41......3:02pm shine yayi daidai da ƙara sa parking ɗin mu a parking space na asibitin cire kaina nayi daga kallon agogon cikin motar na miƙa hannuna na taɓa handling ɗin motar na buɗe zancen Aunty ya katseni tana miƙo hannu
"Kawo Aishar ki sauka saina miƙo miki ita"ba tare da nayi musu ba na miƙa wa Aunty,Aisha,Ni Kuma na fito daga wajen ina fitowa Aunty ta fito da A'isha a kafaɗarta rufe murfin ƙofar ɓangaren dana fito nayi Aunty ma na ɓangaren da ta fito tayi ta sawa motar key
"Yawwa Sumayyah dawo tanan na goya miki ita mu ƙara sa Boot mu ɗauki abincin"Abinda ta faɗa ɗin na aiwatar ba tare da nayi musu ba,kuma ba tare da naji komai ba bare yazamarma zuciyata ƙorafi dan ko Mama ɗin haka take mana ɗin ma indai munanan mune masu goya A'isha da ɗaukar ta nima raino yabi jinin jikina zan iya cewa
Ƙofar boot ɗin Aunty ta buɗe muka ciro kayan sannan ta rufe Boot ɗin muka ɗauka muka ƙara sa zuwa ɗakin da Mama take kwance
A brander ta kusa da ɗakin muka tarar da su Gwaggo su Rumaisa sai su Aunty Jamila sun shimfiɗa tabarma sunyi zazzaune ga kulolin abinci gefen su gaisawa mukayi dasu
Gwaggo ta dubemu ni da Aunty da muke ƙoƙarin aje kulolin namu abincin gefen Gwaggo
"Har da wata hidimar haka Rumaisah?,Ai da kin bari ma su Jamila duk sunzo mana dashi yanzu muka gama ci"Cewar GwaggoAunty ta ɗago fuskarta ta ce"A'a Gwaggo ai ba wata hidima abincine kuma ba yawa ma sosai,na su Jamila ai dabanne nawa ma dabanne, zuwa anjima sai aci wannan"
Gwaggo ta riƙe baki"A'a Rumaisah akwai fa hidima tun jiya da aka kawo Hauwa'u kuke ta faman yi,yanzu kuma ga ɗawainiyar abinci kuma haka mai yawa"
Aunty ta girgiza kai ta ce
"Allah Gwaggo ba wata hidima anan ban ganta ba,duk abinda zanyiwa Hauwa'u ai ban faɗi ba,Domin nasan da Hauwa'u ce mai ƙarfin fiye da wannan zata yimin kuma ba tare data gaji ba,kin tuna dai yadda muke tare dai Gwaggo in banyi mata ba gani nake wazai mata kuma inajinma kamar ubangiji bazai yafe min ba indai ina dashi ban yiwa Hauwa'u ba"Gwaggo ta girgiza kai"A'a Rumaisah kidaina faɗar hakan ai mune dolen Hauwa'u mu ya dace muyi mata idan bamuyi ba Allah ya iya kamamu da laifi ma"
Aunty ta yi murmushi ai nima dolenta ce Gwaggo"
Gwaggo ta jinjina kai ta ce"Allah ya barku tare ya ƙara danƙon zumunci,Allah ya biya ki abinda kikayi"
Aunty tayi murmushi ta ce"Amin Yawwa Gwaggo haka ya kamata kice kawai,yanzu dai ya jikin nata ta farka ko?"
Gwaggo ta ɗaga kai"Eh ta farko ba daɗewa an kirama likita mijinta yana ciki Likitan ma yanata faɗa da yazo ya samemu a ciki gaba ɗayanmu shine kika ganmu wajennan yanzu ma yace ko sun fito bame sake shiga sai can anjima"
Aunty da take ƙoƙarin zama kusa da Gwaggo ta ce"Alhamdulillah,Allah ya ƙara mata lafiya dama ba'asan ana damun mara lafiya da hayaniya ai Gwaggo ɗazun ma inajin abinda yasa basuyi magana ba saboda anyimata alluran barci,barcinnata yayi nauyi amma yanzu zaryar ma sai an rage ta ai tunda private asibiti ne "
Gwaggo ta jinjina kai gami da kallon Aunty ta ce "Eh haka shima duk yayi bayani likitan, amma ya zaki zauna kuma?ai yakamata ki shiga kema dake fa akayi komai jiyan "
Aunty cikin ladabi ta ce"A'a Gwaggo tunda Abdulllahi na ciki kuma shine mijinta ba sai naje ba da dai Daddynsu Jabir yazo ne sai ya shiga jiyan ma duk shine yayi abubuwan da yakamata ace anyi ɗin bani ba"
Gwaggo ta ce "Hakane amma da kin shiga ɗin kiga yanayin jikin nata kunyi ɗawainiya da ita da ƙarfinku da kuɗin ku daga jiya zuwa yau ɗin nan kuma abunda kuke buƙata yasamu,Allah dai ya saka muku da alkhairi ya ƙara zaman lafiya ke da mijinnaki,dan a tunanina a baya gatansu ya ƙare daga abinda ya faru tsakaninsu da waɗancen mutanan yanzu saina ƙara miƙa wa Ubangiji lamuranmu na sake yaƙinin gatan kowa Allah ne"
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.