Mama na kallah da nake gefen ta zaune"Wallahi Mama yunwa nakeji kinji cikina kuwa kamar banci komai ba nakeji gashi Abbah har yau shiru"
Ahmad da yake gefena ya fara magana"ai dole muji yunwa tun safe fa rabanmu da abinci,ni dai Mama ko awara da safe ki riqayi koni zan ɗauka wallahi"
"To Ahmad ai matsalar babu jarin ne da ina zama ya kamani kullum kuna kukan yunwa idan sanadinta rayuwarku ta shiga haɗari fa,ƴan uwan mahaifinku dariya zasu yi suna murna"cewar Mama da a raunane take maganar
Ni ce nayi hanzarin cewa"Mama ki anso rance wajen Gwaggo ko Aunty Maryam duk fa zasu baki,kina gani Abbah tun safe ya fita ko ɗuriyarshi babu ta yiyu babu ciniki ne a kasuwar"
Ahmad ya furta "yawwa Mama wallahi Yaya Sumayyah ta faɗi gaskiya"
Jim mama tayi kafin zuwa wani lokaci
"Banasan karatunku ya samu hanyar lalacewa Ahmad amma in hakan zai zamo mafita sai mu riƙa yi bari Abbanku ya dawo muji ta bakinshi"Tabbas maganar Mama tana kan hanya amma da gurɓatar gobenmu gwara rasa wani ɓangare na karatun namu dan yanzu ma da wannan yunwar dake fafakar mu su Rumaisa sukayi barci in mu muna jurewa to waɗanda suka fi ƙanƙantar jikinmu duba da yadda rayuwar ta sauya,taimako ko sai waɗanda suke mana sun samu abunda zasu taimaki wani,rashin dawowar Abbah ita tafi tsayamin rai na a yanzu
"Assalamu alaikum" inda nake jiyo sallamar na waiga ina kallo Abbah ne mai sallamar hannunshi riƙe da Kwando aje sa yayi gefe ya qaraso ciki ganinshi ya sanyaya zuciyata da bugun da takeyi tunda munsamu dawowarshi lafiya Mama ce ta yi hanzarin amsa sallamar gami da miƙewa
"Wa'alaikumussalam, Abban Ahmad yanzu muke zancen daɗewarka da yara,Sannu da zuwa"
Fuskarsa ɗauke da farfaɗan murmushi ya ƙara so inda muke zaune ya zauna kusa da Mama
"Sannu da zuwa Abbah"muka haɗa baki gurin yi masa
Kallonmu yakeyi da fitilar wayar da take gefenmu jingina a kunne "wai duk damuwar rashin dawowa ta yasa ku ƙinyin barci tara fa nasan ta wuce,ko dai yunwa ce?"
Kai muka girgiza dan kwantarwa Abbah hankalinsa kan shima ya girgiza ya juya ya dubi Mama yana faɗin"An samu dafa wani abun kuwa?"
"To Abbahn Ahmad baka dawo ba tun safe,nan kuma bakomai sai jarin awarar nan da har zan taɓa nayi tunanin ko shirunka ba asamu ciniki bane kar na taɓa azo kuma a rasa jarin"Mama tayi maganar cikin raunin murya
"Kinyi dabara kuwa Hauwa'u ai tun safe dana fita har daren nan ɗari biyu nayi ke kinga kasuwa yadda ta cika da attaruhu,da nake bawa Musa labari ya ce yana da alaƙa da wannan ne zuwana na farko kasuwar,kinga yalo ma na siyo mana da kuɗin,Ahmad duba cikin kayan miyan can ka ɗauko ka wankoshi sai asamu aci kar ku kwanta da yunwa"Abbah na ƙara sa maganar Ahmad ya miƙe kamar ya faɗi ina kula da yanayinshi ba jimawa ya dawo
Abbah ne ya miƙe,Mama ta dubeshi "ya ka tashi Abbah Ahmad kaima Yakamata kaci fa""Kuci kawai ni na biya ta gidan Musa ai na samu na tarar yana cin abinci munci tare"
Nidai kallon yanayin Abbah nakeyi wanda ba lallai ɗin gaskiya yacin bane ba kawai ya faɗa ne dan ya kwantar mana da hankali sai da ya shige ɗaki kamar mai tangaɗi da na sake tabbatar da zargina yunwa ce ke cinsa kalaman ya faɗa mana dan muji sauƙi kan yalon na dawo na fara ci firar ma kasa ta mukayi nice na riga tashi dan yalon ma baya yimin daɗi sai da safe na musu na bar gurin
Tunani ma banbanta nakeyi ga wani ciwo mai tsanani da kaina keyi har zuwa yau nakasa sabo da yunwar da mukan kwana mu tashi da Iran mu yini da ita,ɗumamun hawaye ke zubomin har zuwa yanzu tunanin dangin mahaifina yaka sa barina suna da komai amma sun wofantar damu badan da kwakkwarar laifi ɗaya kwakkwara da muka aiwatar musu amma suka aiwatar mana haka nakasa fahimtar meye ne laifin Abbah maiyayi musu bazasu dubeshi jarabawar da take tare dashi ba wayata naji tana ƙara na yi hanzarin lalubarta na duba mai kiran,Yaya Samir ne kamar bazan ɗauka ba sai kuma na ɗauka ina faɗin
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.