43

38 4 1
                                    

43........

Gwaggo na cikin ba wa Mama Yoghurt ɗin aka turo ƙofar haɗe da sallama aka shigo Abbah Zaid ne da su Jabir sai Abbah

Abbah Zaid da Murmushi fuskarsa yake ƙara sowa
"Alhamdulillah ta samu ashe"

Dukka murmushi akayi Abbah ya ƙaraso yana miƙa wa Gwaggo magani

"Oh ni Abdulllahi sai kaje kayi zamanka kuma"Gwaggo tayi maganar tana ansar maganin

Abbah kansa ya mayar ƙasa ya ce"Wallahi Gwaggo sai chemist na cikin unguwa aka sameshi,ina hanyar dawowa na haɗu da Zaid ma,shine muka ƙara so tare a mota"

Gwaggo da ta ciro maganin a leda ta riƙe shi hannunta ta ce"Oh ni yanzu wannan ɗan abun shine yayi wuyar samu haka"

Aunty Maryam ta kalli maganin tayi dariya kaɗan"To ai Gwaggo haka magungunan suke fa kana rainasu haka sai kaji su da wuyar samu"

"Ai naga alama Maryama Allah ya rufa asiri"cewar Gwaggo ta ƙara sa maganar tana cire maganin akwalinshi

"Gwaggo ina yini ba'a gaisa ba"Abbah Zaid ne mai maganar yana murmushi

Gwaggo ta maida kallonta ga Abbah Zaid tayi murmushi
"Lafiya ƙalau zancen maganin nan yaɗauke min hankali"

Ya ɗaga kai "Hakane ya mai jiki?,aina ga ta samu sosai Allah ya ƙara lafiya"

Gwaggo ta ce"Amin dai Zaidu Allah ya saka muku da alkhairi ya bar tare"

Yayi murmushi "Amin Gwaggo ai yiwa kaine duk wanda ya taimaki wani ai ba wanin ya taimaka ba kansa ya taimaka,Allah dai ya karɓi ayyukanmu"

"Amin"dukka ɗakin muka ce,Cikin haɗin baki muma muka gaisheda Abbah Zaid cikin sakin fuska ya karɓa gaisuwar tamu da tambayarmu ya mai jiki muka amsa da Alhamdulillah

Aunty naga ta wurgawa su Jabir harara sannan naji ta ce

"Baku iya gaisuwa baku?,Sannan Ummin taku fa ba zaku gaishe ta ba?"

Gwaggo tayi murmushi"Kyalesu Rumaisah baki ga yanzu aka gama gaisawa da Abbahnsu ba?"

Aunty ta yi murmushi kaɗan"Allah Gwaggo ba suda niyyar hakan baki gani ba sun tsaya sai kallon mutane sukeyi kawai"

Gwaggo cikin murmushi ta juya ta kalli Jabir da Muhammad da tunda Aunty ta fara magana ransu ke haɗe alamun basu so faɗanba

"Kunji Ummanku tace ba kuda niyyar gaida mutane hakane"

Aunty ta hararesu hakan yasa sukayi ƙasa da kansu Sannan suka ɗago suka furta cikin haɗa baki

"Ina yininku?"
"Ya mai jiki"

Murmushi su Aunty Jamila suka yi suma cikin haɗin baki suka amsa da

"Lafiya ƙalau"
"Mai jiki Alhamdulillah"

Inda Mama take kwance suka ƙara sa
"Ummi Ina yini?"
"Ya jikin naki"

Mama da murmushi ta kallesu a hankali kuma naji ta furta
"Alhamdulillah"

Gwaggo cikin sigar zolaya ta ce"Waye ɗan nawa Jabirun a cikinku?"

Murmushi Jabir yayi ya ce "Nine Gwaggo"

Gwaggo ta dafa shi"To mezan samu,naga hannunka bakomai kar nace nafasa auren"

Murmushi Jabir yayi"Aini dama Gwaggo kinyimin tsufa"

Ido ta zaro"Lallai Jabir to ai anfisan irinmu"

Murmushi duka mukeyi muna jin dramar Gwaggo da Jabir hatta Mama itama murmushi takeyi,da alamu itama firar na mata daɗi

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now