗinkiramata ruwa gashi bata isa a fara bata ko koko ba itama duk ta rame dama ba wani ƙoshi a tare da ita,katse tunanin nayi jin Muryar Rumaisah
"Yaya wallahi taƙiyin shiru na rasa ya zan mata tana barcin fa ta farka ta ci-gaba da kukan,Gwaggon tazo kuwa?"
Cikin yanayin fuskar damuwa na ce"Eh tazo,ƙara ɗebo ruwa mu bata ɗin ko zatayi shiru"
Miƙomin ita tayi ta fita,na soma jijjigata ko zatayi shiru amma kukan take tsandarawa,Rumaisa cikin saurinta ta dawo da ruwa a hannunta a ƙaramin kofi ta miƙomin tana cewa
"Kingani ko bazata yi shiru ba yarinyar nan"Bance komai ba na amshi ruwan na soma bata tana sha sau ɗaya sau biyu ta zubo da shi ta cigaba da tsanyara kuka da nake jinsa har raina na rasa dame zanji
"Kawo ta na fita da ita tsakar gida na lallasheta karta damu Mama, amma wallahi yunwa take ji"Rumaisa tayi maganar da miƙo hannu ta amsheta ta fice
Mama na kalla idanta biyu amma ba damar magana ita tasan irin ciwon da ke damunta
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.