36

25 4 0
                                    

36......

Haka na cigaba da zuwa makaranta tare da ƙarin mutunci dasu Maimunatu da sauran ƴan class ɗin mu wani lokacin da Malika muke tafiya dukda ba wani zuwaa suke ba yarda masu Wa'ec suka fara ragamar SS3 ta dawo hannunmu da tunda naje na samu har an raba temporary prefect kafin su fita a ƙara wasu ko a cire wasu ya danganta da yarda suka tsara,su Rumaisa ma da Khadijah makarantar ɗaya mukeyi sai dai tafiyar tamu wani lokacin tana banbanta,Soyayyata da Juraid kullum ƙaruwa takeyi a zuciyoyinmu jiran na shiga SS3 yakeyi ya turo gidanmu idan na tuna wannan ina sake jin daɗi Maimuna da Hafsah sai nace sun mayemin gurbin Batul da Halima ga kuma Malika da take da babban matsayi dukda batakai Halimah ba saboda ita ɗin na fara san.

******
Yoghurt ɗin da ya rage guda ɗaya da Juraid ya kawomin na rarumo da yake gefena na ɓalle murfin jikina na kyarma a baki na kafa gorar ban cire bakina ba sai da na shanye tas na mayar da gorar hannuna ina bubbugawa wanda yayi saura kamar tsohuwar mayya,ko dake ɗin indai yunwa tayi yunwa inka samu abinci ka kanyi kamar mayyen sai da na gama aikin da nakeyi tas da roba nayi Hamdala ina sake neman tsari daga yunwa dan ko ba abinda bata sanyawa duk juriyarka da ita saika gaji da zama cikinta ka nemi abinci ta kowacce hanya dan saita zamarma musababbin wahalar da baka iya tunani hausawa suke mata kirari da yunwa ba ƙanwar uwa bace dan ko da ƙanwar uwace da tayi maka rangwame gami da alfarma dan ta zama wakiliyar uwa mahaifiyarka, ƙoƙarin Mama nake gani yadda take juriya da takura cikinta ta bamu muci ta haƙuraa mafi yawancin lokaci dukda ta fimu buƙata sai dan ƙarin rufin asirin A'isha ƙarama ce da ko ta kai wata ko huɗu ne sam wannan jinƙan uwa ga ƴaƴanta Mama bazata iya aiwatar mana ba bansan iya lokacin dana ɗauka ɗauke da tuƙewar wannan tunanin nawa ba ,Har sai da ƙarar ringing na wayata ya fargar dani nayi saurin dawowa hayyacina sa'ata guda ma yau ɗin Lahadi ce,sunan nata da na gani yasa ni yin murmushi ƴar halak ɗince Halima dukda ban ambaceta ba amma tana da halaccin da za'a kirata da kai tsaye ƴar halak ban ɓata lokaci ba na ɗauki wayar

"Assalamu alaikum"shine na ambata

"Wa'alaikumussalam,ina kika shige ne kwana biyu?"cewar Halima

Murmushi nayi Tamkar tana ganina daga nan na furta"Bakisan nayi zazzaɓi bane ba ma wai?"

"Ke kiji ƴar rainin hankali wazai faɗamin kuma, nakiraki washe garin ranar da ake taron nan wayarki a kashe nasan ,yanzu ya jikin naki?"

Na yi murmushi na ce"Na samu sauƙi,a ranar da mukayi wannan wayar na fara zazzaɓi"

Halima da muryar tausayi ta ce"Allah ya sa kaffarane,Allah yasa ba jiya a yau kuke ba har yanzu hankalina ya kasa kwanciya sosai dukda bakimin bayanin komai ba"
"A'a babu komai fa ai yanzu Alhamdulillah,ki bani labarin ya taron ya gudana mana"

"Uhmm kin faɗa nasani domin ki kwantar min shikenan dai ai na baki labari dai zaƙwaƙuran ɗaliban makarantar baki ga manyan kyautukan da aka..."

Banjira takai ƙarshen zancen nata na katse ta da cewa"Dan Allah fa waye ya raba musu kyautukan?"

Tsaki Halima tayi tare da cewa"Matsalata dake fa baki cin ribar zance wallahi,waye zai raba kyautar inba mai makarantarba tunda shine yazo taron,ke harda kema a bawa kyautukan shine fa muka riƙa kiranki a ranar bata zuwa,ana gama faɗar ki sai Ahmad da Rumaisa"

"Kinga Halima kinsan banasan kinamin ƙarya gaskiya"nayi maganar ina jiran amsarta dan ni kam ba wai yarda nayi ba   duk da nasan bana cikin sahun daƙiƙai amma a tunanina ban cancanci har a kira sunana a babban taro ba duba da akwai mutane da yawa da ko ba ajinmu ba suke gabana,maganar ta maidoni tunanin da nake yi

"Wato na saba ƙarya sababbiya ko?,shikenan ki samu wani ya baki labari"

Cikin muryar lallashi na ce
"Dan Allah kiya haƙuri haba Halimatussa'adiyya"

Tsaki ta yimin "Ai na gama magana kuma dama baki nemana ai,ki samu Batul ta ƙara sa miki labarin,ita da kike ɗaukar har shawararta"

Tana gama faɗar hakan ƙit ta kashe wayar,cire wayar nayi a kunnena na riƙe ta a hannun ina tunanin rigimar Halima wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa ina zan lalubo kuɗin da zansa a wayar bare na kira Batul yaushe raban ma na gaisa da Batul bare har na nemi shawararta sanin halin Halima yasa ban aje zancen raina ba hanyar da zan kira Batul na cigaba da nema dan Halima ta sakamin ɗokin jin labarin dukda inada yaƙin litattafai zamu samu kyaututtuka tunowa nayi da flashing na Beep call da akeyi a MTN duk da ba ko yaushe yake zuwa ba,hakan dai nayi cikin sa'a suka turomin message ya shiga hakan yasa na ƙara yi baifi minti goma da yina ba ina ƙoƙarin tashi gurin naji ƙarar wayata da saurina na ɗauka da tsammanin Batul ce ina ko kallon screen na samu shaidar itace ganin sunan da nayi mata saving raɗau akan wayata hakan yasa nayi saurin ɗagawa ban jira sallamarta ba na yi saurin rigata gabatarwa

"Assalamu alaikum Batul ya kike?ya su Umma?"

A ɓangaren nata ta bani amsa da cewa"Wa'alaikumussalam Alhamdulillah,ranar taron Tahfiz ɗinku mun kiraki yayi sau ashirin amma bata zuwa"

Maganar da nakesan yi mata ta rigani farawa hakan yasa na bata amsa da cewa"wallahi sai dai matsalar network ranar ma banida lafiya kuma,yanzu ba jimawa muka gama maganar da Halima har taji haushi da zata bani labarin taron ta fasa"

Batul ta ce"Allah ya ƙara lafiya ai bamu sani ba,meya haɗaku ke da Halima ɗin"

Abinda ya faru tsakanina da Halimah kaf na kwashe na bawa Batul,Ina gama baiwa Batul labarin tayi ƴar dariya ta furta

"Kinga kyale wata Halima nan,kyautuka aka rarrabawa zaƙwaƙuran ɗaliban dan mai ginin makarantar ya raba da kansa ku dai da aka kiraku bakunan ba muga kyautukan da aka baku ba,ke har marasa fashi sai da aka bawa kyautukan nan kuma kuna ciki Allah kaɗai yasan meye a cikin jakunkunan nan"

"Wayyo Batul inama naje ni namaga mutumin nan nakeda burin yi ma"

Batul ta ce"Ke dai bari Sumayyah,ai mutumin nan yayi da duk masu kuɗi haka suke da anji daɗi matuƙa da babu sauran mai kukan babu a duniya,kinga a wajennan yarda ake yabanshi ance kyautar trillion ma indai yanadasu zai iya yi,ai ji nayi ina ma makarantarku nakeyi,dukda cewar na  bazata akayi,amma nasan tunda aka fara za'a cigaba dayi yanzu zakaga kowa ya ƙarawa dagewa"Da haka muka cigaba da taɓa fira da Batul mai cike da faarin  ciki

To be continued insha Allah

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now