33

30 5 1
                                    

33

10:00am
Misalin ƙarfe goma na safe da duba agogon wayata kenan na fito yin wanke wanke,na kwanukan suyar awarar safiya da mukeyi

"Assalamu alaikum kamar daga sama nake jiyo murya mai kama data Aunty da ban tsammanin sake zuwanta ba guri kusa sai dai abun mamaki jiya akayi abun yau ma gata ta dawo jinjina soyayyar da Aunty ke yiwa Mama nakeyi dana kasa ganin wadda Mama ke yiwa Aunty a yanzu harta a kwayar idanunta ta rikiɗar dasu

"Wa'alaikumussalam , mene ya kawoki gidana? karo na biyu nayi zaton mun kammala maganar da zamuyi ko?"Muryar Mama na jiyo na ɗago da kaina na dubeta tsaye kofar ɗaki da tabbacin sallamar Aunty ya fiddo ta daga ɗakin inda Aunty take ta nufo

Aunty na maida idona  kallo da take ƙoƙarin ƙara sowa ciki itama sai kuma taja ta tsaya ganin ƙarasowar Mama inda take
"Nazo naji dalilinki da yasa kika hana Ahmad zuwa gidana bayan iya haihuwarshi kikayi amma Ahmad ɗana ne halak malak, inke ƙinƙi tayina bai dace ki hana ni na rayu da yarana ba" da raunin murya Aunty tayi maganar

Mama murmushi tayi da na tabbatar na takaicine "indai kin yarda ɗanki ne da sauran yarana bai kamata ki zowa da mahaifiyarsu magana akan mahaifinsu ba inba mai daɗi ba ya dace ne ki taimaketa ta kowacce fuska nasan zaki iya Rumaisah,ki bawa uban ƴaƴana aikinyi ko taimakonsa da jarin da zai riƙemu"

"Kwarai kuwa Rumaisah AlMustafa Matazu zata iya komai ga Hauwa Ibrahim Alhassan sai dai banda samarwa mijinta wani abu a rayuwa duba da yadda kika bani labarin ƴan uwan mijinki,taya zan samar masa bayan ga jahilcin tunaninsu akanki kiyi nazarin me zaije ya dawo zasu hanashi yi miki komai idan suka janye nasu bakisan alaƙar jini ba ne Hauwah,Rumaisah bazata iya ba"

"Dan Allah Rumaisah karki rinjayar dani da bahagon lissafinki mara anfani ki canzamin tunanina ki yaudareni"

"Idan kowa zai yaudareki ki cire ni a ciki ki tuno wacece ni mana,ba wai wannan maganar takawoni ba ki bar Ahmad ya cigaba da zuwa gidana dan Allah,na  kwana da jin babu daɗi a raina a game da abinda kikayi"Aunty ta ƙara sa maganar tana haɗe hannunta duka biyu alamun roƙon Mama

"Dan Allah Rumaisah ki tafi ki barmin gidana banasan kowanne taimako dama ƴan uwana na jini basu da abin taimakamin dashi da yau na tabbatar da girman alaƙar jini dabance, kawai ina zaune lafiya da mijina da yarana kinzo min da wasu lissafin da zuciyata ta gaza a ɗaukar su"Mama ta ƙara sa maganar da take ƙoƙarin barin wajen

"Ehem"gyaran muryar Abbah naji da hakan ke tabbatarmin ya daɗe tsaye wajen hawayen dake kwararrarmi suka ci-gaba da zubomin abinda nake gudu saida ya faru Abbah yaji halin da ake ciki da nasan hankalinsa zai ƙara tashi

"Hauwa'u tun ba yanzu ba na fahimci cewa ƴan uwana sun daɗe da ɓata zama a tsakaninmu,nasan da ƴan uwanki nada wani ƙarfi da iko da tuni sun tilastamin na rabu da ke wahalar tayi yawa,karki kasa amincewa da ƙudirin ƴar uwarki akaina ba tare da kinsan gobena ba banasan rayuwarki ta faro ta ƙare a rashin jin daɗi kiyi tunani"

Mama dake ƙoƙarin buɗe baki tayi magana Abbah ya ɗaga mata hannu
"Karki ce komai naji komai harda na jiya ma,ba ni da yarda zanyi da ƙaddarata Hauwa'u iyayena sun kasa tallafata fa taya ƴan uwanki da masoyanki zasu jure ganinki a hakan ?,kibi shawararsu nasan ba zasu cutar dake ba,Rumaisah jinin jikinkice kullum ambatarta kikeyi a yanzu data nemeki da kanta ya dace ki sake tabbarwa da gaskiya take tare dake iya gaskiyarta ta faɗa miki kowama hakan zaiyi indai yasan wasu lamuran dake faruwa tsakaninmu"

Aunty da nake kallon yarda jikinta yayi sanyi lokacin da Abbah ya ƙara sa maganar da yakeyi
"Abdullahi ka gafarceni ba nufina na rabaka da matarka ko haifar da wata husuma tsakaninku ba, tunanina rabuwar zata fi muku zama alkhairi,saidai yanzu tunanina ya bani nice ya dace na haƙura da Hauwa'u da abinda ya shafe ta domin ta samu ta zama cikakkiyar uwa ta haƙura da mijinta ba dan komai ba sai dan goben yaranta,karki damu Hauwa'u zan tayaki aikata hakan zan bar miki rayuwarki har sai lokacin da kikaji ya dace ki nemeni bazan sake gaggawar nemanki ba bayan nasan kinada yaƙinin inda zaki sameni"takai ƙarshen maganar tana dafa Mama da hannu ɗaya ɗaya hannun kwallar idanta take gogewa

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now