20
Misalin qarfe goma na safe na kammala shiryawa,Halimah ma ta shirya dan Yaya Baffa zai kaini Tasha tako ce lallai sai ta bishi an rakani da ita Faisal ya dauki jakata ya kaita napep dake kofar gida,Abban Halimah da mamarsu ku'di suka bani nayi ku'din mota da inada niyyar qin amsa Halimah kuwa ta kar'be tace su bata ta bani,tasan halina na musu godiya duka gaisuwa suka bani nayiwa su Mamah da qannenah,haka muka fito ina sake jin qaunar Halimah da ahalinta a raina muna tafe a mota Halimah tana jana da fira har ni kam hankalina baya wajenta tunanikane kala kala a raina ga uwa uba kewar Halima da nakeyi ga Batul ma bamu ha'du ba babu damar hakan hankalina yayi gida ne,Halimah ta kalleni
"Haba mana Sumayya sai zance nake kinmin shiru"
"Yi hakuri Halimah ban jiki ba"
Yaya Baffa ya 'dan juyo ya kallemu
"Haba keko Halimah tunanin gida takeyi barta tayi abunta,nasan ji take kamar tayi tsuntsu ta jita gida,na dauka zakuce ma zaku biya gidansu Batul ai,naga munzo unguwar"Kamar jira muke yi yayi zancen Batul cikin ha'din baki muka amsa
"Zamuje mana Yaya Baffa"Kwanar layin gidansu Batul yayi ba wata tafiya mai nisa sai gamu kofar gidan nasu,Dan qaramin gida amma jikin family house dinsu yake Batul tace mana duk cikin family house din nasu aka yi gidan nasu,Kamar jira muke napep din ta tsaya mukayi saurin ficewa a motar,Yaya Baffa na koramana kashedin kada mu da'de,da Batul muka ci Karo zauren gidan nasu muna tura kofar,wani ihun murna ta saki
"Sumayyah oyoyo ashe kin dawo ba labari,qila ma kina Kano shekaran jiya da mukayi waya,mu shiga ciki"Halimah ta kalleta
"Ke malamah sauri fa muke da Yaya Baffa muke,kinsan ashe su Sumayya sun koma Gwarzo fa,nima sai jiya da Sumayya tazo naji labari,itama batada masaniya a gidanmu ta kwana ma, yanzu Gwarzo zata wuce muka biyo,muje mu gaishe da Mama dai mu fito"Batul ta harari Halimah
"To aku mai bakin surutu aina dauka ma gaishe da Maman ma ba za'a shiga yi ba,Abbah ma yana ciki,amma banji da'di ba Kamar nayi kuka"Da haka muka qarasa ciki Halima na fa'din "Nima haka naji Batul ya zamuyi an saba,kamar nayi kuka nakeji"
"Ke dama uwar kuka ba"
Duka dariya mukayi banda Halimah da ta ha'da fuska a tsakar gida brander muka sami iyayen Batul zaune a qaton tabarma da qannenta duka kasancewar Batul itace babba itama,kamarni,gaisawa mukayi Batul ta shiga koramusu jawabi cewar mun tashi mun koma garinmu Abban su Batul cikin rashin jin da'di ya kalli Batul
"Amma ba jimawa dai da hakan,da ai baza'ayi haka ba, indai matsalar haya ne ga gidan Abbahnku sai su zauna har Allah ya hore musu,aikinma Banda abun Abdullahi ai nema akeyi ba'a zama haka,amma banji da'di ba"Maman Batul ta girgiza Kai da damuwa fuskarta
"Nima haka Abban Batul gashi duk sun saba, za'a rabu Kuma,qila shima yanada buqatar komawa,shiyasa ba labarin kome"Cikin jin da'din yadda iyayen Batul suka nuna jimamin komawar na rashin Jin da'din su na yi magana
"Ai mamah mai gidan da muke hayarne ba zato yazo ya bada notice Abbah nasan bai samu lokacin tsayawa wani tunani ba sai ha'da kaya kawai suka koma gidan duka"Abban Batul ya dubeni
"Hakane amma kwanaki baya mun ha'du ya fara jan napep yacemin Alhaji Yassar ya samu daga wajenshi,Ahmad ma ya samu yake ja"Halima ce tasa baki lokacin
"Ai Abbah napep din Faisal yace ta lalace ba ku'din gyara shine ya maida musu kayarsu""Aini Abdullahi na rasa irinshi tunda yara sun ha'da mu ba'abun yana boyemin abubuwa da yashafemu duka bane,ko yazo wajena ko mun ha'du ba wata magana da za'a taru a jajanta ko abunda ya shafi buqatar taimako da zai fa'damin na rasa wannan abun nashi,tafiyar Sumayya ma sai bakin Batul naji yanzu ai an zama 'daya,dama 'daya ne tunda school 'daya ma mukayi a lokacin da yake yin masters"Abbah ya qarasa zancen da alamun damuwa
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.