40...
"Sumayyah har yanzu baki ƙarasa blending ɗin ba"
Muryar Aunty da na jiyo ta dakatar dani daga blending kayan miyan da nakeyi a electric blander da duk lokacin ta nuna min yadda zanyi aiki da ita juyawa nayi na kalleta mai take soyawa lokacin tana gaban Cooker Gas Mai zaune jikin lokar kitchen ban iya gane mai nawa bane saboda bama anfani da shi kuma ba kalar na gidan Abbah Hashim bane ba ajiye tunanin nayi na ce"Eh Aunty amma nakusa gamawa"
"Ok kiyi a hankali fa idan ya soyo man sai a fara saka wanda kikayi blending ɗin,shiyasa nafisan akaimin markaɗe yafi saurin aiki toh kina jina dq mutumin naki Jabir kansa ke ciwo"
Murmushi nayi nace "Eh Aunty tun a mota yafaɗamin da gaske yake"
"Hmmm baki san Jabir da ƙin aike ba Sumayyah,danshi harma yafisan na barmasa yayi girki,shi kuma Muhammad shiririta garesa ne"Cewar Aunty ta ƙarasa maganar tana ɗaukar robar kayan miyan dana zuba wanda na gama markaɗawar masu yawa,Kayan miyan suna da yawa ba laifi duk tsadar da sukeyi ita Aunty bata gani ba acewarta ai Mama inta farko irin wannan abincin take son ci mai miya mita,shiyasa har kifi mai yawa Aunty tasa Abbah Zaid ya siyo dan kafin mu gama aikinsa Aunty ta nunamin yadda zanyi blending ɗin na fara
"Kamar kukan A'isha naji"tayi zancen tana cigaba da juya kayan miyan da tagama zubawa
Kunne na kasa cikin falon da nima kamar kukan naji kallonta ta dawo gareni ta ce
"Kinji ko kema?"
Na daga kai "Eh Aunty wallahi kamar kukanta"
Aunty ta dubeni"Kinga cire mana kokwanton jeki dubota,ƙila Muhammad ya bar falon ma a jiye blending ɗin maza ki wanke hannu"
Umarnin Aunty nabi na Tara hannuna cikin fanfon wanke wanken kitchen na sa omo na wanke cikin sauri na bar kitchen ɗin
Ban sameta tana wani kukan azo a gani ba dan idanta rufe take kukan alamun tashi takeyi,hakan yasa na ɗauke ta na fara jijjigata dandanan ta koma barci ganin Muhammad baya falon yasa ɗauki towel ɗin ta na rufe ta da shi na koma kitchen ɗin
Sallama nayi Aunty ta amsamin ta dubemu nida Aisha ɗin
"Kukan take ko?"Kaina ɗagama Aunty daganan na ce"Eh Aunty za dai ta fara tana ƙoƙarin tashi barci ne,kingama ta koma"
Aunty ta gyaɗa kai"Wato shi Muhammad ya fice ya barmin yarinya a haka yakeson ƙanwar zai dawo ya sameni ne"
Dariya nayi kaɗan jin zancen Aunty dan yadda nasan Aunty da Muhammad bata bugunsa ko faɗa Jabir yace batasan a yima Muhammad tace mai babban suna ba'a masa faɗa bare zagi,duk da dama banda ƙin jin kaɗan na yarinta baya komai saidai da ɗan gatane
"Kina dariya kenan Allah kuwa,dan Abbansa na hana ni make yaron nan wani lokaci,juyo na sa miki ita baya,kema na lura wahala kikeso ki baiwa baiwar Allah"
Ni dai shiru nayiwa Aunty jin zancenta dan Jabir yana faɗa min zamu fito asibiti cewa Muhammad na kuskurewa sai Aunty tace Abbah Zaid ne kaza kaza alhalin itace,Miiƙa mata A'isha na juya baya ta sakamin ita na ɗaure zanin
Cabbage da Gurji da Karas da sauransu Aunty ta bani yankansu na zauna brander akan kujera a ƙofar baya ta kitchen na fara yankawa ganin banajin daɗin aikin saboda goyo saidai ina miƙewa na sauke A'isha Aunty zata ce a'a baza'a kwantar da ita a barta ita ɗaya ba wani gata nake gani Aunty na nunawa A'isha dan ko Mama albarkarshi,Wani girma na uwa na baiwa Aunty a zuciya irin yadda take kulawa da lafiyar Mama a yanzu ita da mijinta danko Aunty batayi hakaba ko waccen maganar ni banga aibun Aunty ba dukda akan mahaifinane dan a tunanina a zuciya da ɗan uwan nasu aganii zasu iya ɗawainiyarsa su masa abinda suke yaudararsa ya rabu da Mama zasuyi masa ɗin,sai nakeji ta cire min wani daga cikin ciwan na idanuna dukda ban shekaru ban taso da saninta ba amma ta fiye min Aunty Mubaraka,Aunty Maimuna da sauran su musamman Aunty Asma'u ma da har zuwa yanzu abunda tayimin ya kasa barin tunanina nakan ji ciwo mai tsanani a raina na tarin girman laifinta da zuciyata take gani
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.