32

32 6 1
                                    

Aunty kiran mijinta ta shiga yi a waya lallai ya taimaka ya barta taje taga Mama bai hanata ba hakan yasa harta abincin Muhammad ta ajiye sa muka fito ta rufo gidan
Sallama ɗauke da bakinmu tun daga zauren gidan namu har zuwa ciki daga cikin ɗaki nake jiyo Muryar Mama tana amsa sallamar tamu tana mai leƙowa kofar ɗaki,Aunty ce tayi wajenta da saurinta ta ƙara sa wajen Mama rungume Maman tayi da nake shaidar  Maman har zuwa lokacin ba ta gama ganeta ba Aunty cikin kuka ta ɗago ta kalli Mama
"Hauwah kece haka kodai mai kama da ke ce,na kasa fahimtar komai,sauyawarki tayi yawa"

Cikin karayar zuciya Mama naji tana magana"Rumaisah dama zan sake ganin ki tsawan yawan shekarun da bama tare"

Auntyn ce ta saki Mama tana goge hawayenta cikin alamun wacce tayi kuka muryarta da ta nuna
"Ba kya nemana ne Hauwah kina cikin wannan halin har bara Ahmad yakeyi baki nemeni ba,nice kullum na haɗu da ƙawaye nake tanbayarki bansan kun dawo gida ba bansan rayuwar ta tuƙe muku har haka ba banyi tsammani ko a mafarki zaki yi wannan rayuwar ba" tana maganar tana cigaba da goge hawayenta nima da nake tsaye kamar an da sani a gefensu hawayen nakeji da karayar zuciya

"Kin tsaya kallonmu ki mana shimfiɗa mana"Mama ce tayimin maganar cikin sauri na wuce ta gefen Mama nashiga ɗakin maman na ɗauko tabarma nayi shimfiɗa
"Aunty ga shimfiɗa nayi ki zauna"nayi maganar cikin ladabi ina ƙasa da kaina zaman tayi Mama ma ta zauna kusa da ita ni ɗin ma zama nayi gefensu daga ƙasa don banajin zan iya barin wajen ji nake kamar Aunty zata zamar mana sanadiyyar samun sauƙin sauƙaƙar lamuran da sukayi tsamari garemu ji nake kamar zata fitar damu daga wannan yanayin ji nake kamar Mama ta samu inda zatayi kukanta a samar mata mafita ba kamar inta faɗa a gida ba iya haƙuri ne kawai zasu bata suma ta kansu da rayuwarsu sukeyi tamkar matsi ne idan muka takura musu da faɗar halin yau da kullum da muke ciki,ban taɓa jin Mama ta bamu labarin wata ƙawarta Rumaisa ba da har ƙawancensu yakai Mama ta sawa Rumaisa sunanta dukda banida tabbacin hakanne amma yanda zumuncin su yake nunawa hakan ne ya faru bana tantamar cewa Mama ganin bata da shi yasa duk wasu ƙawayenta ma bata nuna mana su ba bata bibiyarsu suma kuma hakan saboda yanda yau da kullum mai wahala maganar Aunty ta katsemin tunanina

"Sam baki kyauta ba na jima ina mafarkin ki na yima su Maryam Hashim maganar ki sosai duk inmun haɗu ko naje gidansu ko sunzo nawa sai suce min bakya yin zumunci ko kinzo gari saidai suji labari na nemi lambarki suka cemin basu da shi wallahi Hauwa na damu da jinki shiru ɗin nan bansani ba ko dan haka nake mafarkinki"

Mama murmushi tayi "nima na damu da rashinki tunda muka dawo nake san nemanki abubuwa suka zo suka cakuɗe shine dalilin da yasa har nakai wannan lokacin ban nemeki ba"

"Amma ai a cakuɗewar abubuwan ya kamata ki nemeni ko zan rage miki wani abun amma ba ace a sanadin barar ɗanki ba,dana hanashi kona koreshi ba,da har zuwa tuƙewar lamuran sufi nada ba zaki nemeni ba,mamakin dana sakeyi ma ancemin gidan surikanki kike kuma na ganki anan"Aunty tayi maganar tana tsaida idan ta kan Mama

Mama tayi ƙoƙarin maida kwallarta da take ƙoƙarin zubowa"sun koremu a gidan an kusa wata ɗaya kenan"

"To me kuka yi musu mijin naki ba ɗan gidan bane"

Mama ta girgiza kai "Ko ɗaya amma korar ce mafi alkhairi ma a wajenmu....."
Nan Mama ta shiga bata labari a takaice nayi mamakin yarda Mama ta iya zaman bada labarin rayuwar da muke ciki har haka sai dai ganin yadda taransu ya kasance a baya da na fahimci yafi nawa dana Halima yasa na cirewa kaina mamaki domin kuwa abokin kuka ake faɗa wa mutuwa

Aunty ta jinjina kai "Waɗannan ko basu san gamawa da duniya lafiya wanda zai wulaƙanta zumunci har haka ai tikitin watsewar rayuwa ya ɗaukarma kansa amma Hauwa ki haƙura da auren ɗan uwan nasu mana kinga yadda kika dawo kuwa,ki barsu dashi indai zai samu sauƙin wani abun daga garesu Allah ya san alkhairin da yin hakan zai haifar na miki alkawarin zan riƙeki da ke da yaranki ko da sunfi hakan nema, inasan yara musamman mata sai Allah ya bani maza kuma guda biyu dukda ban fidda rai ga samun wasun ba amma a yanzu biyunne"

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now