45

44 5 2
                                    

Da yammacin ranar da aka sallamo Mama asibiti muna zaune ni da Gwaggo a ɗakin Mama fifita nake mata Gwaggo tana ɓallar magani zata bata,muka jiyo sallamar Aunty bamu ƙara sa amsawa ba ta ɗaga labulai ta shigo ɗakin

"Aunty Ina yini?"Nayi maganar ina cigaba da abinda nake

Aunty tayi murmushi daganan ta furta
"Lafiya ƙalau Sumayyah kina nan kenan,Inasu Rumaisah?,naji gidan shiru"

"Sunje ɗibar ruwa gidansu Malika"Na furta maganar a hankali

"Ok zasu haɗu dasu Jabir ƙila a waje"Aunty ta ƙara sa faɗin hakan da zama kusa da Gwaggo

"Gwaggo sannu ya mai jikin?"naji Aunty ta furta

Gwaggo tayi murmushi"Mai jiki tana ta ƙara samun sauƙi Rumaisah Allah dai ya biyaku da aljanna firdausi"

Aunty tayi murmushi"Amin ya rabb Gwaggo"

Gwaggo cikin muryar da take nuna kulawarta ga Aunty sosai naji ta ce
"Baku gajiya da hidimar hanya ba ɗazu ɗazu fa muka dawo kuma yanzu kun sake linkowa maimakon ku zauna ku huta kuma"

Aunty ta girgiza kai"A'a Gwaggo ai babu wata gajiya dama Abbahnsu Jabir yace mu zo akwai kayan da ya siyo na abinci da za'a riƙa dafa mata tunda ance da ulcer,sai kuma kawo A'isha"

"Oh ni Zaidu baya gajiya ko Jabir da Sha'aban iya abinda zasu yi kenan fa ɗawainiyar na yawa Rumaisah,Kuma maganar A'isha ba tun a asibiti muka gama ba zata zauna hannunki har ta sake jin sauƙi,idan sun barmuku ita shikenan"
Gwaggo ta ƙara sa maganar tana kallon Aunty

Aunty da take ƙoƙarin sauƙo A'isha a baya ta kalli Gwaggo
"A'a Gwaggo ba wata hidima duk abunda zan yiwa Hauwa'u ai ban faɗi ba ta cancanta fiye da haka kuma wasu ma ana yi musu makamancin wannan inaga ta jikinmu ta jikinmu ɗin ma Hauwa'u,Daddyn Jabir ɗin ne ya canza shawara yace kawai a dawo da A'isha ɗin gani yake kamar kunyarmu kukaji shiyasa kuka amince da ƙudurinmu,shine yace a siyo madara kawai a maidota"

Gwaggo ta girgiza kai tare da cewa"Ai Rumaisah i tunda taƙi karɓar Nono,kuma kin nuna tun farko kina sha'awar ta zauna wajenki ai shikenan ba muda idon da zamu kalleki mu nuna a'a ba idan mukayi hakan munyi butulci mai yawan gaske" 

Aunty da ta ƙara sa sauko A'isha daga bayanta ta ɗaura ta cinyarta
"Gwaggo gani nayi kamar zamu zalunci yarinya mu rabata da ɗumin uwarta tunda dai ta samu sauƙi nasan zata iya riƙon ta da taimakon su Sumayyah"

Gwaggo ta girgiza kai"A'a Rumaisah ai ke ma uwace ai matsala gagaruma tasanya mu yin hakan ba wai da ra'ayin san zuciyarmu bane,yanzu su Malama Habi (da Gwaggo take nufin mahaifiyar Aunty)ai ba zasu ji daɗi ba tunda gabansu aka aiwatar da wannan maslahar akan yarinyar nan"
Aunty ta girgiza kai "A'a Gwaggo ba wani abu da zasu ji suma sunyi tunanin tauye yarinyar da ga baya"

Gwaggo ta kallo Mama ta kuma kawar da kai"Rumaisah ki karɓe ta anan watarana ma ruwan da za'a dama mata madarar na zafi a dama madarar babu iccen ɗaurashi bamu da yarda zamuyi dole ko bake ba saidai a bawa ko Jamila ko Asiya ita tunda taƙi karɓar nono ɗinnan ita kanta Hauwa'u bata da ƙarfin kulawa da ita a yanzu,tunda an gama magana shikenan bazamu dawo da hannun agogo baya ba in mukayi haka ai bamuyi halarci ba"

Mama naga ta dafa Aunty a hankali naji muryarta"Rumaisah na baki ita halak malak indai kinaso dan na miki kyautar ƴa koda Sumayyah kika nuna kinaso nabaki zan baki bare ƴar da ciwon da nayi yamin giɓi da kasancewa da ita guri kusa banaso na zama uwar da kanta ta sani bata nemo masalahar ƴaƴanta indai Zaid bazai ƙi ba na baki ita halak dama ai ɗiyata takice ko ina nan ko bana nan"

Ni dai A'isha dake hannun Aunty nake bi da kallo ba laifi A'isha tana ɗan qara girma ba kamar sanda ta amsheta

Kayan da Aunty tace an kawo Jabir da Ahmad  suka yi sallama suna shiga shigo dasu ɗakin Mama ɗin taliya macaroni, madara,milo komai katan biyu sai ƙaramin buhun shinkafa

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now