NA CANCANTA! 48
Na
Halimatu Ibrahim KhalilRabbi inniy lima anzalta ilaiya min khairin faƙir.
48
Satin Abbah ɗaya a asibiti aka sallamoshi gida da ƙarin jaddada mana hanyoyin kula dashi,Ƴan dubiya sunyi tururuwar zuwa waɗanda muke abun arziƙi da ƴan uwan Mama,daga ɓangaren Abbah babu wanda yazo dubashi dama kuma bamu saka rai ba da zuwannasu,Gwaggo kusan kullum tana hanyar zuwa duba Abbah ɗin, Abbah Zaid da yasamu labari kuɗi ya turo yace a bawa Abbansu Malika abubuwan da ya kashe amma ƙiri ƙiri yaƙi karɓa"Ni dan Allah nayi Sumayyah fata dai ubangiji ya karbi aikina,wannan ku ajiye kwayi hidimar gida tunda an sallamosa jiki ba kwari nasan ba samun fita zai riƙayi ba"
"Amma Abbah..."
Abbah ya katseni"Amma me Sumayyah bazan amsa ba fa"
Ummansu Malika da take wajen na juya na kalla
"Umma kisa baki dan Allah"Ummah ta yi murmushi"Ai Sumayyah ko yace zai karɓa zan hanashi ki tashi kije ki maida ma Mamarku kuɗinnan ƙila ma bashinsu kuka ciyo"
"A'a Ummah Aunty Rumaisah mijinta ya turo mana a bawa Abbah ɗin"
"To ku ajiyesu zasu yi muku wani amfanin tunda ko yanzu ma jigilar siyan magani na nan"
"Mungode Allah ya saka da Alkhairi"Badan inaso ba sai dan bayarda na iya na hakura jiki a sanyaye na dawo gida
A tsakar gida na haɗu da Mama da take shara
"Rumaisah! kina ina kika bar Mama na shara?"nayi maganar da ƙarfi
"Na aiki Rumaisah"Masifar dana tanada zan yiwa Rumaisah na mayar jin abinda Mama ta faɗa na dubi Mama
"Amma Mama saiki jira mu dawo kema ɗin ba ƙwari jikinki yayi ba,na kaima Abbansu Malika kuɗin wallahi ƙiri ƙiri yaƙi karɓarsu wai mu ƙara muyi hidimar gida dasu"
"Subhanallah akanme bai amsa ba kin ko lallaɓashi Sumayyah?"
"Wallahi Mama nayi duk abunda kike tunani bai karɓa ba na ce masa turowa akayi mu bashi yace shi dai a'a"
"Toh shikenan Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi da aljanna"
"Amin ya rabb"na furta a hankali na wuce
Ɗakinmu na shige ina shiga na cire hijabin jikina dan baƙaramin zafi yake min ba kuɗin na ɗaga fulo na saka ina jiran Mama ta kammala aiki da takeyi naje na bata ina ƙoƙarin maida fulon idona yayi duba da wayata da yawan amfani da ita yayi sauƙi gareni tunda Abbah ya fara rashin lafiya
Abun mamaki shine duk faruwar wannan lamari Juraid na kirana a waya kuma bai taɓa canzamin da kalma ɗaya ba sai nake ga ko ya manta abinda ya faru ne ko kuma iyayenshi basu sanarmasa ba dan inada tabbacin Baba bazai mana ƙarya ba duba da bai taɓa zuwa gidanmu ba sai a waccen ranar da na sake tabbatar da faruwar lamarin ganin Juraid bai nemeni da maganar ba yasa nima naja bakina nayi shiru,Har asibiti yace zaizo duba Abbah na ce masa sai dai idan bazaizo da kayan dubiya ba ya furta min sai dai nace kada yazo kai tsaye nayi nayi na fahimtar dashi sai dai fahimtarwar ta kasa yiyuwa dan har haushina yaji dalilin da yasa kwana biyu ma ba muyi waya ba kenan shi a dole yayi fushi nima ganin nafishi gaskiya yasa ko bi takan sa nima kaina banyi ba dan ko flashing ban yi masa na nemesa ba,Tunanin na cire na sauke nannauniyar ajiyar zuciya na ɗauki wayata na maida fulon kamar jira na ɗauka akeyi ta fara ringing da baƙuwar lamba a maƙale a screen ɗin wayar
Ban tsaya dogon nazari ba na ɗauka da zatona ya bani ko Halima ce itace mai yawan kirana ƴan kwanakinnan da baƙuwar lamba
"Assalamu alaikum warahmatullah"jin mamallakin muryar ya sani jin saukar wani ɓacin rai mara misaltuwa a rayuwata Yaya Samir ne,ina ƙoƙarin janye wayar na sake jin maganarsa
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.