44

35 5 0
                                    


44....

"Kukan ubanki kika isa mutane dayi ko ke kaɗai aka ɓatawa anan"Muryar Gwaggo nake jiyowa cikin kukan nawa da alamun ɓacin rai maiyawa take maganar hakan yasa ni tsaida kukan da saurina sai dai idona na ƙasa

Abbah Zaid cikin sanyin murya naji ya ce"A'ah Gwaggo ki barta tayi ko ta samu sauƙi mana"

Gwaggo da kaushin murya ta ce"Zaidu kenan wannan munafukar yarinyace duk ita ta taso da waɗannan fitintinun sarai tasan halin ƴan uwan ubanta taje ta fara soyayya da ɗansu gashinan ai yanzu ma kuka fara gani indai bazaki haƙura da Samir ɗin ba"

Hawaye na cigaba da zubarwa jin yadda Gwaggo take magana wadda batasan meye ya faru ba kuma ba wani ya bata gamsasshen labari ba daɗin haushi gabansu Juraid da na tabbatar yarda zaiyi tunda Gwaggo ta fara bada shaida halin nata sai ita maganar Abbah Zaid da ya ɗaura ta katsemin abubuwan da nake aiyanawa

"A'ah Gwaggo bata da laifi Sumayyah shi dai wani ɗan uwan kinsan dashi sai kaji gwara wani aminin arziƙi sau trillion mene dan ɗan sa yace yanasan Sumayyah shi da kanshi mai iya haɗawa ne to gaba ɗaya na lura jahilci yana ɗawainiya dashi"

Gwaggo naji ta ce "Wanne jahilci hauka dai ai babu hankali a tare da wannan"

Aunty Maryam naji ta saka baki lokacin tare da cewa"Allah Gwaggo ba wani hauka fa cin mutunci ne ke damunsa kawai ki duba fa ki gani yarda yake magana yanaga yafi ƙarfin kowa kawai matsiyaci dashi Allah ya dube wanda aka zalunta kuma baya barin zalunci ai"

"Tafiya zaku yi Juraid?"Jin maganar Uncle Jabir mai alamun tambaya ya sani ɗago kaina inda su Juraid suke a tsaye suke ban iya tantance yadda fuskar kowanensu yake ba,Yaya Nasir naga ya ɗagawa Uncle Jabir Kai ba tare da sun mana ko saida safe ba suka buɗe ƙofar suka fice gami da turo ta banyi hanzarin binsu ba saboda rashin sanin da wanne ido zan kallesu kuma suma da wannan zasu cigaba da kallona

"Kungani sun fice ba ko sallama ai anyi abun kunya matuƙa a gurin nan"Muryar Aunty Jamila na jiyo a cikin tunanin da na fara

Aunty Maryam ta ce"Ba dole ba Jamila mai zasu iya faɗa mana bayan abinda ake gudun sujin sunji da bakinsu kansa ya cuta bakomai talauci ai ba kansu aka fara ba indai ma ya gama fita daga harkarsu ai anyi sa'a" Aunty Maryam ta haɗa rai ta juyo ta kalli inda nake

"Ke kuma dan ƙaniyarki sai kije kotu ta aura miki wani shege Samir ɗan mara mutunci tunda naga alamun ke kafafface baki san ciwan kanki,ke banda ke sauna ce mai zakiyi da waɗannan mutanan qaddara ce shi kanshi mahaifinnaki ya haɗa iri dasu bare ke ga saurayin arziƙi kinyi idan zakiyi saki na dafe shikenan ai"Nidai har Aunty Maryam ta gama maganar bance mata komai ba da nasan ina tofawa zata iya jin haushi

Abbah Zaid naji ya ce"Allah ya rufa asiri dai dare ya fara yi mu tashi mu wuce gida nasan Gwaggo zata kwana da ita"

Mama na kai idona na kallah ta kife kanta cikin ƙafafunta ban iya tantance yanayin da take ba shima Abbah Zaid ita naga ya kalla sannan yace

"Yawwa Gwaggo idan mun tafi sai ki ƙara kiran likita"

Inda muke ya juyo da kallanshi ba tare da ya ji amsar da Gwaggo zata bashi ba ya ce
"Yawwa ku shirya wasu sai na ajesu gida wasu Rumaisah ta ajesu tunda motoci biyu ne"

Inda Abbah yake tsaye ya juya da kai da duk maganar da akeyi bai iya furta komai ba

"Abdullahi!, Abdulllahi!!"naji kiran da Abbah Zaid ke masa hakan yasa nima sake maida hankalina ga Abbah banyi tunanin ya ji kiran da farko ba sai a karo na biyun da na tabbatar tunanika ya faɗa kawai

Cikin alamun ɗan tsoro da ya bayyana ƙarara fuskarsa naji ya ce"Na'am Zaid zamu wuce ɗinne?,muje to" daga yanayin maganar na fahimci hankalinsa gaba ɗaya baya tare damu nasan kawai ƙarfin haline irin wanda Abbah ya sabayi yau ma ɗinma yayi

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now