NA CANCANTA!
Na
Halimatu Ib Khalil
Wattpad @Halimatukhalil25......
3:00pm da misalin ƙarfe uku na rana sallamar da naji kofar gidanmu da nake tsugunne gefe daya ina wanke hannu na da bakina kasancewar tuwon dawa miyar kukar dana gama ci kenan lokacin,da yau ma da safe ba mu samu karyawa ba sai ruwa da muka dinga sha Khadijah da Khalil ko kwanciya sukayi shame shame dan ga yunwar daren jiya ga shi da safen ma ba'a samu anci wani abu ba,sai da Abbah ya lallaɓa ya fita sai gashi da dawarshi kwano uku da kayan miya harda kuka da Maggi duk Abbah Musa ya bashi,ya ce masa kafin ya ɗan bashi jari ya fara juyawa yana ƴar wata sana'a kafin daminar tazo a fara noman dan noman ma sai da kuɗin tunda ba taɓa yi yayi ba yanzu zai fara ,Abbah Musa ma ya na da kirki sosai a cikin abokan Abbah na nan yafi sauran taimaka mana,ko da muna ƙanana muna zaune a Gwarzo haka Mama take bamu labarin Abbah Musa,kuma yanzu dawowarmu bai gaza ba dukda shima famar yake amma akanmu kam Alhamdulillah zai ce tunda har yanada ƙarfin halin taimaka mana,kasancewar shi akwai zumunci ko Abbah bai zo ba wajenshi shi zaizo dalilin hakan ma tasa yafi sauran abokansu Abbah fahimtar halin da muke ciki,Abbah Musa mutum ne gaskiya yana aikin gwamnati da noma dukda koyarwa yake albashin ba mai yawa bane amma Alhamdulillah
Sake jin kwaɗa wata sallamar yasa ni dawowa tunanin dana faɗa gaba na naji yana tsananta faɗuwa nan na fara addu'a,la'ilah ha'illa anta inni kuntu minaz zalimin,haka na cigaba da ambata a cikin zuciyata ina addu'ar Allah yasa kada maganar Aunty Asma'u ta tabbata kada Abbah Hashim yazo tuhumar Abbah ɗan shi,a tafi hukumar da Aunty Asma'u ta anbata daga nina qaramar matsala ce amma saina ɗauka tunda ana san wulaƙantamu kotu ma sai a tafi hawaye naji masu ɗumi na sauka akan fuskata na rasa gane laifinmu kawai dan muna talakawa sai a dinga wulaƙantamu abin har hukuma mah,ace tana ƙoƙarin shiga ma wannan rayuwa wacce iri ce mukeyi a cikin ƴan uwan mu,abin ya wuce muke ganin ana ƙin mu a'a abu ne da duk mai hankali zai yi wannan shaidar ko da yana zullumin faɗa to a ranshi tabbas zaiyi wannan tunanin,na rasa gane ta ina Maman take da laifi,kasa matsawa nayi daga inda nake a tsugunne nayi dan yadda gaba na ya cigaba da dukan uku uku,ga wata sallamar an sake dokawa jin sallamar har karo na uku najiyo Abbah da ga inda nake yana magana
"Ah'a wannan sallamar fa nasan dai ba Musa bane,Ahmad taso kaje ka gani waye,danni kam yanzu ina tashi daga abincin nan na ƙoshi kuma"Ahmad da shi yama rigani kammala ci shirin tafiya islamiyya ma ya fara dan uku tayi harma suna neman makara ni ma Malika nake jira ta kuma cemin sai uku da rabi zamu tafi dan da muka shiga ɗebo ruwa ko wanka bata da niyyar yi makararrace dai danma farkon zuwa ne na biyewa shiriritar Malika ɗin,dukda dai yau rashin samun abinci yasa dole zamu makaran ma,Ahmad da banji fitarshi ba sai sallamar dawowar shi da yayi yasa na sake jin bugun zuciya ta ya ƙaru kasa amsa masa sallamar nayi haka ma su Mama naji Abbah yana ce masa
"Lafiya wanene Ahmad"
Amsar Ahmad yasa naji dum a zuciya ta na dafe kirji nah cikin inda inda naji Ahmad ya ce wa Abbah
"Eh...uhmm..Abbah...Ɗan sanda ne Abbah da kaki naganshi ya ce na faɗama kazo police station yanzu kai da Yaya Sumayyah,ana san ganin ku"A zabure na miƙe daga gurin da ni ke na nufosu
"Abbah ɗan sanda ni me nayi kuma"nayi maganar idona yayi rau rauMama ta ce"Mai kukayi dai zaki ce Sumayyah,shima Abbahnku ba abinda yayi musu kawai don a tozarta shi ne, amma ina zai kai Samir inda bai kaiku ba, talauci ai ba rasa imani bane"
Abbah ya cire hannu daga cin abincin ya dubi Ahmad ya ce "jeka kace masa muna zuwa yanzu"
Ahmad sai da ya fice ya dawo da dubenshi ga Mama ya ce"Hauwa'u ai a ganina ni ya dace su tuhuma ba Sumayyah ba,tozarcin yafi dacewa ya tsaya iya kaina yanzu da me garinnan zasu riƙa kallon Sumayyah"Mamah ta goge hawayenta "Bakomai Allah na tare daku kuma ya isar muku ku nemi agajinsa baya zalinci kuma ya haramta zalunci a cikinmu bayinsa kenan shi mai ji ne mai ganin zahiri da baɗini,nasan munyi kuskuren tura ƴar mu inda kai uban ta ba'a sanka a wajen bare saka ran za'aso jininka,Allah dai ya dubemu da niyyarmu" Abbah ya amsa da "Amin" niko kasancewata a ruɗe ko hijabi kasa shiga na ɗauko nayi sai Rumaisa ce ta ɗaukomin,haka nabi bayan Baba zugui zugui gaisuwar kirki ɗan sandan bai tsaya yayi da Abba yaja machine ɗin shi yayi gaba ganin fitowarmu,dana fi tunanin ko tunani yake Abbah zai nemi wani taimako daga gare shi bayan ga ubangiji da taimakon shi duk muke nema nasan a irin yanayin da ya ganmu ba sile ba sisi banjin zai iya taimaka mana koda yana da hanyar haka a dai yanayin dana ganshi da alama yana cikin waɗanda suka yiwa talakawa kuɗin goro na hassada da ƙyashi da kwaɗayi da maulah da shishshigi da yayi wa wasu tsiraru cikinmu wannan halin yawa a cikinmu,amma a zahiri na gaskiya matsaloli sunsha mana kai da bamu da mataimaka a cikin ƴan uwanmu sai dai muna samun taimako daga wajen ubangiji sai ya kasance ya sadar damu da mutanan kirki masu ƙaunarmu a yadda muke basa tunanin gazawarmu ce ko kasawarmu, basa kallan talaka a matsayin wanda zaka masa rana yayi ma dare,basa kallan mu a matsayin waɗanda ko nan gaba za'a haɗa baki da mu a aika ta musu wani abun basaji ransu zamu ci amanar su sun amince mana ɗari bisa ɗari, tabbas na sani akwai talakawa da ba wai talaucinsu ya damesu ba, amma babu mu a cikinsu kukan rayuwarmu kawai mukeyi ba muda ƙarfin aikata aiki makamancin wannan fatan ubangiji ya qara tsarkake zuciyoyinmu kaɗai a koda wanne lokacin mukeyi,da wannan tunanin kan muka qarasa station ɗin da bata cika nisa sosai bah muna shiga muka ci karo da Abbah Hashim sai su Aunty Asma'u,da tun a harabar station ɗin muka ci karo da tsadaddiyar motar Abbah Hashim ɗin da nake tunani cikin tashi motar suka shigo dukansu dan banga motar Aunty Asma'u ba a wajen, cikin kayansu na alfarma suke zazzaune dan Abbah Hashim ma waya yake amsa wa kallansu nakeyi sama da qasa kafin na maida kaina kanmu dan ko su Aunty Maimuna da suke aure Gwarzo masu rufin asiri sosai suke aure,amma a hakan wai ake tuhumar mu da ɓatan ƙaton saurayi da ya isa ya tara iyali ma kawai dai tozarcin da suke mana a gidan ne bai ishesu ba harda hukuma,saida ya gama wayarsa ya kallemu a wulaqance dukda gefensu muke tsaye muna kallonsu gefensu saida ya kallemu tas da Abbah wani koɗaɗɗan yadi ne jikinsa ni ce ma kayan nawa masu ɗan kyau cikin kayan su Aunty Abida,da Aunty Malika da suke bani,Abbah Hashim ya fara ma wani ɗan sanda magana ba wanda yasa a kiramu bane wani daban da gani shima ba kirkin zaiyi ba
"Yallaɓai ga sunan tuhumar su nake shi da ƴar sa kamar yadda na faɗa muku akan ɓatan ɗana Samir nake tuhumarsu ,dan tunda ƴarsa ta fito da halinta a gidana da tajemin hutun jarabawa,ranar da nace tabar gidana shima ranar ya bar gidan wayoyinsa a kashe na kira su yafi a ƙirga itama mahaifiyarshi ta shaidamin ba tasan ina ya tafi ba,nasan talakawa da muguwar sakayya shine nakeso a bincike min su har sai sun fito min da ɗana koda gawarsa ce sun tsafeminshi saboda suna so suyi kuɗi,bansani ba,dan su ba talaucin da suke ciki bane ya dame su sun riga da sun nuna hakan tuntuni dan dashi ya damesu ba zasu aje mugunta haka bah a ransu"Yadda ya tsara kalamansa da yadda suka ganshi alamun kuɗi sun bayyana a garesa ya sa ba tare da jin ta bakinmu ba kawai suka kwashe mu zuwa cell suka rufe mu da cewa har sai an samu number nashi kuka naji ya kwace min a cikin cell ɗin har sai yaushe zamu samu a fitar damu addu'a kawai nakeyi da tunanin su Mama a raina ya zasuji idan suka ji haka haka su Abbah Hashim suka gama cike cike su kabsr station ɗin da nasan yau zuciyoyinsu sunyi wasai dasu.
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.