28

40 5 0
                                    

Sai da nafara shiga ciki na gaishe da su mamansu sannan na dawo wajen Malikan na jawo kujera na zauna kallona tayi

"Ya naga kin samu kujera kin zauna ba awarar zaki fitar ba?"

Hararar Malikan nayi kafin na ce"kinga ƙari wuqa na tayaki yankawar kina abu salo saloh kamar mara lakka a jiki"

Itama hararar ta wurgomin"ina tambayar ki kina wani zancen daban saboda kin raina kokari na yankan dankali ba kamar yankan awara bace Malama"

Tsaki nayi na ce"kinga ba wani nan ke dai ɗin ce ba kida saurin aiki,kawo na ƙara sa kigani" wuqar ta muƙamin tana ce wa"na sakarmiki gwada mu gani,ina dariya na anshe na cigaba da yankan

"Yawwa kawo kiga yadda ake saurin aiki dama Rumaisa ta ɓatomin rai nazo nan naga kina neman sake ɓatamin,Allah so nayi na kwaɗama yarinyar nan mari ma ta cika yimin shishshigi saikace wata ni sa'arta ce amma dan taga Mama ba tanan ne"

Dariya Malika tayi jin kawo ƙarshen zance na"Allah sarki Rumaisa kace ta kusa shan mari Kamar zaki iya ba sai Rumaisah ta tumurmusa ki ba,ƙila ma gaskiya ta faɗamiki da baki santa,ina mamar ta tafi ne?"

Wata harara na gallawa Malika"Allah Malika zaki sa nayi zagi fa Rumaisah zata dakeni aiko zata iya tasan halin Abbah,ke ɗin gaskiyar kike so?,Mama taje gaisheda Aunty Maryam ne,tun ɗazu ma yanzu nasan tana gab dawowa"

"Toh ni dai yi haƙuri kar idan ya faɗi ƙasa kan harara ko kijema ki yanke,Allah ya huci zuciyar Sumy baby,Allah ya bata lafiya in zaki dubiya zamuje tare"

"Amin" na furta nayi ƙwafa na ƙara maida hankali kan yankan dankalin Malika ta miƙe "yawwah bari na haɗo kayan ana gama yankan sai dai mu wuce,naji anayimin kwafa" da "toh"na amsa mata ba tare da na bata amsar ƙarshen zancenta ba,ta ƙara sa barin wajen Mamansu Malika naji muryarta

"Har kin gama firar kenan Sarkin ƴan shiririta,anya sana'ar nan zata ɗaure kuwa idan kin gaji ki faɗa min ko Na'im sai nasa ya riƙa yi"cikin hassala take yin maganar

Ƙasa ƙasa naji Malikan na magana"Haba Ummah karfa wasu suji suyi dariya ina ƙoƙari daidai fa nawa"Tsaki tayi ma Malikan ta na cewa"naga alama ai wa kika barwa yankan?"

"Sumayyah ce Ummah yau basa awarar ne Mamansu bata nan"Umma ta furta "Naji wuce ni ki kwaso kayan na haɗa su"

Dariya nayi kaɗan jin diramar Malika da mamarsu haka ta kwaso kayan ta ajesu gefe zuwa lokacin saura uku na gama yankawar na dubeta da ɗago kai ina dariya ƙasa ƙasa cikin ƙufula ta dubeni "yi dariyarki san ran ki akwai ranar ramawa ai"tsaki nayi nace "sai me Hajiya Malika ai dama kin saba"na ƙara sa maganar na aje yankan na miƙe "ga kayankinan ki ƙara sa abinki mashiririciya"wajen kayan na nufa Na'im da ya ke ƙoƙarin shigewa ciki da shigowarshi kenan na kallah "Yawwah Na'im fitar da waɗannan ka tayani,aka biye wannan sai akai isha ba'a fita ba"kayan na tsinta marasa nauyi na miƙa masa nima na kwashi wasu naji Malika na cewa"ki tayi dai zan rama amma bani saƙo wajenki bari na fito" ban bi takanta ba muka fice
Haɗa wutar nayi da Na'im ya samo rushi dandanan ta kama na ɗauka kasko na zuba mai da sai lokacin Malika ta fito da robar dankalin tana ajewa na fara zubawa har man ya ɗauki zafi tashi nayi na bata guri ina cewa"Yawwa zauna wajenki Ni wucewa zanyi gida kar Mama ta dawo"kallona Malika tayi"nafa ce za muyi magana amma kike ƙoƙarin guduwa nagode" ta ƙara sa maganar ta na zama kujerar dana tashin,"kai Malika na manta ne fa,ina sauraronki"na ƙara sa maganar badan naso ayi zancen ba dukda bansan kallar sa ba

Malika ta maida dubenta gareni kafin ta fara magana"Yawwah Sumayyah Jurayd yayan Alhassan ya bani saƙo wajenki"
Tsaki nayi na kalleta"kinga Malama kiyi maganarki direct ba tsaitsayawa kinsan sauri nake yi"
Dankalin ta ɗauki matsami ta fara juyawa kafin ta ce"shine hardamin tsaki nagode nuna anshi saƙon ai tayi kai kuma,dama cewa yayi yana sonki kuma da gaske yake da niyyar aure yazo"

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now