NA CANCANTA! 47
Na
Halimatu Ibrahim KhalilDan Allah kuya haƙuri ji na shirun da kukayi ya faru sanadin manyan dalilai na sanar da dalilan a NA CANCANTA FANS GROUP, Ina godiya da ƙaunar da kuke nunawa ga littafin da hartakai ga ƙaunarku zuwa gareni
47
"Lafiyarki kuwa Sumayyah!?"
Cikin sanyi jiki na ɗago na kalli Aunty Zainab da tayi maganar
"Lafiya ta ƙalau Aunty Zainab"
"Da sauƙi dai faɗa min meke damunki?,tun dawowarki na lura da yanayinki ya canza mai Juraid yayi miki?"
Dariya nayi badan naso ba sai dan jin abinda Aunty Zainab ta ƙara sa zancenta dashi wai me Juraid yayimin ni kuwa mai zaiyi min na ayyana a raina
"Au dariya na baki ma?"
Kai na girgizamata ganin yarda tasha kunu na furta
"A'a fa Aunty Zee gani nayi kincemin mai yayimin bayan kinsan ba abinda zaiyi min"
Hararata tayi ta ce"Naga alama,kuma ina nufin mai yafaru tsakaninku ?"
Murmushi nayi dandanan idona ya fara ƙoƙarin kawo ruwa bansan lokacin dana fashe da kuka ba,Aunty Zainab dafani tayi ta ɗago fuskata da ɗaya hannunta tana faɗin
"Haba! Sumayyah kuka fa kikeyi ki sanarmin komai?kafin ki saka nima na fara yi"Ta ƙara sa maganar tana fara gogemin hawayena
Kamar bazanyi magana ba sai kuma na fahimci Aunty Zainab matsayin uwa take wajena bai dace indai inada kara ba idan har bazan ɓoyewa Mama magana ba ita na ɓoye mata duk da kasancewar ta abokiyar haihuwata amma matsayinta na uwa gareni bazai goge ba kuma banada burin ta goge abunda yayi Mama shine yayi Aunty Zainab a taƙaice kenan cikin muryar kuka na fara magana
"Aunty Zee Juraid ya ce zai turo gidanmu"
Aunty Zainab ta bar abunda take ta ɗago da sauri ta kalleni gami da zaro ido
"Ya turo wanne gidan?kardai nufinsa gidansu Abbahnku"
Kai na ɗaga na ce"Eh hakan yake nufi"
"Tabɗi jan ana wata ga wata banjin kuwa gidansu Abbah zasu amshesu wallahi,laifin duniya kuwa idan sukayi hakan ku za'a ɗaurawa shi"cewar Aunty Zainab ta ƙara sa maganar tana kallona
Murmushin da yafi kuka ciwo nayi da dasassar murya da kamar ta wadda ta yini tana kuka na ce"Nima hakan kaɗai na tuna yana ɗagamin hankali sai dai a nawa ganin kamar tunda ba Yaya Samir bane zasu iya amsar zancen"
"To Allah yasa hakan Sumayyah I wished you all the best"
A hankali na furta "Amin thank you"
"Wai muryarki harta fara dusashewa kamar wacce tasha uban kuka zan cigaba da ta yaki addu'a dan Allah karki damu,yawancin wasu dangin uban ba a dacensu ba wai ku kaɗai bane da wannan matsalar,Yaya Nasir ya shigo ɗazu kun ga shigowarsa ma hala?"
Kai na ɗaga da hakan zan iya cewa al'ada tace sannan na ce"Eh hakane,Ya samemu a waje da tare dasu Juraid zasu shigo suka rigashi shigowa,kun haɗu?"
Tsaki ta jamin"Na haɗu dashi nayi masa menene?"
Dariya nayi"Wallahi Aunty Zainab ya mato kanki"
Wani tsakin ta sake jamin "Damuwarsa ce ni karatu nakeson yi wallahi idan su Abida sukazo hutu gwanin sha'awa abinsu"
Murmushi nayi ni kaina inada burin cigaba da karatu amma gashi Secondary ɗin ma taƙi kammaluwa na dai kokarin kawarda tunanin nace"sai ya jiraki"
Haka muka cigaba da taɓa fira har Aunty Jamila ta kwala kiran Aunty Zainab tace ta taho su tafi dare nayi
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.