38

31 5 0
                                    

38........

Dafanin da naji anyi yasani ƙara riƙe A'isha na miƙe tsaye da rawar jiki

"Sumayyaah!"Jin Muryar Aunty nayi kamar daga sama hakan yasa na rungumeta da A'isha na fashe da kuka ina cewa

"Aunty ki taimaka mana akai Mama asibiti kar ta mutu cikin wannan mawuyacin halin"

Bayana ta shiga bubbugawa
"Ya isa haka kukan Sumayyah share hawayenki insha Allah zanyi iya ƙoƙarin ganin Hauwa'u ta samu lafiya,zan taimaka muku"

Jin hakan yasani sakin Aunty, A'isha dake kwanyara kuka ta amsa daga hannuna ta shiga jijjigata  kafin tace
"Kaini ɗakin Mamartaku"

****
Aunty tana ganin Mama kwance ta ƙara sa wajenta ta rushe da kuka
"Hauwa'u sannu Allah ya baki lafiya nasan nayi laifi a karo na biyu na kasa cigaba da nemanki sai da ɗanki yazo da kukansa yake sanarmin"
Da na fahimci Ahmad ne ya faɗa mata fitar da yayi ɗazu ashe gidan Aunty yaje

Aunty Maryam cikin kukan da Aunty na farawa ta fara itama,ta ce
"Kinga dai yadda jikin Hauwa'u tashi guda ya canza Rumaisah,Gwaggo ta fita nemo kuɗi har yanzu bata ɓullo ba shima mijinnata babu shi babu labarinsa"

Aunty ta girgiza tare da tsagaitawa da kukan da take yi "ku fiddota asata a mota mu tafi asibiti,ai zama bai kamamu ba,da kun sanarmin ba wanda zaije yasha wahalar nemo wasu kuɗi ai"

Aunty Asiya ta fara miƙewa da ƙoƙarin ƙomawa wajen Mama domin tayarda ita Aunty Jamila ma matsawar tayi sukayi kama kama suka fidda ta daga ɗakin dan ko ciwon sati gudan yaƙara sabgar da ita

Aunty ta dubeni
"Yawwa haɗo mata kayanta ki kawomin mota dan wannan jikin nata ba sallamar da zamu samu washe gari"

Kai na mayar ƙasa na fara sosa ƙyeya, dankuwa dai rabanmu da wanki saina ce bansan ranar ba babu sabulu ba omo sai zamusa muke jiqawa a ruwa mu barbada omo mu wanke

"Kinaji ana magana kinyi tsaye kina sosa ƙeya uwar taki kikewa hakan kenan?"Muryar Aunty Maryam naji ta katse tunanina

Kaina na ɗago na kalli Aunty da A'isha ke kafaɗarta tana jijjiga ta tayi shiru abunta kamar ba ita ce ke kukan da ta ɗagawa kowa hankali ba

"Wallahi Aunty babu wankakku ko ɗaya"

Aunty Maryam ta kalleni taja tsaki"Dama nasan za'a rina,kowacce taɓarɓarewa da lalacewa sun tattara akan Hauwa'u ,ba'asamu abinci bama,inaga wanki"

Aunty ta katse Aunty Maryam da cewa"mu je kawai Yaya Maryam na samo mata cikin nawa idan zan taho asibitin Abban Jabir nasan mu yake jira,ga A'isha karta cigaba da kukan"ta ƙara sa maganar tana cigaba da jijjiga A'isha ɗin

Aunty Maryam bata sake cewa komai ba suka fito nima na biyo bayansu,banyi gigin binsu inda motar take ba dan nasan Aunty Maryam na ganin na bi bayansu faɗa zansha wajenta ƙila ma yafi na farko dan gaba ɗaya laifin Abbah yana ƙoƙarin komawa kanmu,ina tsaye ƙofar gida har motar ta tashi ina share hawaye da yiwa Mama addu'ar samun sauƙi,rufo ƙofar gidan nayi da tsoro ya fara ziyartarmin lokacin domin mu kaɗaine Abbah da Ahmad har lokacin babu wanda ya waiwayo gidan ɗakinmu  na shiga na zauna na zuba tagumi da hannu biyu ƙannena nake kallo ɗaya bayan ɗaya yarda suke kwance a cure sun takura kansu da alama ba barcin daɗi suke ba bama da alama ba azahirin gaskiya ma hakan ne ka kwana da yunwa ka tashi da ita,ga yarda zumuncin yanzu yake tafiya musamman kalar namu da shine musababbin ƙara lalacewar rayuwar tamu izuwa wannan halin,tausayinsu nakeji fiye da tausayin kaina,Bugun ƙofar da naji anayi yasani miƙewa na fito da tsammanin kodai Ahmad ko Abbah cikin biyu akwai ɗaya dayake kwankwasowa ko kuma dukkansu ne a tare

"Wanene?" nayi maganar ina ƙara sawa kusa da ƙofar

"Nine"jin Muryar Ahmad ya sani buɗe wa na matsa gefe ya shigo kallonsa nayi shima ni yake kallo

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now