31

38 5 0
                                    

31....
Bansan yarda Mama sukayi da Abbah ba sai washe garin ranar da safe na kammala wanke wanke gidan ya rage dagani sai Mama inda Mama take kwance a tsakar gidan na nufa ina riƙe cikina na zauna mama ta dubeni
"Lafiya kuwa Sumayyah?"
Hawaye naji suna ƙoƙarin zubo min da in ban manta ba tun abincin jiya da daddare ban ƙara sa komai cikina ba sai awara guda uku da ba inda tajemin yau kuɗin siyo kokonma sun gagara hawayen naji sun zobomin,mama tsawa ta dokamin

"Wai ke lafiya?,ina tanbayarki ko baki da baki ne?"hawaye na share na dubi Mama na ce"Mama yunwa nakeji kamar zanci babu"tsaki Maman tayi "to kici babun mana,tunda kinfini jin yunwar ai,kuma ba kinci awara ba ɗazu?"

Kai na girgiza"Wallahi Mama banci ba sai wadda aka bamu uku ukun nan"

Tsaki Mama tayi"To ina laifi Sumayyah iya abinda ya samu kenan,ki daina ƙoƙarin tayarmin da hankali,ƙirjina ciwo yakeyi"

Bani da yadda na iya na tashi kamar na faɗi saboda yunwa Abbah na gani ƙofar ɗaki tsaye kamar an kafasa kallonsa nayi da alamun tausayawa ya rame ya rame sai idanu da hanci kawai har zan wuce naji muryarshi a cikin kunnena
"Ki shirya ranar Monday zan kaiki makaranta",dukda nasan ba iya wannan maganar bace bakin Abbah dan inada tabbacin sai Mama ta bashi labarin Jurayd yace zaiyimin uniform da Abbah nasan sai ya nuna ɓacin rai akaina yadda nake bari Jurayd nayimin hidima, da dan ya kwantar min da hankali yaƙi yin zancen dan nasan yaji duk firarmu da Mama "toh Abbah" na bisa da shi na ja ƙafafuna da kyar zuwa ɗakinmu kwanciya nayi a saman yaloluwar katifarmu kwanciyar kasa yimin daɗi tayi sai juye juye cikina kuka yake hannuna rawa yake yi kamar zanci babu in samu kwarin da zan iya fita ko barar nayi makwafta na samu ta gagara bansan tsawan lokacin da na ɗauka a haka ba har barci ya kwashe ni yunwa ce da ta taso min fiye da ko yaushe,cikin barci naji ana kiran sunana a hankali na shiga buɗe idanuna na saukesu tas akan Ahmad da yake gefena a tsaye murmushi yayimin yunƙurawa nayi dakyar na tashi na jingina da bango ina sake kallon Ahmad

"Ahmad lafiya kuwa badai an taso makarantar ba?"na qarasa maganar ina kallonshi

Kai ya girgiza min"A'a break akayi mana saina biya gidan Aunty dama tace naje kingani abinci ta bani ma,ina zuwa Mama tace kina kururuwar yunwa ɗazu na zo na kawo miki "

Sai lokacin da yayi maganar naga kular dake riƙe hannunshi gidan da Ahmad ke aiki matar nasanshi sosai kamar ɗan ta yadda yaran ta ke kiranta haka Ahmad yake kiranta shima dan kam yana bamu labari,murmushi nayi

"Amma kaifa Ahmad?,Mama ma yunwa takeji nasan ga Abbah da zai fita"

Kai Ahmad ya girgiza"Kinga ki aje lissafinnan ni da Abbah mazane Mama kuma ta fiki juriya,inkin ƙoshi ki rage mata a yanzu munfi buƙatar ingantar rayuwarki akan tamu ai Yaya,in kingama ci dama saiki kai mata kular kinga zan makara idan zan koma kai mata ai zaki gane kwatancen gidan Please"

Kai na ɗaga ba tare da na sake cewa komai ba har Ahmad ya ajiye kular ya fita nasan gaskiya Ahmad ya faɗa dan kam batun hankali gurin Ahmad har ya fini Kasancewarsa namiji kuma Allah yasa dai mai hankali ɗin ne buɗe kular da ya aje gabana nayi ƙamshin abincin yafara shiga hancina shinkafa da miya ce tasha kifi tun kafin na fara ci nake haɗiyar yawu dan yaushe rabona daganin irinta ai ko a makwafta ma namanta rabon in ganta dukda ɗin ba makwabtan nake shiga ba sai da naci na ƙoshi na fito na miƙewa mama sauran da inda take na sameta tana jijjiga A'isha da itama ba wani girman da tayi dan ko ta kusa wata biyu a yanzu ma,inda na hango buta na nufa na jiyo Mama na cewa

"Ba dai harkin ƙoshi ba?"
Ba tare dana furta komai ba na ƙarasa wajen  butar nayi sa'a da ruwa na wanke baki da hannuna na sha ruwa na dawo kusa da Mama na zauna ganin ta aje abincin na dubeta
"Mama kin ƙoshi ne?, Ahmad yace fa nakaima Auntyn kular in na gama"

"Ba yanzu ai zanci ba ɗauko guri ki juye ai da ragowar omo ko?"cewar Mama

Na bata amsa da "Eh mama akwai" daganan na miƙe kwano na ɗauko na juye na ɗauki kular na wanke sosai,ɗaki na shiga na lalubo hijabi cikin kayan wanki da baicika dauɗa ba nasa na fito tsakar gidan da har lokacin Mama tana nan na ɗauki kular

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now