34.....
Ina kammala wanke wanken na koma ɗaki wani barci mai nauyi ya ɗaukeni"Ke dalla can ki tashi"dukan da naji an makamin a baya tare da jin muryar Malika cikin barcin nayi hanzarin miƙewa ina sosa bayana saboda yadda dukan ya shigeni
Kallona Malikan ta sakeyi da faɗin "Gaskiyane ke barci ma kikeyi?"
Tsaki naja da gama wartsake idanuna cikin yanayin ɓacin rai"Wallahi bakida mutunci Malika ina barcina kikasan da yadda nayi kin maka min duka haka,Allah ya isa wallahi kuma in banyi barci ba mai kikeso nayi?"
"Masifa ni zakiyiwa Allah ya isa daga taimakonki,naga mai rakaki siyo yadin makarantar danni yanzuma ba zani ba rana tayi bazan je na kwaso uwar ranar nan ba"sai da yanzu na tuna da abunda yake gabana
Murya na marairaice na ce"Haba Malika daga faɗin hakan wallahi namanta ne,kuma barcin ya ɗaukar min daɗi"
Tsaki Malika tayi tana ƙoƙarin tashi nayi saurin riƙe hannunta"Dan Allah ki zauna mana,kefa matsala ta dake kenan,nifa ba sanin garin nan nayi ba"
Hararata tayi ta ce"zaki sani ai ƴar rainin hankali ni dai koma zani ba zani cikin tsawon ranar nan ba wallahi"
Kai na dafe Malika matsala kenan haka duk Malika take ko ita kaɗaice hakan bansani ba dan Aunty Malika ba sabo tsakaninmu da zan fahimci hakan daga gareta na cire tunanin kar na sake ɓata mata rai
"To da yamma fa?"Sororo ta tsaya kallona"Wacce yammar islamiyya?,zan fasa zuwa ko kuwa dai nufinki na fasa sana'ar da nakeyi na raka ki?"
Murya na sassauta"Amma Malika nima fa ina islamiyya ɗin nan ina kuma sana'ar tunda ba zaki ba amma shikenan"na ƙara sa maganar ina komawa kwanciyata
Kallona naga Malika tayi "Malama haka zamuyi dake kenan wato barci ma zaki koma wato matsalata ce bataki ba"
Cikin ɓacin rai nima na tsaida idona kanta"To ya zanmiki tunda kinkawo uzurinki bakomai zan biya gidan Gwaggo naja Rumaisa ta rakani yanzu ma tunda nasan sai yamma zasu dawo"
"Wai cewa nayi miki bazan rakani bane,kice zaku sha yawo kafin ku gano inda zaku samu yadin a ca muku kuɗi kuma ku bayar a ɗinka muku ba mai kyau,saidai idan kinaso kija Zainab da kuma nasan bazata rakaki ba ba shiga ba fita nasan halinta"
Jin ƙarshen zancen Malika na kalleta na ce "Toh ya zanyi miki ne Malika koma mara kyau zan samu ai yfimin jiranki ɗin tunda bazaki ba"
"Allah zan fasa rakakin da nayi niyyaryi yanzu wallahi"rigima Malika kenan ko ina tace yanzu zata rakani,naja numfashi na ce
"To yanzu yaushe zaki rakani ɗin"na ƙara sa maganar da murmushi
Baki ta taɓe"ya zanyi kinyimin asarar islamiyya wajen 3 na yamma saiki shirya da wuri kar ki sake rainamin hankali"
"Toh shikenan naji Nagode"nayi maganar ina juya kaina dan kar a sake cewa anfasa rakon
"Kinga nima tafiya zanyi gida ba sai kin juya kaiba,idan kinyi niyya ki gama shiriritarki wajen 3 na rana zaki iya zuwa mu ta fi"
Ko amsa ban bata ba dan na ƙagu ta tafi rikicin Malika sai ita sam bata fahimtar situation ɗin da mutum yake ciki ma wani lokacin
Uku saura na samu na shirya dan zullumin kar Malika tacemin ta fasa Mama na leƙa ɗakinta na faɗa wa mun tafi addu'a tayi mana daga bisani na fito gidansu Malika na shiga,
Ummansu Malikan na samu a tsakar gida tana tankaɗen gari gefenta Na'im ke wasa da motar yara gaisheta nayi cikin sakin fuska ta amsa min ta ɗaura da cewa
"Malikan na ciki har ta fara mitar ta zata ma fasa rakakin"Nayi murmushi na ce"Kai Malika Umma uku fa mukayi zamu tafi kuma har yanzu bata ƙara sa ba"
Ummata ce"Ai kinsan halin Malikar taki"
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.