26

30 6 0
                                    

NA CANCANTA!

Na
Halimatu Ibrahim Khalil
(Halimatu Khalil)
Wattpad@Halimatukhalil

Note!
Ba true life story bane suna da gari duka arashi ne wanda yayi dai dai da labarinshi ko na wani daya danganceshi ,suyi haƙuri ba da niyya bane.

Har yamma gaf da magriba muna cikin cell ɗin,ba wanda ya waiwayemu,banjin Mama tasan tsaremu akayi ba,ina cikin cell din na ga shigowarta ita da Abbah Musa da kana ganinta zaka san bawai a hayyacin ta ta shigo ba tanbayarsu aka shiga yi "lafiya",nan naji Abbah Musa na labarta musu wajenmu suka zo wani cikin police ɗin da a lokacin da muka iso ban ganshi ba ya ɗauki file da case namu yake ciki ya karanta ya kalli su Mama"kunga ku zauna ai case ɗin ba wai babba bane sai naga duk rashin fahimta ne ma,yanzu in kuna da number ɗin yaron ku kirashi" yanayin yadda yayi maganar na fahimci wannan police ɗin ba shida damuwa

Mama ta share hawayenta ta fiddo wayoyi biyu hannunta tawa da ta Abbah da nasan kayana ta bincika ta nemo qaramar wayar tawa da ban fara amfani da ita ba,ta nunawa police ɗin"ka ga wayar nan ta Sumayyah da Abbahnsu ɗin ce tunda suka taho nan nake kiran Samir ɗin bana samu"

Ya girgiza kai ya sake duban Mama"ki sake trying Aunty ko za'a samu ta shiga jin lafiyar yaron ce zata fiddasu banji zasu yarda a bada belinsu" ,jin haka Mama ta sake ɗaukar wayar ta kirasa ta wa ta raruma ta danna tasa a kunne a loudspeaker ta sakata cikin rashin zato ta shiga number ɗin sai aka katse ,Mama ta ɗago tace"Ta shiga amma an ka..."bata ƙarasa maganar ba kiransa ya shigo, Mama da hanzari ta ɗauka ko sallama bata yi ba ta fara"Samir kana ina ne muna ta kiranka bama samunka dan ka kira Abbanku ka sanar masa inda kake hankalin kowa ya kwanta"kasancewar loudspeaker ta sake danna wa naji Muryarsa yana cewa"Ummi Hauwa'u ki faɗa min maike faruwa dan Allah,ina ita Sumayyah ɗin"Mama ta ce"Dan Allah Samir ka fara kiran Abbahnku ka shaidamasa kana lafiya" yana ƙoƙarin sake cewa"Toh amma Ummi...",Maman ta katse shi "dan Allah Samir kayi abinda na ce maka hankalin kowa ya dawo jikinsa"daganan ta katse wayar"Mama da sakin murmushi ta furta"Alhamdulillah"Abbah Musa ya kalleta ya ce"Hauwa'u kinji wani abin mamaki ga yaro ya amsa waya hankali kwance shi baisan da faruwar komai bama,amma ana neman wulaƙanta Abdullahi har abun yayi tsamari haka",ɗan sandan da bai gama fahimtar komai ba ya ce "To yanzu dai Alhamdulillah tunda an sameshi a waya Allah ya tsare gaba bari na shiga ciki na sanarwa da dpo ɗin a kira su suzo da wuri dan kwana cikin gurin nan sai dolen dole dan yanzu ma nasan zai sa a fiddo su" su Mama suka ɗaga kai"Mungode Allah ya saka da alkairi" da haka yabar wajen Mama da Abbah Musa suka cigaba da tattaunawa can sai gashi ya dawo yake sanar da su Mama DPO zai kira su Abbah Hashim yanzu a waya azo a qarasa maganar case ɗin ya wuce,sai da Abbah Hashim ya dawo, danshi kaɗai ya dawo sauran nafi tunani daya kwasosu sun tafi gidanjensu,dama Aunty Luba ita ban da ita dukda bata da mutuncin itama amma mijinta bai cika barinta unguwa ba,sai sannan aka fiddomu cikin cell ɗin,da sai gaf da Isha yazo nan ya fara cewa musu yaronsa ya kirashi ɗin ,anan aka kashe maganar sai kuma iyakar da Abbah ya nema da Abbah Hashim ɗin haka sukayi baran baran kamar basu fito ciki ɗaya ba Abbah ma yayi haƙuri da shi a dai yadda ya daɗe yana nunawa

Abbah Hashim ya kalli Abbah da sauran mutanan wajen kafin ya cigaba da magana"iyakata ta ƙarshe da kai Abdullahi ka raba ɗiyarka da ɗana dan ko zai mutu ba aure bazai auri wannan ƴar iskar ƴar taka ba, yaron da suke sheƙe ayarsu da ita tunda na masa zancen Fatimah bai sake neman mu ba"

Abbah da kallo yabi Abbah Hashim"Ai tunda ka nuna ga abinda kake so ni kuma bazanyi ba,kaje ka cusawa ɗan ka halinka firstly ka nuna isarka akanshi,amma ni bazaka nuna min isa akan hakan ba zumunci shi in yaga zaiyi damu bazan Koresa kona ci mutuncin sa ba yadda ni kama tawa ,lalacewa kuma da kake kallan ƴata lalace take da ɗan ka suke lalacewa amma kuma har yanzu basu taka ƙafarka ba ɗaga ƙafarka ma basuyi ba, kuma maganar yaro da kake yi yaga iskancin da ɗan ka ya koyamata kazo da wanda yafi nasu,dan nayi imani a yadda tunaninka yake akwai matsalar hankali tare dakai ko akwai cutar raina abinda ubangiji yabaka ga cutar hassada da baka ganin samunka saboda rashin godiyar Allah sai talakan talau shine kake ganin yanada samun da zaka tsaya jayayya da shi"

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now