49

56 4 2
                                    

NA CANCANTA!49

Na
Halimatu Ibrahim Khalil

ADABI WRITERS ASSOCIATION

"Ina Sumayyah ne?"Naji muryar Abbah yana kiran sunana mayafin Mama dake saman gado na ɗauka na yafa na fito ina cewa

"Abbah gani nan"

Inda suke a zaune na ƙara sa shi da baƙon yanada fara'a a yarda fuskarsa ta nuna baza'a kirashi matsayin fari ba kuma baƙi ba a shekaru bazai wuce Abbah ba ko ya fishi to da kaɗan ne

Har ƙasa na durƙusa na gaishe da baƙon da ya kira sunanshi Lukman

Abbah ya furta a hankali"Sumayyah sunan ta itace babbar ƴata"

"Masha Allah Allah yayiwa rayuwarta albarka ta kammala karatu ne"

Abbah ya amsa da "Amin,a'a bata samu qualyfying ba amma yanzu tana SS2"

"Allah ya taimaka"

"Amin"

Abbah aljihun rigarsa ya duba ya miƙomin dubu ɗaya da cikin kuɗin Abbah Zaid take

"Ungo ki siyo masa ruwa da lemo a shago"

"A'a kabarshi Alhamdulillah wllh nagode"

Abbah ya kallesa
"A'a Malam Lukman baza'ayi haka ba dan Allah ka tsaya ko ruwa kasha"

"Da kabarshi akwai ruwa a mota..."

Miƙewa nayi ban jira abinda zai ƙarasa faɗa ba,ina tafiya ina tunanin halayyar mutumin babu wani abu da zai nuni da cewa baƙon namu mai wani abin hannune indai a halayya ne sai dai ko idan ka kalli kayan da yake sanye dasu ina mamakin dama har zuwa yanzu akwai masu kuɗi marasa faɗin rai da jin su  wasu ne sai gashi ni ganau ce ba jiyau ba akwai irinsu da nasan sun zarcewa masu faɗin ran yawa saidai idan Allah bai ƙaddara ma mu'amala dasu ba,Da wannan tunanin na ƙara sa wani ƙara min shago dake bayan layinmu Soft Drinks Store ne sai dai ba wani babba bane sai nace yau ne zuwa na na farko shagon hakan yasa mai shagon,gaba ɗaya dubu ɗaya saida ta ƙare a siyan ruwa da lemo fearless na siyo guda uku sai ruwa Swan guda biyu dan gani nake tuwon girma miyar nama ya dace ayi mata

Sai a wajen dawowa gida na hangi mota daga ƙofar gidanmu gefen guda dukda bansan motoci ba kyawunta da fasalinta ya bani tabbacin mai tsada ce

Ina shiga na samu su Rumaisah sun dawo suna tsugunne a wajensu Abbah baƙon yana musu tambayoyi game da karatu ni dai kallon ikon Allah nake sake yiwa mutumin saina ga kirkin nashi a zahiri harma yayi yawa ban tsawaita tunani ba na barshi a dandai bamu saba haɗuwa da irinsu ba shiyasa danko Abbah Zaid shi ba mai yawan surutu bane ba

Lemon da banyi tsammani zaiyi masa ba naga ya ɗauka ya buɗe,Da haka muka tashi  muka koma ɗaki

Rumaisah ta dubeni "waye shi Yaya Sumayyah?"

Harararta nayi "Kunfa rigani shigowa aiku zan tanbaya"

"Dan Allah Yaya kefa da gani kinanan aiken kima naga alamar akayi ma nasani tunda mun maga alamun hakan"

Bayani na fara yi musu, Rumaisah bata jira na kammala ba,ta yi min wata runguma dana kusa   kwanciya reras

"Dan Allah Yaya dagaske kikeyi"

Harararta nayi "Aikinsan na saba da ƙarya ko?,Ni cikani karki yarda ni ƙasa"

Ƙoƙarin sakenin tayi tana faɗin"Bafa haka nake nufi ba kinsan abu ya baka mamaki kana kalar wannan maganar"

"Tsari kawai,ku jira Mama ko Abbah baƙon ya tafi ya baku labari su za'a fi yarda da zancensu"

Khadijah ta ɗan ɓata fuska"Yaya,Yaya Rumaisah fa tayi mu babu ruwanmu ai munsan bazaki mana ƙarya ba"

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now